Chapter 18
Chapter 18
kalaman banza da bai dace taji ba amma za a dinga Yi a gabanta wasu ma su dinga janta da Harkar banza irin wannan ke sawa Yan talla suke lalacewa yau da gobe zata Saba har ta daina kunya,sannan ga gogayya da maza mutane manya daban daban zai sa idonta ya bushe ta dawo Bata da kunya Kuma bata tsoron kowa kadan daga illar talla ga ya mace,Aslam yace hakane Nima sai yanzu naga hakan, Uhm ta furta tana kallon Wayar hannunsa me tsada Sabeer ne yayi sallama tare da shigowa shima,Sai yau Siyama taga Sabeer,gaida shi tayi Yana binta da kallo ya mikawa Aslam Hannu suka gaisa ya zauna yace ko kece Siyaman? Charity tace ae yace Sannu mun gode fa,Sabeer ya dameta da kallo,Aslam Yana kallonsa,Siyama mikewa tayi tace zata tafi,sai yaushe? Aslam ya tambaya tace sai an ganni Kawai yace muje na rakaki Suka fito tare suna tafiya a hankali suna hira tana ta bashi dariya. Nusaiba aka sauke a taxi ta tsaya tace Charity sai da Kika sake biyo mu Nan dan masifa yanzu ba kudin da za a baki to,Tsaki Siyama ta ja tare da furta banda lokacinki Nusaiba,Nusaiba ce tace zo wahalalliya Ina son magana dake,Charity ta ja gefe Nusaiba tace tunda taku tazo Daya da Aslam dan Allah kisa ya sakeni,ki fada Masa Ni takarda ta nake so ya sawwake min na gaji bazan iya rayuwa da shi ba,Siyama ta kalleta tace ki kalli Namiji irin Aslam hadadden mutum Kamar shi yayi kansa kice Wai kin gaji da shi,ae dan Allah ni na gaji bana son auren ya sakeni,kinfi so ki Zama bazawara ae gwara haka ke karuwai ma suna nan su da karuwanci suke Yi suna zaman su a duniya Lafiya bare ni Dan an sakeni na Zama bazawara,wlh idan Bai sakeni ba Kara Zan kaishi wajen Yan Hisba,Siyama juyawa tayi tare da komawa wajen Aslam ta fada Masa abinda Nusaiba ke so saki,yaji Matukar ciwo ya danne,Yana komawa gida tace wallahi yau ba zaman lafiya sai ka sakeni,Aslam yaki kulata rigarsa ta rike ya samu ya kwashe ta da Mari ya sake zabga Mata Mari Wanda ba shiri ta sake shi tana kuka wallahi sai ka sakeni,yace baki ji kunya ba mahaukaciya aure wata hudu na sakeki Baki da hankali,kuka Nusaiba takeyi sosai yaki sakinta haka Suka kwashe satikai kullum da masifar da zata fito da ita a saketa sabo da bai da kudin da zata karba yanzu Kuma sai takalo rashin mutunci iri iri shi Kuma yaki sakinta,harda daina kwana a dakinsa ta dawo palo a nan take kwana kullum. Yau Mama ce tazo gidan tana zuwa ta saki ihu a palon tace a Nan yata take Zama daki nawa ne? Nusaiba dake zaune tace daya,Daya tal yanzu idan da kwana zanyi bani da wajen bacci kenan tab amma Aslam ba karamin azzalumi bane ka ajiye bawa me rai a nan, Nusaiba tace zauna Mama bari na Miki girki dama bana dafa Masa abinci,Mama tace kinyi dai dai tana zaune Nusaiba ta dafa Mata shinkafa da Miya harda kazar da ya siyo jiya Mama taci ta tauna Kashi ta sha ruwa me sanyi ta sake zuga yarta tace Kai Kai kamarki a wannan gidan daki Daya sai Palo kujerun ma ba na kasar waje bane ba Yan Dubai ba Yan nan Kano ne,Nusaiba tace kalleni Mama yanda na girma nayi kiba nayi wani fresh kowa ya ganni yaga kalar hutu amma matsiyacin ya makale yaki sakina,gida ko filin tsakar gida babu kalli tv din ma karama sai kace ta Office din principal din makarantar sikandire cewar Mama,wani takaicin Aslam ya sake rufe Nusaiba,Mama Kuwa sai sake zugata takeyi,tashi tayi ta leka kitchen ai wani ihu ta saki tace hodijam inji Dan fillo wannan kina samun balance kuwa? Sai dai manage Mama shi yasa bana shiga Suna haka Aslam ya shigo sanye cikin wata shadda Yar ubansu grey color cikin kayansa na baya masu tsada ya saka ya shigo da takardun makarantarsa,Mama ta Bata rai tare da kallonsa shekeke ta tabe baki tace kamar gaske akwai kudin Kai karya bata Yi ba,Aslam ko kulata baiyi ba ya wuce bedroom dinsa,Mama tsabar rashin son zaman lafiya tace sai na dawo kwana zanzo na kwana biyu haka,Nusaiba tace Allah ya nuna mana Mama sannan ta fita ta tafi gida,Aslam ya fita bai dade ba ya dawo da Leda a hannu yayo cefane harda Naman rago da yawa,tun kafin yayi magana Nusaiba tace wlh sai dai ka dafa da kanka Kuma abinci daga ni sai uwata na dafawa mun cinye,bata ko rage Masa ba gashi Yana Jin yunwa Charity bata da waya bare ya Kira ta, tashi yayi ya fita bai ko saurari Nusaiba ba ya shiga Napep zuwa gidan su Charity Yana Fitowa daga Napep Suka hadu da Shehu Baban Nusaiba,Shehu da fara'a da murna yace surukina gobe nake so nazo gidan naka jaje wlh ashe haka Abu ya faru marar Dadi,Aslam ya duka zai gaida shi yace tashi tashi Aslam ubangiji ya maida alkhairi,yace ameen,Shehu yace ya Nusaiban iceko lafiya kuke? Aslam baiyi kasa a gwiwa ba ya zayyanewa Shehu komai,Shehu Baki ya rike yace wallahi ban San me ake ciki ba abin wato har ya Kai haka,duk uba bazai so a saki yarsa ba amma tunda Nusaiba take maka haka na baka dama ko nine iyaka abinda Zan iya kenan na saketa,Dan Allah kayi hakuri Kai mutumin kirki ne,har gobe Ina ganin mutuncinka Kuma bazan fasa zumunci da Kai ba ko da ace baka tare da yata,Aslam yaji dadi da farin ciki,Shehu yace ka kyale Maman Yarinyar tunaninsu daya taho muje gidan Yar uwata ka huta a can,Shehu yaja Aslam zuwa gidan Yar uwarsa Alawiyya ba nisa da gidansa ita me rufin asiri take aure komai nasu me kyau ne,kana ganin Aslam zaka Yi tunanin da kudinsa tunda Yana da sutura,palon Alawiyya Suka shiga babbar dattijuwa yace mijin Nusaiba ne,Alawiyya tace Shehu ai na gane shi,Aslam ya gaishe da ita ta fita ta kawo musu lafiyayyen girki Aslam dama yunwa kamar zai mutu baiyi Kara ba ya zage yaci ya koshi shi da Shehu Kamar ba surukai ba suna yin Sallar la'asar Aslam yace zai tafi Shehu ya rakoshi har kofar gida Suka Yi sallama shi ya koma cikin gidan wajen Yar uwarsa,Aslam Kuma ya karasa kofar gidan su Charity,Yana tura yaro ciki sai gata ta fito zata siyo manja,taga Aslam ba zato,Murmushi ta saki kayatacce tace Ina yini ya amsa da fara'a tace Ina kaje haka? Yace cefane nayi tace baza ta dafa ba nama ne zai lalace shi yasa nace Bari na kiraki ko ki dafa min ko kizo ki dauka ki kawo gidanku kuci Kar ya lalace,Charity tace nama guda wa yaki dadi har kasa yawuna ya tsinke,ya saki Murmushi ba shiri,ciki ta koma tace Aunty ga kudin ki aiki yaro Aslam yazo nema na,Aunty tace Kuma dan Iskanci sai ki dawo da kudin,Bata tsaya ji ba tace ki fadawa Kawu matsala ce a gidan zanje wajen Nusaiba,Aunty tace to a kula dai tace to,ta fito tare da cewa muje Suka fito tare Suka Mike suna tafiya suna Hira har yaji sanyi a ransa Titin kwalta zasu tsallaka Yana ta tunani ya tafi bai kula da mota ta
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71