Chapter 38
Chapter 38
tace Siyama gwanar addini a dinga sawa da mu,yau zafin da akeyi yafi na jiya bari na sake sheka ruwa a jikina,Siyama a ranta tace aha yau baza ku Shana ba sai dai ku kwana a haka, Aunty kam Kawu ta zubawa ruwa yayi wanka tare da tsarkake jikinsa Aunty ma tayi Suka dawo Suka kwanta aka bar Siyama bau a Palo har bacci ya kwasheta a nan. Washe gari Kuwa gani Suka Yi Siyama tana ta kwalimar dakinta ta Masa wani uban gyara na musamman ta kunna turaren wuta ta kulle ko Ina ya dauki kamshi, da Yamma tasan Kawu bazai bari ta fita ba abinda take so ta yiwa Aslam duk bazai siyu ba dole Wayar Aunty ta dauka a boye ta Kira kawar Aunty me yin snacks na gidan biki tana yi ma ana order,tace tayi Mata meet pie me dadin gaske da Samosa sannan ta siyo lemo juice babba ta hado da shi ta bawa yarta ta kawo mata,idan ta kawo sai ta bata kudin ta kawo Mata Suka Yi lissafi tace ana yin Sallar Isha take so a kawo matar tace to ba damuwa Siyama sai gaf da Sallar Isha ta fesa wanka ta saka doguwar rigarta ta larabawa wata maroon taji ado kawar Aunty ce ta bata da taje aikin Hajji bara rigar tana Mata kyau shi yasa take Adana ta,ta yafa mayafinta taje ta shafa humrar Aunty ta dan zubo wata a Yar karamar kwalaba,Aunty tace ke Kuma Ina Zaki je? Siyama tace to bana fita an hanani fita Kawai sai na bar kayana su rube bana sakawa,Kawu Yana jinsu ya tashi ya tafi Sallar Isha,Aunty ta shiga daki Sallah aka kawowa Siyama order dinta ta karba a boye ta biya kudin Yarinyar Yar budurwa Siyama ta kalla tace ungo kudin kice na gode sauri ki ta tafi bana so Aunty ta sani,Yarinyar ta tafi da sauri,Siyama ta Kai ledar daki ta kwaso plate biyu ta zuba meet pie din da Samosa a plate ta rufe ragowar ta boye a abinta ta ajiye lemo da cup kusa sannan ta fice,sai ga Aunty ta fito da Hijab tace zanje gidan kawata Jamila yarta ta haihu sai 10pm Zan dawo ki kula da gidan,Siyama tace to Kawu fa? Aunty tace baki ji yace yau gidan liman zai je ba abokin babanki ya gayyace shi walima an Haifa Masa yaro ai Kawunki yau sai an ganshi, tana murna dake gidan su Jamila ma ba nisa a layin ne tace Aunty a dawo lafiya tace yawwa ta fice,tana fita Siyama ta fito tayi sauri ta karbi wayar me shago ta shigar da number Aslam ta Kira,bugu daya ya daga ta matsa gefe tace ka taho kuwa? Yace gani a layin ma Sabeer ya saukeni zai dawo ya daukeni,tace kace ya dawo tara da Rabi,yanda tace haka aka yi,tana waya sai ganin Aslam tayi a kusa da ita Yana kallonta,me shagon ta mikawa wayarsa ta Masa godiya Suka jera Suka tafi,Yana faman kallonta yace yau kin Sha kyau haka ni aka yiwa kwalliyar,Murmushi tayi tace ae Suka Shige gidan har dakinta bata kulle kofa ba tasan ba kowa ta kawo Masa pie din da lemo,yace harda tanadi tayi dariya Yana ci yace yayi Dadi kuwa suna ta zuba hirar soyayya abinsu 9:30 Sabeer yazo suka tafi Siyama harda rakashi har cikin mota Suka gaisa da Sabeer ta koma gida ta cinye Su samosarta da lemon tayi Shirin bacci tayi kwanciyarta har Aunty ta dawo. Haka lokacin na tafiya Aslam duk Sanda yaga damar zuwa sai sun faki idon Aunty da Kawu suke samu su Shige su Sha Hira ya tafi basu taba Kama shi ba. Siyama ta gaji da halin Kawu tace wlh yau Zan Bari ya kamamu,ai Kuwa Aslam yazo yana dakinta dama da shi aka shirya plan din,bai taba kwanciya a katifar ba sai yau,Suka dinga hirarsu Kamar ba matsala ko an gansu da karfi yanda kowa na gidan Yana ji har dariyarsu ana ji,Kawu Yana tsakar gida daga shi sai dogon wando da Singlet,Aunty ta mike ta zauna tsoro taji ma ko aljanune a dakin Siyama suke Hira maganarsu ta fito fili,Kawu yace Siyama ke Siyama,Siyama Suka Yi kus Kamar ruwa ya dauke can tace naam ta fito har da nuna rashin gaskiya,Kawu ya mike ta koma dakin da gudu zata turo kofa Kawu ya Danna da karfi Siyama tana dannawa amma yafita karfi ya Bude ta karfi ya shiga ya Iske Aslam a kwance sanye cikin shadda Yar ubansu,Kuma ko a jikinsa ko tsoro bai ji ba tunda Yana sani,Kawu ya Fara salati harda rufe Ido ya fito gashi Yana Jin kunyar Aslam sosai bazai iya ci Masa mutunci ba,Aunty ma ta leka ta dawo baya tana salati tace kaga abinda nake fada maka ko da alama ba yau Suka Fara ba na dade Ina zargin Siyama dan Kuwa akwai Sanda takeyin kwalliya ta musamman da dare to gashi ka gani da idonka har cikin dakinta,Siyama ta fito tana kukan karya Dan Allah Kawu kayi hakuri dama Kaine ka hanashi zuwa shine nace ya dinga zuwa Muna buya Watarana ma Sai 2am yake barin gidan nan laifinka ne Kawu,Aunty tace yanzu kaga duk abinda zai faru ma ya faru,Aslam ne ya fito Kamar gidan Ubansa ko ajikinsa Yana takunsa,Siyama tace ai Kaine Kawu.....Mari ya zubawa Siyama sabo da Takaici,Aslam ya riketa da sauri,ta juya Masa Fuska tace tayani gani fuskata Kuwa tana nan,Aslam yace tana nan sosa min wajen,yasa Hannu ya Sosa Mata,Kawu yace Aslam Ina ganin mutuncinka ka sani Allah Yana ganinka,yata ce duk abinda ya sameta Kaine wlh,Aunty ta ja tsaki tace mene ma bai faru ba kana gani dai wlh ka Amince ayi sauri ayi bikin nan tun kafin masifa ta danno Mana gida,Kawu ya tsorata matuka tunda Aslam yake iya zuwa cikin gida har dakin budurwa su raba dare to komaima zai faru,Kawu cikin bacin rai yace Dan ubanki kinwa kanki Babu ke ba kayan daki cokali bazan siya Miki ba,Kai Kuma gobe gobe ka turo manya ka sani ficika bazan kashe ba Kuma babu taro auren bazawara ma Sai yafi naku armashi in Banda Yan daurin aure kar naga uban kowa a gidana,Kuma Babu me Kai maka Amarya ana daurawa kazo ka dauketa,Aslam yafi kowa murna a ransa yace mun Zama turawa Haka ake so ai,Siyama tace Wlh Kawu ba abinda mukayi Wanda ya sabawa Allah,Kawu yace ai tun daga Kebewa da kuka Yi daki Daya Kun sabawa Allah kuci gaba da istingifari Kawai mutanen banza sakarkaru Kai ka girma Namiji ka dinga biyewa mace,Aslam harda durkusawa yace dan Allah Kawu ku yafe Mana,Itama Siyama ta durkusa baza mu sake ba,,Kawu yace kanku kuka yiwa bazan siya Miki komai ba ko tukunya baza a Dora ba,Babu shagali ba gayyata,Aslam yace hakan ma yayi mun gode,karma ku gode ku tashi ku bani waje,Suka juya Suka fice Siyama ta diinga murna,Aslam yace Ni dama ban damu da wani taron Iska ba,Siyama tace shike nan ba anko ba gayyata ta furta da tausayi,Aslam yace nan da sati za a daura kin Zama amarya yau bazan Yi bacci ba, Siyama tace Ina waye ya bani bacci ai sai addua,Aslam yace yanzu an gama yakin karshe ki Fara bawa kawu hakuri lokacin bashi hakuri
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71