Skip to content

Chapter 35

Chapter 35

AURENMU Book One Complete Hausa Novel 1,248 words 0 views Progress saved
Download Book

tace Aisha me Zan gani ba dai an sakeki ba? Aisha ta fashe da kuka,Umma tace ba kece da kuka ba nice da kuka Aisha,yanzu Zaki zo ki addabeni ki buwayeni ki damu rayuwata,ki dinga wulakantani nayi nadamar rabaki da gidan mijinki Farooq,Nice na zugaki laifina nane dama ance Indai yarinya ta wuce zaman gaban iyayenta to idan ta dawo sai ta kusa dukan uwarta,Aisha tace ai kece Kika jawo min yanzu gashi nice a wahala kalli yanda na koma sai kace Jimina,wa yace ki yarda da shawara ta,ai da kina da hankali tunda ni Kika ga na kauce Hanya sai ki gyara min ai Nima ban wuce ayi min fada ba tunda na Fara manyanta kullum kwakwalwata sake kwancewa takeyi Saura kadan Aisha tayi dariya yanda Umma tace kwakwalwarta ta kwance, Aisha ta kwashi kayanta ta koma ciki wani sanyi taji a rayuwarta. Farooq Kuwa da Nabeela amarci suke Sha amma zuciyar Nabeela Babu dadi tunanin Affan takeyi Ina zata ganshi ta nemi yafiyarsa sanna son Affan take kamar hauka ko sex sukeyi da Farooq sai ta tuna Affan take gamsuwa sunayi tana ganin Farooq kamar Affan ne ke Mata sai tayi ya jin Dadi,Indai bata tuna Affan ba to baza ta gamsu ba ranar, gashi kunyar Affan take tunda yazo ya samu an daura Aurenta da dan Uwansa bata sake farin ciki ba a rayuwarta wannan yasa ta tsani Yusuf gaba daya basu zauna lafiya ba,ta dinga nunawa Yusuf halin ko in kula tun Yana binta har ya gaji Suka Fara fada kullum basu da kwanciyar hankali har ya koma wulakantata karshe ma ya saketa hakki ne ya Kama su kwata kwata Allah bai bari sunji dadin auren ba,Farooq Kuwa zuciyarsa tana ga Aisha Kawai gangar jikinsa ce a wajen Nabeela nan ma dai Nabeela bata Yi dace ba. Kamar yanda Raudat tace Affan ya shirya suje garinsu ranar na zuwa wani wanka Affan ya dauka da jakarsa ta kaya me kyan gaske in ka ganshi ka rantse turai zai tafi,Raudat kuwa wata doguwar Riga tasa na leshi dinkin manyan Mata masu ji da kansu ta Sha dogon takalmi da Jakarta ta kayan sawa sai hand bag komai coffee and white,tana Fitowa ta mikawa Affan flight ticket,wani yaron Affan ne yazo a motar Affan ya kaisu airport suka shiga jirgi ranar farko kenan da Affan ya Shiga jirgi tsabar gayu sai kace Wanda ya shekara dari Yana shiga yanda yake tafiya Yana gabatar da komai nasa,ga sit dinsa ga na Raudat suna zaune idan ya saci kallonta sau daya sai ya dauke Kai itama sai ta juyo ta saci kallonsa haka suke faman Yi har suka sauka lafiya,suna zuwa wani driver ne da mota me tsada Yana jiranta,suka Shiga mota da Affan ta Fadi sunan wani Hotel a garin ta rigada ta Masa booking Bai kashe kwandala ba,suna zuwa Hotel ne me tsada da kyau har room dinsa sannan tace Zan tafi zan dinga kawo maka abinci daga gida idan Kuma kaci a nan baka bukata ka fada min a waya tana kallonsa tana Murmushi,yace to sai ki ta min abu da kudinki karfa Watarana a min gori ni bana so nasan halin Mata bana Jin Dadi ki dinga kyaleni Ina biya Mana please bana so idan ba Haka ba Zan koma gida Kawai kin maidani yaro,Dariya tayi tace afwan to ka huta ,yace karki kawo min abinci nifa ba yaro bane ba Kuma duhun Kaine dani ba sannan Ina Jin turanci,tace to sorry na daina tace zanzo da dare muje yawo ta Kai hannu zata ja Masa gemu ya goce yace wannan fa raini ne ke ba matata ba sannan ba budurwata ba Zaki lalatani ya juya tare da rufe kofarsa,ta tafi tana Murmushi dama tsokanarsa tayi tasan fadin ransa. Yau Kawu yana dawowa Siyama ta masa Sannu da zuwa ya amsa ta karbi kayansa ta Kai daki sai tsarabar Kauye lafiyayyen nonon shanu kindirmo cikin katon wani bowl,Kwan zabi,etc Aunty tace Sannu da zuwa Suka shiga daki Siyama kuma ta Kira Aslam,kashewa yayi tare da kiranta back sallama tayi ya lumshe Ido yanda muryarta ke tafiya da Imaninsa,inyini yaya ya aikin,lfy Alhmdllh ya furta Yana gyara kwanciyarsa saman kujera tace Kawu ya dawo yanzu,yace Allah mun gode maka tunda ya dawo lafiya daga nan Suka fada hirarsu ta masoya har Kawu ya fito yayi wanka tare da gabatar da Sallar Isha Yana Jin Siyama ta makale murya tana ta yiwa bawan Allah shagwaba,bata San yana jinta ba,tana kwance a tsakar gida suna Palo shi da Aunty ita Aunty ma bata ji me take cewa ba amma Kawu hankalinsa na kanta,karaf yaji tana cewa kasan Ina sonka nima amma sai kayi ta cewa Kai kadai kake so na gobe zaka Zo da Yamma,yace bayan kin daina zuwa layin mu ma,tace zanzo ne ,Kawu ya zaci Siyama gidan Farooq take shiga bai san ko taje unguwar ba a waje suke Zama Kuma tunda Nusaiba ta bar gidan sau daya taje,Kawu a ransa yace wato Siyama ba Wasa take ba zuwa zatayi ya Mata cikin shegen amma gobe zai gani idan zata fita, gajiya yayi da ji ya fito,Siyama tana ganin ya fito da Fushi tace Zan kiraka Yaya ta kashe wayar amma sai tayi kamar bata kashe ba taci ga da cewa ka jirani gobe zanzo gidanka da Yamma,Dariya tayi tace hmmm sai dai na zo,kawu yace Siyama zo magana tayi Aslam Kawu na kirana ka kirani anjima Kawu ne ya daka Mata tsawa Allah yasa dama ta kashe wayar, yazo ya fisge Wayar tunaninsa wayar suke da Aslam ya Kara Wayar a kunne Yana masifa yace duk abinda ya samu yata Kaine wallahi Matukar aka lalata min yarinya Kaine ya Danna wajen red ya kashe bai kula ba dama a kashe take,yace ke Kuma Siyama duk abinda zaku yi kuyi bazan bashi ke ba ya juya ya koma daki. Siyama ta fashe da kuka kasa kasa karshe ma ta koma dakinta ta kwanta,washe gari Kawu ya kafa ya tsare Yana jira yaga ta Ina Siyama zata fita,4pm yaga tayi wanka ta shirya ta saka hijab tace Aunty zanje karbo Miki Humrar, Kawu yace gidan ubanwa Zaki je,Ashe da gaske kike Siyama gidan Namiji Zaki je,tace nife ba can Zan je ba jiya ma kawai fada nayi amma na kashe wayar,Ni kike tsokana sabo da ni sa'anki ne ya taso zai sharara Mata Mari tace a'a bada Kai nake ba da Kaina nake tsokana,yace to daga yau ba inda Zaki je na hanaki fita ko kofar gida Kuma ki fadawa Aslam din Kar ya sake zuwa min gida tunda ba alheri kuke shukawa ba,ke Zaki iya sani inyi abinda banyi niyya ba. Siyama bata ce komai ba tace kayi hakuri kawu ta koma ta zauna a dakinta,Aunty ta fito tace wallahi abinda kakeyi ba tsari gaskiya duk abinda yaron nan yayi maka idan yaji ka hanashi zuwa gidan nan ai mutuncinka zai zube dan Allah karka Yi haka ai da kunya,Siyama baza ta aikata ba wlh ba abinda zai faru me yasa kake haka wai,Kawu ne ya mike ya fice,Yana fita ya hadu da Maman Nusaiba ta dawo daga unguwa ta Masa kallon banza tace oh Mallam Dauda sai muka ji Kuma wannan matsiyacin zaka aurawa Yar rikon

Table of Contents

Chapters

71 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71