Chapter 64
Chapter 64
musulmai to dan Allah ka sa baki kayiwa Shehu magana ya maidata Kaine kadai zaka fada Masa yaji dan Allah,Aslam ya gama Jin Aunty yace ni Aunty mene hadina da iyalin Abba Shehu,Ina yaro me zai kaini shiga zancen manya in yaga dama ya dawo da ita idan bai ga da ba ta hakura ta koma Kauye inda tafi wayo ni ba ruwana da ai bata san dan Adam me daraja bane bata taba zaton ma Zan Mata rana ba a rayuwa,Aunty tace bana son taurin Kai Aslam ya Ina rokar ka kana botsewa,yace Aunty shike nan taci darajarki albarkacinki Zan Masa magana amma bata da matsayin da Zan taka har can wajensa Zan dai kirashi a waya kawai in ya yarda tayi murna idan bai yarda ba ruwanta mutum dai abinda ya shuka shi zai girba Kuma Alhmdllh ko yanzu tun a duniya ba ayi nisa ba sun Fara girban nasu hukuncin,bazai yuwu ka shuka gero kace zaka girbi shinkafa ba bazai yuwu ba kowa yayi yanda yake so to bazai ga yanda yake so ba, idan Kuwa kayi abinda baka so to kuwa zaka ga abinda kake so haka rayuwa take,basai Yar taki ta auri me kudin ba jarinku kuci gaba da cin duniya gashi nan talaka ma ta rasa yanzu sai ku nema Mata hatimin annabi Yusuf ta sha ko ta samu ko talaka ne abinda bakwa so din dai...Aunty ce tace ya Isa haka Aslam idan baza kayi ba ka Mana Shuru ni ban ma San haka kake da mugun riko ba,Aunty baki San me aka Masa bane har uwarsa sun zageta babu wulakancin da basuyi Masa ba cewar Siyama,Aunty tace bana so Siyama gyara nazo bana son tone tone ke me Miji Zaki zake ki tare masa Maman Nusaiba ai uwarki ce kema,Mama tace Siyama kiyi hakuri ki yafe min,Siyama tace ni baki min komai ba zagina nane da tsine min da kuka yi Kuma kanku ta koma to haushin me zanji,Aslam yace ko ma dai mene dan kanku Kuma ko yanzu kasuwa ta tashi dan koli yaci riba Zan Masa magana,Aunty tace yawwa ko Kai fa Basu dade ba Mama tana Jin tsoro ta damu sai an tafi Aslam tsoro yake bata,ai Kuwa Suka tafi Suna tafiya Aslam yace lallai Aunty ai Kawai lallaba su nayi ba inda zanje ko waya bazan Masa ba ta shekara dari bata koma gidan Miji ba,Siyama tace a'a fa ka riga ka fadawa Aunty yanzu jiranka zata yi kayi hakuri dai kayi Masa waya sabo da Aunty idan baka yi ba ka raina min Iyayena fa Kuma ni nasan mijina ba haka yake ba Wanda na aura me yafiya ne da hakuri yace naji Mrs Aslam zanyi ku kyaleni na Sha ruwa please,Jikinsa ta koma ta kwanta. Yaran Mama Kuwa tunda Suka ji tana gidan Kawu kullum suna gidan Wajen uwarsu Yara da mahaifiyarsu akwai shakuwa ta musamman sabo da yaran Aunty da Kawu Suka dage Shehu yayi hakuri ya maida Mama sai Nusaiba itama duk da Shehu Yana Mata fada haka take bashi hakuri bata gajiya amma Shehu ya kafe yaki abinka da me hakuri bai iya Fushi ba, Landlady ce ta siyowa su Nusaiba kayan sawa harda takalma da kudinta ganin Basu da suturar arziki Musamman Nusaiba da Sufyan ya kwace Mata sutura gaba daya ya hanata shi yasa bata da kayan sawa,Aunty har Raudah ta bugawa waya tace dan Allah ta hado Mata kayan da zata bayar kwance ta Aiko Mata zata bawa Yar mijinta bata da kayan sawa,haka Raudah ta ciko Leda da Kaya masu kyau kusan ma sababbi ne Landlady ta bawa Nusaiba kala bakwai a ciki sai Ihsan da take Yar budurwa itama aka bata wasu a ciki kala hudu, har takalma kala hudu Raudah ta bada da mayafai duk aka bawa Nusaiba,Nusaiba tana murna sosai wani bangaren Kuma idan ta tuna tsiyar data shuka da daular da ta shiga ita da sutura ma Sai dai ta bawa wani yau ta dawo gidan jiya ita ake bawa kwance a rayuwarta ta baya talla ne Kawai bata dauka ba,Watarana cikin dare sai kuka take tilka ta koshi. Tunda Aslam yace zaiyi ma Shehu magana ya manta ma da batunsu har an wuce Sati biyu Mama tana jira a gidan Kawu,Kawu ma yaji Shuru Shuru waya ya bugawa Aslam da Kansa yace bayan sun gaisa yace Aslam kaci gidanku Ina batun Maganar da kace zaka yiwa Shehu akan matarsa,Aslam sai yanzu ya tuna ma da batun Yana Office ma yace Kuyi hakuri wlh na manta,ka manta ma kace cewar Kawu,Aslam yace Bari na kirashi yanzu yanda Muka Yi zan sanar da ku,Aslam Shehu ya Kira bayan sun gaisa yace Kawu dama magana zamuyi,yace Ina jinka Aslam,yace Alfarma nake nema a wajenka Abba,Shehu da sauri yace Fadi Aslam ko Mene shi Inshaallah zanyi maka,yace akan Mama ne dan Allah kayi hakuri Allah ma muna Masa laifi Kuma Yana yafe mana bare dan Adam musamman ma Wanda yasan yayi laifi ya tuba ya gane kuskurensa,ko dan yaranta ma kayi hakuri yaran zaka duba,Shehu ko musu bai iya yiwa Aslam sai yace dama Ina sonta ai iskancinta ne yayi yawa bata da mutunci ko kadan amma zata dawo Inshaallah tunda kayi magana Inshaallah Zan dawo da ita amma ka kyaleta ta Kara Shan wahalar rayuwa tukun nima sai na gama amarci na sannan ta dawo yanzu Kam kace ta koma Kauye zan Mata magana,Aslam Yana dariyar Shehu Wai sai ya gama Amarcinsa a fili yace to Abba za a fada Mata na gode,Aslam nan take ya Kira Kawu ya fada Masa yanda sukayi da Shehu,Kawu yace Alhmdllh kaga kaima ai ka samu lada yanzu bari na sanar mata. Kawu Mama ya samu yace ki godewa Allah Aslam yayi Miki rana Wanda duk duniya babu me miki irinta ya sa Shehu zai maida ke dakinki amma yace ki koma Kauye zai Miki magana da Kansa,Mama ta fashe da kukan farin ciki tace dan Allah ku barni a nan ku taimakeni Kauye wahala inda kasan Ina cikin wuta,Kawu yace ai yace Indai a nan kika zauna bazai dawo Dake ba ai da sauri Mama ta Fara tattara kayanta zata tafi kauyen nasu haka,Kawu yaji tausayinta amma gwara ta Sha wahala sosai yanda ko ance ta sake yin wani abin baza tayi ba,Haka ta koma Kauye taci gaba da Shan bakar wahala a gidansu tunda ba iyaye ne da ita ba a gidan Yan Uwa ne Kuma Yan uwansu kaf basu da mutunci kowa dan iskan Kansa ne kudi Kawai shine mutuncinka a idon su,Gashi idan tana so ma a San Mata abincin sai taje anyi aiki da ita a gidan surfe da daka sai tayi dole,hannun Mama yayi kanta yayi kaushi sabo da wahala,gashi Shehu Shuru har ta sake yin wata guda a kauyen su Nusaiba sai rokonsa suke Yi har kuka sai da Suka yiwa Shehu sabo da Ameer yaje yaga halin da mahaifiyarsu take ciki,Shehu sai lokacin ya nemi yan uwan Mama maza Suka Yi magana za a sake maida aure sabo da ta gama Idda tuni,bata sani bama sai Yan uwanta ne Suka sanar Mata an maida Aurenta da Shehu,Zabura Mama tayi gwanin tausayi tace yazo ne? Yace ae yazo ya koma ma yace idan kin
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71