Chapter 36
Chapter 36
ka sabo da ba yarka bace za a zalunci yarinya a bata me karayar arziki,da yarka ce ai da baka yarda ba,Kai Kam juya marar amfani,ai Kai hoto ne a duniya mutum mutumi tunda baka haihuwa mene amfaninka baka San ciwon haihuwa ba baka San zafin da ba,in Banda Kai kwangiri ne kana gani 'yata ta fito sai da muka sa ya saketa sabo da bakin talauci shine Kai zaka Kai Yar wani sabo da zalunci me za aci da Aslam,ka duba Nusaiba yanzu ta shiga daula fantamawa takeyi yanda take so, tsohon banza ta juya ta wuce,Mamaki ya Kama Dauda ya bude baki haka Kawai shi ba kulata yake Yi ba ta bude baki taci mutuncinsa haka ta tafi,yace irin wannan annoba ne ga al'ummar duniya wannan matar Shehu Yana fama ai fasa fitar yayi ya koma gida,Yana zuwa ya fara bawa Aunty labari kaf har gwadawa yake yanda Mama tayi Masa,Siyama ta kyalkyale da dariya ta dinga dariya tace hakkin marainiya ne,hakkina ne wlh a guji batawa maraya rai gashi Allah ya saukar da aya,wlh Kawu Ina jiye maka Kar rabo ya kasheka lokacinka baiyi ba,rabo kisa yake watakil sai baka raye za ayi,gwara ka hakura Kar lokacin zuwan 'ya'yana duniya ya matso kazo ka hana zaka iya mutuwa,Kawu tunawa yayi yanda akace rabo na kisa tsoro ya kamashi Kar ya mutu,Shuru yayi tare da lulawa tunanin duniya,Siyama ta dinga dariya ta mike ta ebo kindirmo ta zuba sugar tana juyawa tana cewa rai ,Kawu yayi Shuru Aunty tace ayi bawa da kafiya haba Dauda. AsmaBaffa [4/1, 5:47 AM] Sis Asma: 🛢️AUREN MU🛢️ 56-60 Official By AsmaBaffa Page naku ne UMMY M MARYAM BASHIR MBELLO Dauda Yana zaune bai ce komai ba,Siyama tana kallonsa ko zata ji zai ce ya yarda amma sai ji tayi yace idan na mutu ma kwana na ne ya kare dama Allah yayi kwanana ya kare sabo da haka Ina Kan bakana Kuma karki sake yazo min gida,kwana uku Kawu ya hanata fita Kuma ya hana Aslam zuwa zance,Siyama duk ta Shiga duwa,Aslam ma Sai dai suyi waya a boye kasancewar yace sai ya kwace Wayar in ya sake ji suna waya,ai Kuwa Watarana Kawu ya Kama Siyama tana waya da Aslam,tana tsaka da waya sai ga Kawu Katsam ya Miko Hannu yace bani Wayar,Siyama tace Yaya Aslam karka kirani idan kaji Shuru Kawu yazo zai kwace Wayar,Aslam yace alright bashi I love you karki yarda a raba mu please,tace Inshaallah Muna tare har abada,Wayar Kawu ya fisge ya kashe ta gaba Daya ya juya ya tafi da wayar, Kawu Yana Fitowa ya fice daga gidan,Siyama ya bari tana kuka Aunty ce ta shigo ta zauna a gefen katifar Siyama tace kiyi hakuri Siyama,duk aure da Kika gani idan aka Yi sak ba wani kalubale to bai ma fiye Danko ba ko Mene zaka Nema idan da nasara sai an samu matsaltsalu sai an Sha wahala,abinda nake so dake kici gaba da addua idan Aslam ne Alkhairi Allah ya baki shi idan Kuma ba Alkhairi ne bane Allah ya zaba miki mafi Alkha....ba wani mafi Alkhairi Aslam ne Alkhairi na Kawai idan ana son zaman lafiya a bashi ni tun kafin na kangare na daina Jin magana gwara ma ki fadawa mijinki tun kafin na Fara fetsara a gidan nan,Aunty tace to fa ku Yara idan kuka tsunduma bakwa Jin Kira ai sai kiyi tunda bakya Jin magana.. Siyama ranar haka ta yini sukuku ko aiki bata taya Aunty ba,Aslam kuwa gidan da Mum take yaje ya sameta a Palo ita Daya,bayan ya gaida ta,Mum tace Aslam kamar kana cikin damuwa kwana biyu Naga Kuma kamar ka Dan rame lafiya? Marairaicewa yayi sannan ya Fara bawa Mum labarin komai,ita Mum Murna takeyi danta ya samu mace,yace Mum kina murna baki ji me nace ba Kawunta yace bazai bani ita ba Kuma ya kwace Wayarta sannan yace Kar na sake zuwar Masa gida,Mum ta kalli Aslam tace Inshaallah zai hakura karka damu ka kwantar da hankalinka,Mum taya hankalina zai kwanta idan ban sameta ba fa ya zanyi,Ni ban taba son wata haka ba,ka kwantar da hankalinka nace Inshaallah zai hakura Kuma ko waye haka zaiyi a matsayinsa na uba babbar kawar yarsa dole ya hana,Addua zaka Yi sosai,Aslam yace yanzu Mum baza kije min ba? Wannan yakin naka ne Aslam ka dage kawai,Shuru yayi Kawai ya zuba tagumi ya tsinci muryar Mum tana cewa Amma na maka sha'awar Siyama,Ki daina sha'awar min Mata Ni kadai nake son abata Wai yaji haushi tace baza taje Masa ba, Mum ta dinga dariya tace to aci gaba da sonta lafiya,tashi ma yayi ya bar gidan. Bayan kwana uku Aslam duk ya wani fututtuke ya tashi hankalinsa ya rasa inda zai sa Kansa rashin Jin Siyama,itama bangaren Siyama haka. Zuwa Yamma Siyama da Aunty Suna tsakar gida saman katuwar tabarma suna Jin radio Kawu Yana zaune saman kujera aka sako wakar soyayya Siyama ta mike zaune tana saurar wakar Mawakiyar tace kaine tunanina,Siyama tana bada amsa uhmmm Aslam ne wannan wakar sak tamu, mawakiyar ta sake furta Kaine ruwan Sha na,Siyama tace me gardi ma ruwan, kaunarka tayi girma a zuciya tace tabbas haka ne Aslam dina,Zo ka kula Dani me so na inji me wakar, Siyama harda hawaye tana Jin wakar Kawu ya tsaya kawai Yana kallon ikon Allah shi da Aunty, kuka ta saki sosai tasa tafukan hannayenta tare da rufe fuskarta,Aunty tausayin Siyama ya kamata,tana shesheka tace amma Aunty ke da Kawu ba auren soyayya kuka Yi ba da alama baku San mene so ba,Kawu ta kalla tace Kawu kasan Kuwa me nake ji a raina ka tausayawa yarka Kawu ,shi kuwa ko kulata baiyi ba. Zuwa dare Aslam ya kasa daurewa yazo da Kansa gidan ya Samu Kawu ya tafi wajen abokansa Bayan Sallar Isha,Aunty tana daki sai Siyama a tsakar gidan zaune ta hada Kai da gwiwa,Aslam da Kansa ya shigo gidan ba Sako ba,tana Jin taku da kamshi ta dago da sauri,Siyama ta mike Zumbur tana kallonsa,tsoro take ji Kar Kawu ya shigo ya samu Aslam hannunsa ta ja da sauri tayi maza ta turashi dakinta,tana turashi ciki Kawu ya shigo gidan Aunty ma ta fito tayiwa Kawu shimfida a tsakar gidan Sabo da ana zafi a waje suke kwana,Siyama ta dora Hannu a Kai tana kallo Kawu ya kwanta,Aunty ma tayi nata shimfidar gefen Kawu ta kwanta,Siyama ta Fara tunani ta ya Aslam zai bar gidan oho,Aunty tace kin tsaya Mana a kai ke baza kiyi shimfidar ba? tace sai can anjima,Kawu yace bar algunguma ita ga Yar soyayya,Siyama dakinta ta Shige ta kulle kofa harda sa key sun zaci duk fushin soyayyar ne. Ta samu Aslam a katifarta a zaune,a kasa ta zauna shi Yana katifar tana Murmushi wani sanyi take ji Yana ratsa ta,kallonta yake sanye take Riga da skert na Atamfa masu kyau,Ina yini tace tana Jin kunya amsawa yayi kasa kasa,ya furta ya kike kwana biyu naga ma kalau kike ai ko missing Dina baki yi kawai cin abincin ki kike Yi kina koshi Ina can hankalina a tashe,Siyama tace ka taho min da wata Wayar? yace no Kawu ya hana muyi hakuri yanzu idan na baki wata zai ce mun raina shi bai kamata ba,Siyama tace
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71