Skip to content

Chapter 62

Chapter 62

AURENMU Book One Complete Hausa Novel 1,265 words 0 views Progress saved
Download Book

wanke da shara a dauke ki aiki kin tsaya kin zuba Mana Ido, Raudah tace ai wallahi gwara aiki ya kashe Ni idan ba namiji zaka dauka ba Indai macece bana so zanyi komai da kaina,Nusaiba juyawa tayi tana tuna rayuwarta a gidan Aslam,da kyawun Aslam da yanda yake nuna Mata so da kauna,kuka ta saki tana tafiya kasa shiga gidansu tayi ta zauna a kofar gida bakin kofar su tana ta kuka,tausayi ta bawa Raudah taje wajenta tace baiwar Allah kuyi hakuri wlh bamu fada dan mu wulakantaki ba mun San darajar dan Adam kune bakwa kau da kai ga mazajen wasu kiyi hakuri idan abinda mijina yace ya Miki zafi,Nusaiba tace ba wannan ne ya dameni ba,nadama nayi a rayuwata na tafka kuskure,to Allah ya Mana me kyau cewar Raudah tana juyawa motocin Aslam biyu Suka Yi parking daya motar securities ne daya kuma shine a bayan motar tare da Siyama,Fitowa yayi a hankali wanka iya wanka ga kyau,zagawa yayi tare da budewa Siyama mota ya riko hannunta ta fito da dan karamin cikinta a gaba ya Fara Fitowa ta Sha Abaya ta zuba kyau Kamar ba Yar kasar nan ba,sunyi kiba da kyau sun Kara wani fresh,da gani kasan sun dan huta a kasar waje, Nusaiba ta bisu da kallo kawai,Aslam Yana ganin Affan ya koma gaban Siyama ya kareta Wai Kar ya ganta tsohuwar budurwarsa Kar so ya dawo sabo,Affan dariya abin ya bashi,ke Kuma Raudah da kin ga mace sai boye Miji a tsiri nunawa lallai ita fa matarsa ce,Aslam zai wuce tsabar kishi harda nunawa bai San Affan ba,Affan ya Mika Masa Hannu da kyar ya karba Suka gaisa Siyama ta dawo gaba tace Affan kaine a unguwar tamu,yace Amarya Muka kawowa Alhaji Shehu kawar matata ce,Siyama ta kalli Raudah tace Sannu Ina yini,Aslam harda Jin haushi dan me zata gaisar da Raudah ai Raudah ce ta kamata ta gaida Siyama,Raudah ta amsa da fara'a Suka gaisa ta gaida Aslam ya amsa,Affan yace Nasha Kaye a wajenka mene abin bata rai,tunda ka lashe zabe Kai fa kace ba gaba,Murmushi Aslam yayi ba shiri ya dai tsaya sun gaisa sosai harda bawa Affan katinsa yace gashi idan kana so Watarana mu gaisa,Affan ma ya zaro katinsa yace ga nawa Wai ya nunawa Aslam shima fa babban yaro ne da aikin yinsa,Raudah sai kallon cikin Siyama takeyi dama itama ta samu nata da Affan,gidan su Siyama zasu shiga Wanda dole sai ka wuce ta kofar gidan su Nusaiba,Nusaiba tana tsaye tana ta faman kallon Aslam Kamar mayya,Aslam ya gane itace harda shafa cikin Siyama suna tafiya,Siyama tayi dariya tace dan Allah ka kyale babyn nan haka kullum hannunka na kai,Siyama tace Nusaiba kece dama ko magana haba Nusaiba,Nusaiba an sakko tace Charity sannunki tana tabe baki ,Hannun charity ya rike Suka Shiga gida me kyau Nusaiba bata gane gidan su Siyama bane yanda Kawu ya gyara gidan yayi kyau ya canja sosai,haka ta Shige gidansu ta iske kannenta duk basa nan sun tafi sashen amarya,Shehu Yana dakinsa yaji sallamarta,Fitowa yayi yaga Nusaiba a gabansa ta zube gudun Kar ya koreta ta fashe da kuka ta rike kafar Shehu tana dan Allah Abba ka yafe min na tuba wlh bazan sake biyewa Mama ba,Shehu yace Nusaiba ki ma biye Mata ni ba ruwana kece a wahale,Ka yafe min Abba yace dama ni bana Fushi dake na yafe Miki, Yar da na Haifa ai kullum Addua Zan Miki Allah ya shiryeki ,Nusaiba taji Dadi sai ta share waje ta samu wajen Zama duk da haka bata leka wajen Amarya ba abinci taci duk Yan uwan Shehu sun tafi itace ta gyara gidan tsaf tare da kannenta tayi wanka,Shehu Kuwa ana yin Sallar Isha ya wuce bangaren Amarya landlady anci gayu ta hade cikin rigar baccinta pink ta Sha kyau na musamman,Shehu duk an gigice anga sabon jini,kajin da ya siya Mata sai da ya siyawa yaransa ya basu nasu na Amarya Kuma daban,Nusaiba yaushe rabon da taga nama tana Kauye sai yanzu,kannenta su Ameer sai dariya suke kyalkyala mata. Landlady wayayya ce wacce tasan ta Kan maza ga iya shagwaba da kisisina Shehu tun a wajen kwanciyar aure yasan sai yanzu yayi aure da haukarsa Kawai yake yi,washe gari kasa Fitowa yayi ko kafar gida Yana ta soyayya, Landlady girkinta tayi Nusaiba itace tayi nasu girkin ita da kannenta,da yamma Kuwa sai ga Shehu a kitchen ya ajiye hula a gefe Yana taya amarya wanke wanke,Yana gamawa yazo Yana yanka Mata Alayyahu,yau ma Shehu kwanan farin ciki yayi sun gurji juna shi da Landlady gaba daya Shehu ya susuce ya samu mace Yar gyara wacce tasan kanta,Satin Landlady daya ta Fara girki da su Nusaiba duk da haka Nusaiba bata taba shiga gidan ba sai da ta gaji taga kannenta sai shatara ta arziki Aunty Amarya take musu amma banda ita,haka da Yamma tayi wanka ta shirya ta Shiga bangaren Amarya a ranta tace gaskiya Aslam bashi da mutunci mutumin nan ba karamin makiri bane shine yayiwa Amarya wannan mu Kuma ko oho Nusaiba harda goge kwalla ta shiga Palo ac da kamshi Kawai ke tashi,Abbansu taji a kitchen suna ta Wasa da dariya da Amarya suna girki a hankali tayi Sanda Kamar barauniya ta leka kitchen din ta hango Landlady akan cinyar Shehu suna kissing,da sauri ta dawo baya tana rufe Ido ta zauna tana mamaki tace oh duniya ashe Abba dan duniya ne haka,Amarya ce tace naji Kamar yarmu na sallama ta mike ta fito tasan Nusaiba a hoto,Nusaiba tana ganin Amarya shegu kudi ba karya sai ta Mata kwarjini har kasa ta rusuna tace Ina yini Aunty,Aunty ta amsa da fara'a tace sai yau Zaki zo min kema kishi kike taya mamanki ko banga laifinki ba,Nusaiba mayyar masu kudi tace ba haka bane tana sadda Kai Kamar ba Nusaiba ba ,Shehu ne ya fito,Nusaiba tace Sannu Abba tana Zama a kujera ya amsa da fara'a sai rawar kafa yake sabo da anzo gaida Amaryarsa,bedroom ya shige Landlady tace Nusaiba jeki kular min da abincin can bari naje,Nusaiba ta Shige kitchen Itakuma Amarya ta wuce ciki tare da Shehu suna soyewarsu aka bar Nusaiba da aiki,Wasa Wasa sai gashi Amarya bata aikin kirki a gidan nan gaba Daya kusan Nusaiba ce ta Zama Yar boyi boyi ita take Kai kanta tayi ta dirzar aiki ba tare da an sakata ba sabo da Landlady tana da kudi. AsmaBaffa [4/1, 5:47 AM] Sis Asma: 🛢️AUREN MU🛢️ 96-98 Official By AsmaBaffa Page naki ne FUTURE RM Nusaiba gajiya tayi da rashin mahaifiyarsu ta tattara kannenta suka koma gaban Abbansu tare da durkusawa,Shehu yace Yaya aka Yi ne? Nusaiba tace zuwa Muka Yi mu roke ka dan Allah Abba ka dawo da Mama gida badan halinta ba ko don mu,Amarya Landlady tana ji,Shehu yace babu ruwanku Kar na sake ji Kun min maganarta Indai maganarta Zaku kawo min to karku zo inda nake,ku tashi ku bani waje ya musu tsawa suka mike sum sum Suka bar wajen,Nusaiba babu abinda take da buri face ta samu mijjn aure ko ba me kudi ba amma ta rasa me sonta yanzu duk irin farin jininta yanzu babu ko wani ya fara tunanin zuwa a unguwar za a fada Masa gaskiya halin Nusaiba da

Table of Contents

Chapters

71 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71