Chapter 16
Chapter 16
haka tunda motar nan sun riga sun siyar,Nusaiba tana daga ciki a kulle ta saki kuka tace wlh dan damfara ne ya gudu da kudin,Aslam saman kujera ya zauna cike da bacin rai sai da yayi kwalla sabo da bakin ciki yanzu ya tabbatar Kuwa siyar da motar tayi,yana so ya siyar da su ya biya banki kudi yanzu ta salwantar da motar gashi tafi kowacce tsada,hawaye ne ya zubo Masa Sabo da bakin ciki wannan wacce irin kaddara ce haka,tashi yayi Kawai ya sa key ya bude Nusaiba ta fito tana kallonsa tace akan wata tsohuwar mota harda kwalla lallai ka cika me son kudi Kan bala'i,waccen irin marar Imani ce ke Nusaiba Charity ta furta ranta a jagule ashar Nusaiba ta dura Mata ta haura sama tana Jan tsaki tana cewa akan wata banzar tsohuwar mota. Cikin kwana uku Aslam ya tattara komai na kadara ya damkawa bank gida Kawai yake jiran ranar da zasu zo,Mum ma dubu dari Uku ta turo Masa daga can kasar da take Qatar, wasu kayan girkin ma babu a gidan yau Charity ta rasa me zata dafa kwata kwata tana Jin kunya Kuma a halin da yake ciki ta tambayi wani Abu Kawai sai ta dafa wake da shinkafa da Mai da yaji,ta shiga tayi wanka ta canja cikin doguwar rigar tsohon leshi tayi kyau gata kyakyawa komai yaji,tana Fitowa ta iske Nusaiba an Sha gayu cikin wani tsadajjen material tana latsa waya,Aslam ne ya fito sanye cikin kayan Shan iska Gajeren wando da Riga me gajeren hannu sky and white yayi kyau sai dai ya dan rame sabo da matsalar da yake ciki,Siyama tace Yaya Aslam na gama abinci amma wake da shinkafa na dafa da Mai da yaji,yace oh da kin fada min ba abubuwa na manta wasu abin sun Kare da an siyo ai Allah bai hanani kudin cefane ba ai ni na manta ke kuma baki tuna min ba,Charity tace bana so na takura maka ne ban San halin da kake ciki ba,thank you ya furta,Nusaiba ko kallon su Bata Yi ba tana Danna waya sai ma tabe baki da tayi,Siyama tace amma Ina ganin da kifi zaka fi iya ci,dubu Daya ta isa? ya tambaya tace ae ta karba,Nusaiba ta ja tsaki tana kunkuni Dan karya anzo gidanmu da motocin aro ana nuna kudi an kawo Ni tankamemen gida Ashe duk na aro ne daga yin aure cikin wata uku za ace komai ya Kare bank ya cinye kudi dama ba gaskiya bane duk kayan aro ne. Charity ta kalleta Kawai ta yafa mayafi ta fice ta siyo salat da tumatir da kudinya ta siyo kifi manya soyayyu ta dawo ta iske Nusaiba inda ta barta ta samu Aslam a dining Yana jira,a gurguje ta yanka salat da tumatir da cucumber ta wanke ta kawo Dining,tana zuwa Nusaiba ta taso ta zuba abinci tasa Mai da yaji ta barbada Maggi zata kwashi salat Charity ta rike hannunta tace kinyi kadan yarinya wannan ba kudinki bane sai ki bari sai na zuba Miki,Nusaiba tayi zuciya ta mike tace bazan ci ba na fasa cin abincin gaba daya,Wacce Nusaiba ta zuba Charity ta ja gabanta ta saka kifi da Salat sannan ta zubawa Aslam shima da kifi da Salat ya fara ci,Nusaiba Kuwa ta WhatsApp tace anjima Sufyan saurayinta yazo ya kaita zata ci Dinner a restaurant da rawar jiki yace an gama. Aslam Yana fita Sufyan yazo da Yamma likis Nusaiba ta dauki wanka har bakin gate ya dauke ta ya kaita hadadden wurin cin abinci,Suka ci Suka Sha harda ciko Mata Leda da snacks Suka dawo har bakin gate ya sauketa Suka Yi sallama,lokacin Aslam bai dawo ba a taxi ya fita Charity tana kallonta basu kula juna ba. Bayan kwana biyu Aslam Yana gudun Kar azo a musu wulakanci Nusaiba tana gyara kayanta yace Baby ki shirya gobe zamu tashi daga wannan gidan zamu koma gidan Dana Kama Mana haya,Wani Takaici ya kama Nusaiba,Aslam yace kaddara ce kiyi hakuri kinji,Kuka Nusaiba ta rushe Masa da shi tace ka cuceni da ka min karya na aureka,me yasa baka da Imani burinka ka jefani a wahala,Aslam yace kiyi hakuri,ranar kwana Nusaiba tayi tana kuka dama yanzu bata bashi hakkinsa ta daina tunda taji ba kudi ta daina yarda da shi Watarana sai yayi Kamar zai Mata kuka take yarda da kyar. Washe gari taxi ya Nemo Siyama ta fito da kayanta itama ta sa a Bayan mota,Dukkan kayan sawarsa da na Nusaiba mota guda aka Yi aka Kai gidan,kayan abinci da komai aka kwashe da abin bukata sauran duk a gidan aka bari,kayan kitchen na amfani duk ya tattara komai ankai,Nusaiba tana hawaye ta fito ta Shiga taxi ya zauna a gefenta Charity tana gaban mota,mota na tafiya Nusaiba tana hawaye tana cewa babu ac ne tana fifita da hannu,Siyama ta furta Aslam Wanda ya Saba da ac baiyi complain ba sai ke sama ta Kai da can kin San ac din ne, ki min Shuru munafuka cewar Nusaiba. Hanky Aslam ya mikawa Nusaiba ta dauka da bala'i ta jefar,wata unguwa Suka Isa wacce ta masu rufin asiri ce da talakawa a Kano,wani dan karamin gida ne Wanda na bulon siminti ne gidan hayane Wanda ke dauke da Palo da one room kacal sai toilet da kitchen shikenan gidajen haka suke a jere iri Daya sun Kai guda goma wani me kudi ya Gina yake zuba Yan haya,Yan makaranta ma sunfi yawa a wajen Sabo da irin kankantar gidajen,Nusaiba taki Fitowa daga taxi tana kuka sai da me Taxi ya daka Mata tsawa,dama an diga an kawo kayansu duka, Ciki Suka shiga kujeru ne a palon matsagaita amma masu kyau ne sai karamar plasma tv,dama duk tiles ne har dan tsakar gidan,bedroom din Kuma gado ne shima Kalar kujerun da labile Kalar komai kala Daya Kamar wani gidan Yar maryar talaka,kitchen Dan kut da shi,Yace ki daina kuka ki shirya kitchen,Nusaiba ko kulashi bata Yi ba Siyama ce ta shirya Kaya ta gyara komai har bedroom din ta shirya sannan ta dauki jakar kayanta tace Yaya Aslam na tafi sai na sake leko ku,Yace dan Allah ki dinga dan zagayowa, Inshaallah cewar Siyama,Ya bata dubu biyar da kyar ta karba Dan Kawai bata da ko sisi ne,a nan ta bar Nusaiba a zaune tana shirga kuka. AsmaBaffa [4/1, 5:47 AM] Sis Asma: 🛢️AUREN MU🛢️ 31-35 Official By AsmaBaffa Page naku ne BK MMN MUNIBA HAFSA ABDULLAHI Kallonta yayi tana ta kuka shima yayi shuru ya gaji yace kaddara ce ta afka min ba haka naso ba ki daina wannan kukan daga karshe ya tashi ya fita abinda Babu na ci ya siyo musu ya sake zubawa a kitchen amma Nusaiba ko kallonsa bata yi ba har azahar tayi lokacin yace kin San dai lokacin Sallah yayi ko,kanta ta dago idonta jajir ta watsa shi a saman fuskarta,tashi yayi tare da daura alawala ya fice ya barta nan tana zaune sai da aka idar da Sallah sannan ta iya tashi ta shiga bedroom din ta jefa hand bag dinta saman bed din ta shiga toilet tana Jan ajiyar zuciya kamar wacce aka nadawa duka. Siyama Kuwa tana komawa gida ta shiga da sallama Aunty tace ba dai an koroki
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71