Skip to content

Chapter 24

Chapter 24

AURENMU Book One Complete Hausa Novel 1,245 words 0 views Progress saved
Download Book

Baban Sabeer Doctor ne,Sabeer Yana aiki shima a bangaren ministry of Finance Yana da motarsa me kyau baiyi aure ba amma Yana da budurwarsa Na'ima gaf suke da aure,Aslam Yana zuwa ya bawa Sabeer labarin saki,Sabeer yace Alhmdllh Kai Kam ai ka samu hutu dama Siyama ka aure,Aslam yace kawarta ce fa ni bayan nan ma yanzu ban shirya aure ba sai na huta,Sabeer yace hutun me Kuma yanzu ka Saba da mace gwara ka Fara Shirin aure dan Watarana zaka ji Kawai dumin jikin mace kake bukata,Sabeer yace rabu dani Kai na gaji,Nabeela ce ta shigo dakin Sabeer tare da ajiye musu abinci da lemo,Nabeela ta Kaduna tsohuwar budurwar Affan mamanta yayar Maman Sabeer ce ubansu daya,Nabeela watanta biyar a gidan mijinta Yusuf yayan Affan ya saketa. Tana fita yace ko na hadaka da Nabeela Yar uwar mu ce bazawara sakin wawa ce kwana nan tayi barin Yan biyu bayan mijinta ya saketa cikin ya zube da zaka aureta ma,Aslam yace hmm amma Sabeer ya dage Yana ta faman yabon halayen Nabeela Yana so lallai sai ya hada aure tsakanin Aslam da Yar uwarsu Nabeela,yace har Babarta suna nan gidan mu sun dawo nan da Zama gaba daya sabo da can Kaduna su kadai ne a gidan,Yarinyar nan ta Sha wahala a hannun tsohon mijinta,Sabeer bai San hakkin Affan ne ke bibiyar Nabeela ba,Aslam dai Yana Jin Sabeer. Yau Raudat Fitowa tayi zata siyo abu Affan ya fito da 3qtr da riga Armless ya ganta Murmushi ta Masa yace Hajiya Aunty Ina kwana,yau nice Hajiya Kuma Aunty a'a Kaine Yayana,Affan yace baza ta sabu ba bindiga a ruwa dole kece Aunty kuma Hajiya,yace Zaki iya sawa a toshe window din dana hada mana ke macece bai dace ba Kuma ba muharramata ba,Raudat tace a barshi Kawai Zan saka labile yau yace hakan ma yayi yanda kike so,tace Ina zaka je ne Haka ko Appointment ne? Murmushinsa me zauta Yan Mata ya saki yace ai banyi Shirin fita ba kalleni fa a haka Zan fita shago Zan je na siyo kayan tea nawa sun kare,Raudat tace nima can zani yace aha yayi gaba abinsa yana tafiyar gayu,Raudat daga baya ta karasa tana Shiga ciki ta dinga jido manya manyan Madara na gongoni kayan shayi na kirki komai ta hada ta Mika ATM card dinta aka zare kudin ta mikawa Affan katuwar ledar kayan tace gashi ka huta siye,ya kalleta ya kalli kayan yace Allah sarki Ashe mutuniyar kirki ce ke ban sani ba ta gari ce ga kamun Kai ba ruwanki da kowa da wata ce da yanzu mun gaji da ganin samari iri iri,Raudat tayi Murmushi kawai,ya karbi ledar yace gaki da kunya Kuwa Allah ya Miki Albarka ya karbe Kaya ya Kara gaba abinsa. Liman ne ya samu Affan yau bayan Sallar asuba yace yaya budurwar taka Kuwa na jika Shuru? Affan yace naje ta wulakantani bani da kudi Wai, Liman yace da zaka yarda da na baka manager a gidan Mai na dana gama ginawa kwana nan,Affan yace me zai hana na karba manager fa na gode ubangiji ya Kara girma,Kamar Wasa sai ga Liman a cikin gidajen mansa ya bawa Affan manager a guda daya,Wanda Affan me zamarwa a shago ya sanarwa suka Yi sallama ya taya Affan murna Affan ya koma Zama a office dinsa Dake cikin gidan mai ai tunda ya fara Kama kudi wanka ya ninka na baya amma Liman Yana ganin gaskiya Yana ganin aiki da ci gaba a harkar,farin ciki yasa liman ya siyawa Affan Mota dalleliya ta matasa,Affan ya Karo wulakanci,ba ruwansa da Raudat yanzu sun daina fada baya shiga safgarta itama Haka sannan window dinsu ma ta saka labile,Affan Kara rike aikinsa yayi Hannu bibiyu sun Zama kamar Da da uba tsakaninsa da liman sanadin zuwa masallaci Bayan kwanaki Raudat kullum bata da aiki sai tunanin Affan da shi take kwana da shi take tashi tun tana jurewa har ta kasa ta window take zuwa ta dan bude labilenta tayi ta leken Affan tana kallonsa tana Jin dadi a ranta. Taji Sanda ya shigo da motarsa da sauri ta bude labilen window dinta kadan ta leka cikin palon Affan akan idonta ya shigo sanye cikin shadda Yar gaske laptop ce a hannunsa sai ledar take away na abinci a Palo ya ajiye ya nufi bedroom ai Raudat da gudu ta fada bedroom dinta ta window din ciki ta sake lekawa tana kallonsa tace na Shiga Uku meke damuna haka mutum bai damu Dani ba amma na damu da shi haka fa nayi akan Hussain na Kare a wahala,jikin window din ta bari ganin Yana kokarin cire kayan jikinsa Bayan wasu satikai Liman ya Kira Affan zuwa gidansa,Affan yaje aka Masa iso palon baki ya shiga Suka gaisa da Liman,Liman yace Affan na yaba da hankalinka da irin rike Amanarka tabbas na yaba akwai wata Alfarma da Zan nema a wajenka fatan zaka min, Affan yace Inshaallah bazai gagara ba,yace Ina da babban aboki Yana da yarinya budurwa ce amma nutsatsiya ce ta dace da kai idan ba damuwa Ina so na hadaku aure,Affan yaji ba dadi bai zaci haka ba shi Kam baya son auren wata mace ko wace amma idan ya duba abinda liman ya Masa bazai iya kin tayinsa ba haka baya so yace na amince Mallam ai Kamar mahaifine a wajena nasan baza ka min zaben tumun dare ba, Liman ya washe baki yace na gode da ka daukeni a matsayin uba mahaifi ubangiji yaji Kan iyayenku,Affan yace a Ina matar da Zan aura take? Liman yace a nan kano take Babanta ya Dade da rasuwa a hannun yayan Babanta take,Affan yace ka bani address sai na Fara zuwa zance,Liman ya fara karantawa Affan gidan su Siyama, gumi ne ya Fara ketowa Affan yace Mallam ya sunanta? Yace Siyama,Affan gumi yake gashi ya amsa bazai iya yiwa liman Musu ba har ga Allah shi sunan ma Siyama yayi Masa local a harkarsa ta gayu, jikinsa a sanyaye ya basar yace shike nan zanje abinda mukayi da ita zan dawo na sanar maka,Liman yace Alhmdllh ka taimaki marainiyar Allah tausayi suke bani Babanta abokina ne amini,Affan dai ya tafi gida jiki ba kwari. Raudat yau tana compound ita da Landlady suna Hira Affan ya shigo da motarsa a fusace yayi parking ya fito cikin bacin rai ya shiga part dinsa yana huci,Raudat ta tsura Masa Ido har ya kule, Landlady tace yau Baban wanka meke damunsa haka Kinga yanda yake fushi,Ni abin mamaki ma a Ina yake samun kudi yanzu Kamar fa yanzu yana zuwa wajen aiki duk da ba abinda ya iya sai karya amma a Ina yake samo kudin Kar dai ko barawo ne? Raudat ta bata rai tace Allah ya tsare min shi da Zama barawo Kuma Yana zuwa aikinsa babban aiki ma ki daina fatar Masa masifa ehe ta mike ta Shige part dinta da sauri tana yiwa landlady masifa,Landlady ta bude baki tace me nake gani haka mutanen da kullum basu da aiki sai fada amma yanzu sun daina Raudat ma wani Kare shi takeyi ita da take zaginsa tana gulmarsa yau taki yarda a aibata Affan harda Jin haushina uhm to meke faruwa tsakaninsu oho. Aisha bayan tayi idda tayi sabon

Table of Contents

Chapters

71 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71