Skip to content

Chapter 41

Chapter 41

AURENMU Book One Complete Hausa Novel 1,239 words 0 views Progress saved
Download Book

kuka ya taho,dangi Suka Yi caaa a kanta da tsokana sabo da kowa ya Santa da baki amma yau Kamar ba Siyama ba,kawaye suna Mata tsiya Kawai ta kwanta a katifa ta juya musu baya tun tana hawaye har bacci ya kwasheta kowa yazo Ina Amarya sai aga tana shakar uban bacci tun 12 har kusan 3pm bacci takeyi,ana ta posting pics din ango da na Amarya a online Wanda suka Zo bikin duk da cewar ma basu dauki hoton tare ba, ai Yan layinsu suna fara zuwa bikin Suka tasheta da tsokana wata tazo ta Dana Mata duka a gadon baya ke dalla tashi Amarya da bacci ki tashi kiyi wanka aka taru akan Siyama sabo da mutane da yawa ana Wasa da ita ta ko Ina caccakarta akeyi,4pm Aunty tasa tayi wanka tare da canja Kaya wani material ta sa me shegen kyau na lefe,suna bikinsu dai Kafin dare aka Kai Yan biki gidan Amarya duk me son ganin gidan Amarya Aslam ya turo wasu bakin abokansa sun kaisu a mota har Aunty taje taga gidan yarta komai yayi Mata itakam,Yan bikin ma suna ta yabawa da yan uwa,na nesa sun tafi ma tuni sabo da Kawu dama ya fada musu ba taro shi yasa Basu zauna ba,Aunty Kuwa dama ta fadawa mutanenta Kawu ne zai Kai Amarya da Kansa shi yasa babu macen data zauna zuwa magriba kowa ya watse sai Yan uwan Aunty su Uku suna ta aikin gyara gidan,Sabeer ne yazo ya kwashi kayan lefe duk wani abinda Siyama take so ya tafi,Aslam ce Masa yayi ya bar kayan a motarsa da ita zai dakko Amarya idan sunje gida ya cire kayan gaba daya,Kamar Aslam bazai Zo daukan Siyama ba sai dare Aunty tace tayi wanka ta shirya ya yo waya yace gashi nan,Siyama tace ban dade da yin wankan ba fa to ai na Amarya ne idan Kika Yi yanzu ai kin huta Yi a can,Siyama haka ta fesa wanka tazo ta Gama shafe shafenta ta saka wani Leshi da Kawu ya dinka Mata na biki me shegen kyau sea blue and black mayafinta me shegen kyau Kalar kayan da takalmi da jaka komai same color tayi kwalliyarta me kyau ta shafa turaruka tana shiri Kawu da Aunty Suka shigo Suka zauna a dakin Suka Fara Mata nasiha iri iri tana ji ta fashe da kuka suna Yi tana kuka kanta a kasa har Aslam yazo tana kuka,Aunty itama harda hawaye ta fada bedroom dinta ta kwanta tana ta kuka Aunty zata rabu da yarta,Kawu shi ya tasa keyar Siyama tana kuka kanta a kasa ta rufe kanta da mayafi tana kuka ya kaita har mota inda Aslam ke mazaunin driver sanye cikin wata shaddar Yar ubansu ruwan kwai,Shiga tayi gefe ta zauna Kawu ya rufe dama ya yiwa Aslam tasa Nasihar tuni,Siyama ta sauke glass din motar tana shesheka tace Kawu..... Kawu yace a'a Siyama karyar rashin kunya ta Kare ki daina nemana gaki ga Aslam aje ayi ta samun ciki idan Kinga dama ki Haihu sau goma a shekara Allah yasa Albarka,Aslam Murmushi yayi Kawu ya yiwa Aslam godiya yace su tafi Aslam yaja mota Suka tafi Siyama na kuka. Affan dawowa yayi gida daga wajen daurin Aure Raudat ta tsaya a jikin window tace Ina kaje ne haka? Yace yau ki tayani jaje an min gora,Nasha Sanda da Kaye an min mugun Kaye budurwa ta aka daurawa aure Bata so na wani take so,Raudat taji wani farin ciki tace amma ya Naga baka damu ba? Juyowa yayi Yana kallonta yace sabo da ke nake so,Raudat baki ta bude yace yes ke nake so fa na fada Miki kince sai kin duba shike nan ai rayuwa ce harda yin Kalar tausayi,Raudat tayi dariya tace ai zan baka amsa ne nan gaba,Affan ya girgiza Kai a ransa yace zanyi maganinki. Washe gari da Yamma wata budurwa ce Yar kwalisa Fara ta dau wanka ta sa key ta bude part din Affan kawai ta Shige a gaban Raudat dake Compound,Raudat ta bita da kallo yarinya Shuru Shuru bata fito ba har Raudat ta gaji ta shigo ranta a bace tace ke wai wa kike jira? Yarinyar tana yanga tace Affan, Raudat tace a Ina Kika samu key dinsa? tace shi yaje gidanmu ya bani yace na jira shi, Fitowa Raudat tayi cike da kishi hankalinta a tashe ta zaune a compound Affan ya dawo da sauri ya fito ya shiga part dinsa Kuma ya rufo kofa,Shuru Shuru ta ga bai fito ba shigowa tayi ciki ta same shi a zaune shi kadai bakuwar Kuma tana kitchen tana girki kamshi na tashi,Raudat zuciyarta ta jagule ta rasa inda zata sa kanta a duniya taji san yi fita tayi cikin fushi ta koma bedroom dinta ta kwanta a saman bed dinta ta Fara hawaye kafin kace me ta fara ciwon kai ko Hussain bata taba sonsa haka ba bare ma tayi wani ciwon Kai a kansa amma Affan bayan ciwon Kai harda zazzabi ya lullubeta,Affan Kuwa Yana ganin Raudah ranta ya baci ya mike ya shiga kitchen yace Safara'u zo ki tafi gida kin gama aikinki, Safara'u ta fito tace Yaya Affan ka manta sakon da zaka bani na bawa Mallam,Yace af na manta ya mike da sauri ya dakko Mata kudi yace gashi kice ragowar kudin gidan Mai ne da nace Zan kawo tace to tare da ficewa,tana tafiya dan Masifa kunnen Raudat taji Sanda tayiwa Affan Sallama tashi Raudat tayi tare da saka hijab sai palon Affan. Kishi ya gama cika Mata zuciya ta banko kofar ya mike zai shiga bedroom tace waccen wacece? Yace wa? Who is she? ta furta da fada tana rawar sanyi yace baki da lafiya ne? Ban sani ba mayaudari kace min Ni kake so kana zuwa ka kawo wata macen mene baka fada min ba,Affan yace Yar Liman ce fa uban gida na a'a Yar gidan sarkin musulmi ce karewar limanci si ba muharramarka bace da zaku kebe dan ubanta tazo tace zata maka girki Kawai kace sonta kake yi Kuma bana sonka bana bukatarka gaba daya ta juya ta fice Kamar zata tashi sama. Affan yaji Dadi yace yawwa kin Kama kanki ya zauna Yana murna sosai tana sonsa,washe gari ogan Raudat yazo zai dauketa zasu tafi aiki,taji sauki ta fito cikin shirinta da simple doguwar Riga marar nayi ta fito da takardunta,Affan yau hutawa yake a gida yaga Raudat an dauketa a dalleliyar mota ya zaci saurayi ne ya kule sosai Kamar zaiyi duka. Yamma nayi ta dawo Affan ya tareta a Hanya waye wancan? wa? Wanda ya daukeki a mota,abokin aikina nane ai gwara ni ba namiji na kawo dakina ba,Tambayarta yayi a nutse Raudat mu daina irin wannan kina so na ko bakya so na? Tsayawa tayi tana tunani Kawai ya juya ya Fara tafiya abinsa tace wait bai tsaya ba ta bishi da sauri tace Ina sonka kayi hakuri,tsayawa yayi cak Yana murna,gabansa ta dawo ta tsaya tace Ina sonka wlh kayi hakuri,sabo da murna ma kasa magana yayi,takardunta ya karba yace mu je na Zama mijjn Kan tace suna tafiya abinsu Suna hira abinsu amma kishin masifa ne da Raudat duk da haka tana zargin Affan ko suna shiri da Safara'u. Aslam

Table of Contents

Chapters

71 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71