Skip to content

Chapter 39

Chapter 39

AURENMU Book One Complete Hausa Novel 1,259 words 0 views Progress saved
Download Book

yayi ai suka Yi dariya ya Mata sallama ya tafi. Siyama ta shiga gidan harda durkusawa Kawu tace Mahaifina ka yafe min,sai yau Wai zata mahaifinta ta bawa Aunty dariya, tace Kawuna ka yafe min na tuba bazan sake ba dan Allah Kar kayi Fushi dani sai Allah ya tsine min na tuba,tashi ki bani waje Yar banza fitsararriya tunda nace zan bashi ke Kuma mene na damuna,Siyama tace Kawu ka sa min Albarka to,duka ya Kai Mata ta tashi da gudu tana dariya ta koma dakinta sai tsalle da murna harda cewa Babana dake lahira yayanka Amadou Yana rike yarka Amana yanzu,su Kawu suna jinta tana ta hauka iri iri. Raudat bayan taje gida ta huta suna ta hira da kannenta kanana su biyar da Mamansu,haka Babansu ya dawo daga Office tana murna yace a'a Raudat zuwa haka ba sanarwa tace Papa nayi missing naku shi yasa nazo ranar Monday Zan koma,yace Alright ya aikin naki? tace Alhmdllh Papa na iskeku lafiya yace lafiya lau,ciki ya shiga ita Kuma taje tayi bacci ta huta da Yamma lis tayi wanka ta fito cikin hadaddun kayanta English fited gown ta Sha me dogon hannu,kyau Kam ta Sha shi tayi rolling da mayafinta,hand bag ta dakko ta fito tare da yiwa Umminsu Sallama tace Zan dan zaga gari,Ummi tace to a dawo lafiya ta koma part din Papa tace papa Zan Dan zaga gari bani mukullin farar motarka please yace duba kasan pillow, ta duba ta zaba a ciki sannan ta Masa sallama ta fita abinta kannenta suna Aunty zamu je tace ba Zan je da kowa ba Affan ta Kira a waya ya Gama bacci ya tashi yayi wanka Yana shiri ta Kira ya daga tace fito mu tafi,kana nan Kaya ya Sha wani wando pencil creazy da shi me kyan gaske sai riga me Fadi Yar sarau sarau bata da kauri daga baya ta zobe baya yafi gaba tsayi Suma Tasha gyara sai da Raudat ta gaji da jira daga cewa Kaya Kawai zai sa ya gama komai Yana ta kalailaitar jikinsa ya gama ya fito Yana kamshi ana taku dai dai da wayarsa me tsada,tun daga nesa take kallonsa yanda ya Sha kyau Kamar a turai,Raudat harda kwantar da kanta a saman sitiyari tana tunaninsa horn tayi kadan sannan taci gaba da kallonsa har ya bude Gaban mota ya shigo,duk kamshin da takeyi nasa sai da ya doke nata,yace Hajiya Aunty,tace dan Allah ka daina ce min Aunty ni bana so ka girmeni sosai ka dinga ce min Aunty,yace alright Yana dariya an gama Hajjaju ta,ta sake kallonsa kamar zata Yi kuka sai kace tsohuwa,yace to Raudat shike nan, tace haka gatsal kuma,yace to me zance? Ina laifin ma kace min Queen,Queen dina my Queen ya furta tayi Murmushi tace naam Affan International yanda taji Sayyeed Abokinsa Yana fada Masa,Dukkan abokansa sai kace Affan International ake ganewa,dariya yayi yace wannan fa Yan school ne suka saka min,Affan International. International na wanka ko? Yace yes tana driving tace ni Kuma Affan Appointment,dariya ya saki suka je wani hadadden wajen cin abinci acan Suka ci Suka Sha sannan ta Kai shi wuraren shakatawa suna ta yawo cikin nishadi,Affan wani Kara son Raudat yake ji Kamar ya hadiyeta, sai wurin goma ta kaishi masauki baya so su rabu itama haka, Suka zauna a motar juyowa tayi kadan tana kallonsa shima ita yake kallo, hannunta ya rike a hankali tsigar jikinsu ta tashi kasa hakuri yayi tana mazaunin Driver a haka ya rungumeta yace Ina sonki Raudat ya sake kankameta Yana shakar kamshinta,jikinta ta janye yace please ina kaunarki na Dade Ina sonki na kasa fada miki dan Allah muyi aure,Raudat tace kana saurayi Ina bazawara ai bazai yuwu ba Affan International,yace ni ba komai ina sonki haka ba ruwana da wani bazawara Annabi ma ya auri Zawarawa bare ni,Raudat tace ku da samarin zamani ne sai budurwa,dan Allah ki daina fadar haka mene a virgin Ni ke nake so,Raudat tace ka bani lokaci to,zuwa yaushe? Koma yaushe ne in Naga ka cancanta shike nan, Affan yace au yanzu ban cancanta ba sai ma kinyi tunani,ya kalli Kansa yace mene Nawa bakya so ko bani da kyau ko dirina bai Miki ba? Raudat tace wane mutum akwai wacce ta Isa ma tace baka Yi ba,Zan baka amsa ai yace Allah yasa naji Alkhairi tace ameen ya bude mota ya fita tace sai gobe karfe nawa zanzo? 11am lokacin na tashi a bacci,tace gobe zamu je ka gaida su Ummi da safe sai kace ranar zaka koma kaga washe gari sai mu tafi,Affan yace ban gaji ba mu Kara kwana biyu tunda kullum zamu dinga yini tare tace no Monday da aiki yace ni na sanarwa Oga ai farko sati Daya Kika ce,kasan aikinmu ko yaushe za a iya Neman mu,Aslam yace gaskiya gwara aikin gomnati bazan iya barinki ki dinga fita haka yanda Kika ga dama ba,a Haka suka rabu Raudat ana ta murna Kamar zata kashe kanta. Washe gari Affan harda saka wani yadi me tsada me karamin dinki ya Sha kyau sosai cikin fararen kaya za aje gaida suruki,Raudat tazo a wata kalar motar har room dinsa ta shiga tana shiga ya mike,ya ganta da ledan kayan abinci na take away yace ai na karya Ni naci abinci,a Ina? Yace fita nayi na samu waje tace nace kaje ne da zaka tafi kaci abinci a wani waje Yan garin nan fa Mata mayun maza ne so kake wata ta nace mak..tunawa tayi ta dauke wuta duf harda fuskewa tace hmm to ba komai fito muje gidan namu,Aslam ya fito Yana Murmushi ana kishinsa,katafaren gidan su Raudat suka je dama ta fada a gida wani da suke compound daya zai zo ya gaishe su yazo garin,Raudat har ciki ta Masa iso,Ummi ta fito ya durkusa tare da gaidata tana fara'a ta amsa shima Papa yazo Suka gaisa Yana cewa na gode na gode fa shi Kam Affan ya Masa ya kwanta Masa a rai, Ummi harda Zama ta saki jiki suna ta hira da Affan,shi Kuma an wani nutsu Kamar ba shi ba,kannen Raudat Suka zo Suka gaida shi,last born Dan yaro Affan yace boy zo Nan ya dauke shi yace ya sunanka? yace Irfan,Yana tsokanarsa ya Dan dade har yace zai tafi ya rabawa yaran kudade ya fito Raudat ta rakashi,tace zata maida shi masauki yace da Kansa zai koma shi zai Gane. Kwanan su Raudat biyar a garin nan suna shakatawa kullum tare da shi suke yini kwanciyar bacci ke raba su,ranar kwana na biyar Suka dawo gida Kano,Raudat tana shiga part dinta ta hau gyara shima haka,ta Riga shi gama aikinta shi ya fita kalailaitar masifa,Yana goge kujeru ta leko ta window ya duka ta wajen saitin windown ta dan yakushi bayansa ta koma ta buya ya duba yaga ba kowa ya koma yaci gaba ta sake lekowa da cokali ta dan karci bayansa ya juyo da sauri ya kamata dariya Suka Yi yace dama naji ajikina kece ai tunda Kika yakusheni ban ji zafi ba naji wani Dadi da shock nasan kece Affan da karya yakushinta ma Wai dadi ba zafu,Raudat har yau bata bashi amsar tana sonsa ba sai aji take ja Masa tun Yana tambaya har

Table of Contents

Chapters

71 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71