Skip to content

Chapter 57

Chapter 57

AURENMU Book One Complete Hausa Novel 1,249 words 0 views Progress saved
Download Book

da bala'i Mum tace Wai wace ne ta damemu da Sallama taki ci taki cinyewa,Mama ta marairaice tare da langabar da kai tace surukata...ohhhhh da baki san ni surukarki bace sai yanzu dan Allah malama Fadi me ya kawoki sauri nake yi Ina da aikin yi,Mama tace zuwa nayi Dan Allah Surukata ki taimaka kisa danki ya maida Nusaiba dakinta dan Allah kuyi Hakuri komai ya wuce zamu gyara Inshaallah dan Allah ki taimaka Mana,Mum wani kallo ta Mata up an down sannan ba tare data furta komai ba ta tofar mata da yawu tuf ta juya tare da komawa ciki ta bar Mum a tsaye kikam,gajiya tayi da tsaiwa ta juya ta koma gida dabarunta sun Kare dama duk Shirin da tace shine kawai zata yi,Nusaiba ana gida zaman gida Wasa farin girki, bayan wasu Yan lokuta Shehu baya dagawa mama da Nusaiba kafa baya sakar musu fuska da Mama da Nusaiba wahala suke Sha sauran yaransa yake yiwa abinda suke so kawai,suna haka katsam sai ga Aslam,Shehu Yana gida yace a'a dana yau Kaine a gidan? Aslam yace ae Abba ya zauna kusa da Shehu a tabarma ya gaisar da shi ko kallon Mama da Nusaiba baiyi ba Wanda gasu nan a tsaye sun taho da sauri sun tsaya musu a kai suna magana kasa kasa da ita da Nusaiba,Shehu yace ashe haka arzikinka dama yana nan ya dawo naji labari Ina ta so ma nazo har gidanka Allah mun gode maka,Aslam yace Abba Kai na daban ne nasan me kaunata ne Kuma babban mutum ne Kai idan ba damuwa bana Inshaallah zamu tafi aikin Hajji tare da Kai,Shehu yace wayyo Allah dadi kashe ni Aslam ya dinga dariya,Nusaiba da Mama harda murna tunanunsu bikon Nusaiba zaiyi shi yasa ya Fara kashe musu kudi irin da,Aslam yace Kawu ba iya Makkah zaka tsaya ba Paris da Dubai zaka je inda Nusaiba take mafarkin zuwa yanzu gashi Shehu Babanta shi zai je Kuma Aslam Yana sani yayi hakan Sabo da farkon aurensu haka tace sai an kaita honey moon Paris ko Dubai,yace sannan duk Sanda kaji kana son hutawa Abba karka damu ka hada kayanka kazo gidana ka huta,ko me kake bukata Kawai ka kirani a waya,Shehu Kamar yayi suman dadi haka yake ji gani yake Kamar a mafarki,yace Kuma tare da abokinka zaku je Baban Siyama Kawu da Aunty,Shehu yace Alhmdllh na gode na gode ya dinga godiya Yana murna,Aslam yace Maganar shirye shiryen visa Zan kiraka a waya ya mike ya zaro Yan dubu dubu ya mikawa Shehu yace gashi kayi amfani da wannan,Mama ta dafe kirji,Nusaiba Hawaye ya Fara antayo Mata a kumatu,Mama tace surukina dan Allah kayi hakuri abinda Muka maka,Nusaiba tace dan Allah ka yafe min ka dawo muyi aure,Aslam yayi hanyar barin gidan ya juyo yayiwa Nusaiba da Mama kallon banza yace mugaye kawai yaja Tsaki ya juya shi da Shehu Suka fice,har mota Shehu ya rakashi ya tafi sannan ya dawo Yana taku dai dai Yana doro,Shehu yace Alhmdllh Yana takama a gidan ya zama Dan gayen dattijo aka bar Mama da Nusaiba da bakin ciki. Aisha tuni an maida Aurenta da Farooq suna zamansu lafiya yanzu duk Karya da fadan da sukeyi sun daina sai mutunta juna kowa baya so wani Abu yazo ya shiga tsakaninsu,soyayya suke me tsafta abinsu su,Nabeela kuwa tana yin Idda ta samu miji wani babban mutum ne me Mata ta hakura da Affan tasan babu aure a tsakaninsu ma tunda Dan Uwansa Yana raye amma ta take gaskiya yanzu Kam ta hakura ta auri me Mata Kuma tayi zamanta babu Neman rigima,Sabeer ma yayi aure ya auri zankadediyar matarsa Habiba. Raudah da Affan suna soyayyarsu sosai matsalar Raudah kishin tsiya,yau tana zaune a gida Affan ya fita sai ga Wayar Landlady ta shigo tana ta kiranta dagawa tayi tun kafin tayi magana Landlady tace Raudah maza maza fito ga mijinki Affan da wata sun shiga shopping zo ki gani da idonki,Raudah tace what? Na fada Miki maza basu da amana mijina haka ce ta rabamu da shi na aminta da shi Ashe maci amana ne,gani Ina ShopRite maza kizo kafin ya bar wajen, Landlady tayi gaskiya domin Affan ne da wata zasu shiga ciki ita Kawai dan ta ganshi da mace shine tace budurwarsa ce bata San cewar Amaryar liman bace ogan Affan Kuma Liman dinne yasa Affan ya kaita wajen wata Mata suna business tare da matar Liman,matar daga kasar waje tazo shine Affan ya kaita. Raudah hijab ta zurma ta fito da uban gudu tare da bude motarta ta shige ta Mata key motar taki tashi tayi tayi motar taki ta fito da sauri daga gidan sai ga yaron Affan da machine yazo gidan zai karbi takardu,da sauri tace dan Allah kaini ShopRite sauri,ya zaci ma wata masifa ce ta faru ya juya machine ta hau da sauri tana cewa kayi gudu Yi sauri Salahu dan Allah Yana tambaya lafiya Hajiya? Kayi sauri please duk ta gigita me machine suna ta fyalla gudu a titi tana kayi sauri ka Kara wuta Yana tsinka gudun gaske a rude yaje ya daki mota Suka watse a gefen kwalta Raudah ko motsi bata Yi kanta ya fashe daga gefe Yana jini,me machine din Kuwa Suma yayi Yana farfadowa yasan inda yake sai raunuka da yaji,mutane sun taru akansu aka kwashi Raudah da Salahu yaron Affan zuwa asibiti,lokacin Affan ma ya koma Office Kawai yaji Kira Yana dagawa ya mike Zumbur a gigice Yana tambaya a wanne asibitin ya tafi da sauri figi motarsa sai asibitin,matarsa Kawai yake cewa dakin da Raudah take aka kaishi Yana Shiga ya iske ta farfado amma ta karye baras a kafa sai kanta an nade daga gefen da bandage,tana ta kuka a kwance Affan bai ma tambayi me ta fito Yi ba Kawai ta lafiyarta yake Yi,ganin tana ta kuka ya Fara lallashinta,a gefenta ya zauna tare da maida kanta jikinsa Yana lallashinta tana hawaye yace Inshaallah Zaki warke kinji,anjima kadan za ayi aiki a dora min ke,ya Isa haka kukan Affan ko aiki sai mataimakinsa yayiwa magana ya kula da komai ya tafi jinyar matarsa sai ta warke zai dawo ya sanarwa liman gaba Daya family Suka Zo dubiya har Liman,a ranar aka dora Raudah ana ta zuwa dubiya har Yusuf da matarsa sunzo,shi kuwa yaron Affan tuni ma an sallame shi sai da Raudah ta kwashe sati biyu a asibiti Affan shike jinyarta shike Mata komai bai bari ma yan uwan Raudah sun zauna ba tunda suka zo dubiya,mamanta ce ma ta dage sai da tayi sati guda a asibitin sannan ta koma. Wheelchair aka bawa Rauda da sandunan koya tafiya lokacin da aka sallameta,Raudah tana tuna dalilin fitarta daga gida sai hawaye da kukan takaicin halinta tana nadama da Dana sani,gashi Affan din yand a yasan bata tambaye shi ba ta fito amma ko zancen bai Mata ba ta lafiyarta yake Yi ya daina zuwa aiki sai jinyarta shike Mata komai ita Kuwa me zata ce da wannan bawan Allah tayi dacen miji da wani ne sai dai a kaita gidansu in ta warke a dawo da ita, motar Affan ce ta shigo gidansa ya fito ya Bude dayan bangaren sannan ya bude booth ya dakko wheelchair ya dakko

Table of Contents

Chapters

71 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71