Chapter 65
Chapter 65
shirya ko yaushe zaki iya tarewa a dakinki,Mama tace yau Zan koma ai tsofaffin gidan Mata Suka ce ai Kya tsaya dai ki gyara jikinki,Suka hana Mama Sai lokacin suke bata abinci ishashe sabo da sunji taci gaba zata koma birni lokacin abinci sai ta ture,har kyautar Sabulai da su Omo suke bata Kuma ta daina taya su aiki amma abinci sai ta ture,kowacce sai ta bata kyautar magungunan Mata na gyara jiki,Mama sabo da an Mata kishiya ta dage da Sha tana ta gyara kanta bata aiki kaushin Hannu duk ya gudu babu tayi Yar kibarta da haske,sai da tayi gyaran sosai sannan ta shirya wasu dattijai su biyu Suka rakota gidan mijinta,Yaranta sai rungumeta da murna Kamar me,Su dai dattijai suna kawota Suka koma Kauye abinsu,Yaran Mama sun zagayeta suna ta murna yau sun rasa inda zasu saka kansu,Nusaiba ce ta kawo Mata abinci a plate da cokali harda siyo Mata lemo, Mama ta bude abincin ta ga shinkafa da Miya da nama harda salat,Mama yaushe rabo tace haka kuka ci gaba a rayuwa? Nusaiba tayi dariya tace Mama ai yanzu Abba abinda muke so muke dafawa,haka yake cewa mu zabi abinda muke so,Ameer yace kinga shagon Abba da kasuwancinsa ya bunkasa sosai, Mashaallah cewar Mama ta Fara antaya loma sai da taga bayan abincin nan tas,Nusaiba tace a Karo miki? tace na koshi Alhmdllh,duk da haka Nusaiba sai da ta tsamo Mata nama a tukunya kusan guda goma tace Mama cinye nasan yanzu kina yiwa mutum baki ko tsinuwa zata Kama mutum sabo da rashin cin nama akwai dafi me zafi yanzu a yawunki,Mama tayi dariya tace sai ku kuka da kanku amma ai kullum Albarka nake saka muku ko laifi kuka min naji haushi a bayan idon ku sai nace na yafe muku Allah ya muku albarka,Nusaiba tace badan Aslam ba shike nan Mama baza ki dawo ba,Mama tace ke dai bari Naga rayuwa yanzu fatana ki samu miji ko talaka ne, ameen cewar Nusaiba zanje Nima na nemi gafarar Aslam da Sufyan. Shehu dai a ranar ma Mama bata ganshi ba haka ta kwana ita kadai,washe gari da Yamma Nusaiba ta shirya ita da Ihsan kanwarta ta rakata Suka Fara zuwa gidan Sufyan sun ci sa'a Yana gida dake weekend ne,shima matarsa tana da ciki,matar bata San su waye ba ta sauke su cikin mutuntuwa Nusaiba sai kallon gidan takeyi komai an zuba sabo,Sufyan ne ya fito ya ga Nusaiba abinka da so,Sufyan gangariyar so yayiwa Nusaiba tsakani da Allah bai wani bata Fuska ba tunda yasan shima Yana da laifi tana da aure ya dinga soyayya da ita,gaisawa Suka yi tace zuwa nayi na baka hakuri ka yafe min abinda nayi maka,Yace oh ba damuwa na yafe Miki Nima ki yafe min munyi kuskure Allah ya yafe mana,tace na gode ta mike zasu tafi ya bata 5k taki karba sai Ihsan ya bawa ita Kuwa ta karbe Suka wuce gidan Aslam Tunda tazo bakin gate ta Fara hawaye ta tuna haukar da tayi da wannan gidanta ne ta cuci kanta,Ihsan tace Aunty kiyi hakuri haka kin Riga kin cuci kanki Siyama ta Shige gidan kunyi change kawa da kawa Kun auri miji daya haka Allah ya rubuta sai kin Fara Shiga gidan itama gashi tazo ta Shige ta fiki wayo da Imani Aurenku Aunty kawaye ko wacce ta dandani zumar Mijin Daya shike nan 50-50,Nusaiba tace yau na shiga Uku ubanki Ihsan wato har kinyi girman da Kika San mene zumar maza zanci Ubanki wallahi sai na fadawa Abba yaci ubanki wato Yar iska kike so ki dawo,Nima fa Aunty na Isa auren nan wlh 18yrs fa komai na hada wlh ina samun miji aure zanyi ni dai,gashi nan a novel nake Jin soyayya idan Muna karantawa a makaranta a Wayar wasu friends, writers da basa tsaftace alkalaminsu wani ka rantse Bf kake kallo,Nusaiba tace ai wasu na daya daga cikin Wanda suke gurbatawa Yara tarbiyya komai fada akeyi gatsal batsa tun farko har karshen novel yawanci ma yaran Mata sunfi manyan matan karatun novels,Allah ya shirya yasa su gane su gyara alkalaminsu wajen rubutu sabo da tarbiyyar yaranmu masu tasowa gaba,Ihsan tace to Aunty da dadi auren? Baki Nusaiba ta bude tace ke in kina da saurayi ki fito da shi gwara a Miki auren nan, Ihsan tace Ina da abina,dariya ta bawa Nusaiba suna rike da hannun juna tace waye? tace Mahmoud wani yayan kawata ne manager ne a bank baki ganshi ba Aunty ya hadu mugun sona yake kin San na fiki haske duk gidanmu nice ziza haka yake ce min Zizata,Nusaiba tace ba karya Ihsan na yarda to kice ya dinga zuwa zance,tace dama ce Masa nayi Kar yazo Abba zai dukeni,kice yazo kina yin candy sai a daura mu Sha biki,Murna Ihsan take yi writers sun ruda yarinya da soyayya. Suna compound na gidan Aslam sai ga motar Aslam ta shigo ya dawo, door bell Nusaiba ta danna amma Siyama tasa an hanata yin kara,knocking tayi Allah yasa tana kitchen ta fito tace Baby tare da bude kofa ai Kuwa Ihsan ta washe baki tace irin Yan Novels,dariya ta basu Siyama tace kune a gidan ku shigo suka shiga kamshi da sanyi Yana dukan su,Siyama tace yau an tuna da kawancen kenan? Nusaiba tace uhm zuwa nayi mijinki ya yafe min ko na samu hakkinsa ya daina bibiyata na samu mijin aure,Siyama tace Inshaallah ma ya yafe Miki Nusaiba,Duniya kenan Wai Nusaiba ce yau ke neman Yafiyar wani,bana son Iskanci tunda kin aure shi da shegen munafuncinki da kutungwila ai sai ki kyaleni,Dariya Siyama tayi tace kece Kika yiwa kanki fa Nusaiba babu laifina,Nusaiba tana dariya tace da laifinki Mana tunda kece kike kula da shi idan ba shishigi ba Ina ruwan Yar aiki da kula da mijin matar gida,to ita matar wa yace tayi wasarere da mijinta,Kinga mu ki kawo mana kayan dadi muci karki dame mu cewar Nusaiba,Siyama ta kawo musu abubuwan ci da sha sai lokacin Aslam ya turo kofa tare da shigowa,Siyama ta mike taje tana Masa oyoyo oyoyo harda Masa kirari ga hantsi leka gidajen kowa,me karya icen dawa sai giwa,hadarin sama zo da jido ko tsawa,angon Siyama Oga yazo, Kaine da gidan Kaine da dakin, bakaki me karya gada,ko su bi ko suki sai dai su bari, abi oga a zauna lafiya,Oga karya kafafun arna,aje gari ya jima sai kwarya,sunyi bakar tafiya ka kayar,Dan asali kuji babban suna,sai an Kai su tasha ko sunki,dariya yakeyi shi mamaki ma Aslam yake sai kace wata Yar tauri yanda ta iya kirari kamar me Waka kullum da Kalar da take Masa ba irin na baya ba Indai tana nishadi to zai Sha kirari sai dai ya tsaya Yana kallonta Kuma wani Dadi yake ji sai yaji Kansa yayi wani gingiringim, rungumeta yayi tana dariya itama hannunsa ta rike ta kaishi ya zauna ta kalli Nusaiba da Ihsan Wanda Suka zuba musu Ido suna Shan kallo Siyama tace ga Sadauki ku gaida shi,Sadauki Aslam shi Kuma an murtuke Fuska ba raini,Nusaiba tace Ina yini wani kallon banza ya Mata da kyar yace lfy,Ihsan Kuwa tana gaida shi ya amsa da fara'a yace ya school tace Alhmdllh,Siyama tace wannan ba karatu take ba na Santa har gidan kawarta
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71