Skip to content

Chapter 9

Chapter 9

Zuciyar Masoyi Book One Complete Hausa Novels 1 1,175 words 0 views Progress saved
Download Book

kunna wayoyinsa wayar mami ce ta fara shigowa ya amsa da sauri a dayan bangaren mami tace kun fito meeting din ne? Abdullah yace yanzu muka fito tace zaka karaso da wuri ne domin ina da baki agida . Abdullah yayi kasa da murya cike da shagwaba yace zan taho da wuri zan tsaya na dan tura sako ta email ne Amman zuwa 5 ina gida yakatse wayar yana mai lumshe idanunshi yana matukar son maminsa ........ MMN SUDAIS CE [3/12, 3:01 PM] Kaunace Sila: 💗💗💗💗💗 ZUCIYAR MASOYI 💖💖💖 💗💗💗💗💗 AISHA A BAGUDO Page 4 Yayi sallama ya shiga falo mami wanka kawai yayi ya canza kaya yafito , a nutse ya zauna yana fuskantar maminsa sannan yayi fuska yaki gaida bakin da yagani duk yasanta , mami cike da kulawa tace baka gane mamanka hafsa ta sokoto bane . Abdullah ya waske sannan gaida ita mama hafsa tace ai ni tun yashigowarsa nake kallonsa gabadaya Abdullah ya canza min ,ya koma bature . Abdullah ya gyara zama hade da lallasa wayar dake hannushi yayin mami ke dariya gashi baije yagaida ke ba har kinzo . Mama hafsa tacigaba da nuna mamakin yadda Abdullah din yazama tace tsawon shekaru goma zuwa Sha daya fa dole ya sauya kana cikin turawa sun maida kai irinsu da wuya karinga gane yan,uwa mami tadan gunri kafarshi ta yadda mama hafsa bazata gani ba saboda bataji dadin yadda yayiwa mama hafsa ba dagowa yayi suka hada ido ta haaresa ,shi dariya ma tabashi, yayi murmushin gefen baki sannan yace kuyi hakuri mama wlh ba haka bane tun dawowata mukai maganar da mami ina son kwarai in zo aiki ne yarike min wuya Amman ina nan zuwa mami kam abun nasa mamaki yabata dan haka da ido take bin Abdullah da kallo ganin irin karyar dayake shararawa daga tace yayi magana Kuma sai ya bige da karya suna hada ido ya marairaice mata fuska .mama hafsa tace a to dan wannan wata rana sai ka hadu da yan'wanka baka San su ba. Mami ce ta kwallawa ramatu kira sannan tace wannan yar'uwarkace nasa baka santa ba Abdullah yamata kallon kasan ido tabbas itama Yar mama hafsa ce don ga kamannin nan rahma ta gaishe shi ya ams a ciki sannan ta tashi ta koma gurin su teema dan dukkan su saannin juna ne ,mikewa Abdullah yayi dan zaije ya duba wasu sakonnin a system din shi ,bayan ya fita mama hafsa ke sake yabawa da abdullah km yayi mata kyau matuka . Har kusan magariba yana gaban system sakonnin dai akan tafiyar da sukayi da dady ta south korea akan neman hadin gwiwa da suke so domin bude reshen company acan reshensu na Denmark shine tun safe yaga sakon ya shigo. sallah magariba da ishai ne yatashe shi a gurin , hakan kuwa yasa mu dady da batun nasarar da suka samu na yarda da kungiyar tayi da km interview din da zasu nemesu . Duk a wannan dare suka tautauna da dady kan batun don haka bai shiga part dinsa ba sai wajen goma saura na dare ,wanka yayi yasha tea ya kwanta yayi rigingine yana kallon sama , tabbas a dare yau yaso kwarai yaga Aisha Amman hakan bai zai yuwu ba ya rufe Ido tare da fadin Aisha.....ahankali , bai San sanda murmushin ya kufce masa ba sunan yadace da ita komai nata simple ,haka da ganin family dinsu baza suyi tashin hankali ba ,ya jawo filonsa ya rungume shi a kirjinsa yana tuna kallon tsoron da ta dinga yi masa a Daren jiya . A wannan lokacin kuwa mami da mama hafsa sun kulle a daki suna shawarar hada Abdullah da diyar mama hafsa faiza auren zumunci dake karatu a sokoto to a ganin mami ya dace kwarai Abdullah yayi aure yanzu musamman yadda harkokin ke yin gaba , komai Kuma Abdullah ne inyayi aure hakan zai kara masa kima sosai a idon mutane ,mami ta dada amincewa da shawarar mama hafsa don ko ba komai dai gara ita faiza ta gida ce ,don bata San wacce Abdullah zai kwaso ba Kuma yawan fitar da yake shima tana gudun kada yaje ya auro wata baturiya da ba kabilarsu ba don haka suka daidaita a atsakaninsu sosai , sannan a dan zuwan da mami take sokoto tana ganin faiza bazata bawa dan ta matsala ba ,duk ma wani abu da takeji zata dau nauyin nunawa yarinyar yadda zata kular mata da abdullah . a daidai wannan lokacin ita Kuma Aisha na can tun magariba ta shige daki ta kulle kanta tace bata jin dadi tai kwanciyarta don ma kada bakonta na jiya ya dawo yau ace sai ta fita ,kmr yadda yace zai dawo tanajin usman a kofar dakinta zaune kan Yar tsugunne inna yana cin tuwo yana sanya hirarsa da ita Amman bata kula shi ba ,yace zan danyi kokari in dinga kwaikwayon su inna wajen azumi Lada,yaya Umar dake wanke kayansa a bakin fanfo yace matsa can ka bawa mutane guri kai din da kullun safiya zaka tashi kmr ka kwana baka Ci ba shine zaka wani iya azumi na dole ma yaakayi aka cika ,. Usman yayi dariya yace "ai tashi ne yaya sai inji kmr an kai min farmaki cikin dare , Amman ina son yin tun yaushe nike fada ,su yaya Aisha bana jin an taba kwatanta fadar zaayi . Yusif yashigo ya Mika masa kudin maganin soro na duka gidan ya karfa ya wanke hannushi ya fita . Washegari da yamma ne Aisha na tsakar gida tana tankade garin tuwo usman ya aro dutsen guga kennan zai fara aka dauke wuta da Kyar ya hada na gawayi ya gama hurawa zai fara suka dawo da wutar NEPA , usman yace wlh baza ayi da wutar NEPA ba dana gawayi zanyi tunda ba dole bane yi dana NEPA. AISHA ko mai zatayi in ba dariya ba Abba dan makarantar su usman ya shigo usman wai kaje ana kiranka usman yace injiwa Abba yace wasu ne a waje su biyu Maza usman yatashi yafita jimawa kadan ya dawo wannan Karon a natse yake magana Amman acikin Yar murya yace yaya Aisha baki kikayi a waje ina ga balaraben nan ne da yazo shekaranjiya da daddare . Aisha kallonsa kawai take duk da bata nuna komai ba a fuskarta ba Amman sai ta tsinci kanta da faduwar gaba cigaba tayi da abunda take zuciyarta na dukawa da sauri da sauri usman yashiga gyada kai dan Allah yaya Aisha kije wallahi suna da kwarjini da kima bazan iya komawa ince ba zaki zo ba . Bata kulasa ba haka bata bar abunda takeyi ba , saboda a ranta bata da niyar zuwa Amman tarasa meyasa zuciyarta ke harbawa , usman yace innarmu zan gayawa zata saki kifita yanzu ,ta ja tsaki har ya nufa dakin inna kome ya tuna sai Kuma ya fasa ya juya ya sake kallonta ya girgiza kai ya fita .yayin da tabishi da kallo ,har ya dawo ya cigaba da gugarsa bai sake ce mata uffan ba . Gabannin magariba wasu guraran ma an soma kiran sallah yaya Ali ya idar da alwala ya fita , Aisha na kicin dinsu tana sauri ta kwashe abinci itama

Table of Contents

Chapters

62 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62