Chapter 31
Chapter 31
Abdullah kullun cikin maganarsa take.. matsalar dai can gurin yarinyar da iyayenta da akaje aka ciwa mutunci .... a fili dady ya kira sunnansa yace Abdullahi... kana son yarinyar nan Aisha har yanzu? "A firgice Abdullah ya dago da sauri yana kallon dady hade da mummunar faduwar gaba, ZUCIYAR sa ce tashiga dokawa da sauri da sauri yadan jigina da gadon da yake zaune akai yayin da har yanzu hannushi na cikin na mahaifinsa ,yasake kallon dady da kyau yana son karanto wani abu yadda yaga idonsa bbu wata zolaya ko wasa a cikinsu kuma kusan koda yaushe a hakan yake ,ya kau da kai gefe ya fara inda indar magana yace da..dy mami bata son.....that is not the answer to my question I said do you still love her ....cikin tsanyin jiki Abdullah yace ina...ina sonta sai dai ma...hannu dady ya daga masa ya isa shikenan abinda nike son ji daga gareka yacigaba da yi masa wata maganar a hankali yake sake nazarinsa.. Tun yinin biyu nan da sukayi da dady sai ya kasance kullun cikin zirga zirga dady yake a nan cikin Germany sai dare zai kasance tare Abdullah wanda har Abdullah din yadinga mamaki ,kwanan Dady takwas tare dashi a daren da zai baro shi ya kara nuna masa barcin ransa Sosai akan wayan tunanin dayake yawanyi ,da bakinsa Abdullah yayi wa dady alkwarin ba zai sake ba domin yasan barcin ran dadyn nasa ,a hakan ya baro shi da cewar next week zai dawo... Ta zubawa takardunta na makaranta da aka karbo mata idanu tana Jin daya daga cikin abunda ke sanyata farinciki kennan a Yan kwanakin nan, Amman kuma tun a jiya da safe da yaya umar ya shigo yana yiwa inna bayanin zuwan mahaifin Abdullah abin ya tsaya mata a rai dan tasan dai koma meye magana ce a kanta ..inna kasa zaune tayi kmr tayi tsuntsuwa taganta alhj ishaq taji tana son taga danuwanta har gashi bakin basu tadda mlm abu a gida ba kasancewar da wuri suka zo gashi duk an tura koina bayanan dan haka dady yabar sakon a yau zasu dawo shi yasa ta natsu a daki haka nan Kuma shima mlm abu yau tun safe yana gida sannan Kuma tun safen ya tura yusif yaje ka'oje yazo da mlm dahiru to har yanzu sai dai bbu yusif din bbu baki daga bangaren Abdullah duk inna tabi tadamu dan tana son sake ganin danuwanta ita dai banda mlm da kuma tana da cikakken karfin iko akan Aisha zata so ayi ..... MMN SUDAIS CE [3/12, 3:01 PM] Kaunace Sila: 💗💗💗💗💗 ZUCIYAR MASOYI 💖💖💖 💗💗💗💗💗 AISHA A BAGUDO Page 20 Sannan kuma naji kace kana bukatar auren cikin sauri nan kusa nidai ina ganin idan har ba wata matsalar a dan dagamin kafa zuwa nan da sati hudu nan gaba. Dady ya sake Yi musu bayani dalla dalla akan yadda likitan Abdullah yace alhaji aminu ya numfasa yace a satin nan kennan a yadda kuke so dady ya girgiza kai Amman yake dan nakalci wani abu kadan game dasu "wanda da kamar ya manta Amman nan da nan yayi saurin cewa basa bukatar komai game da kayan daki yarinyar kawai suke bukata" mlm abu yace matsalar dai kennan tun farko ta hargitsa abu idan har ya kasance kowa yayi hakuri abin yawuce to a gaskiya ni dai sadaki kadai da yazama dole shi kadai nike bukata daga yaro ya fada yana duban mlm dahiru.... sannan batun daurin aure abarshi nan da sati biyu alhaji Mansur abokin dady kusan duk wata dawainiyar nan da shi akayi ,wanda tun zuwansa sau biyu kawai yayi magana sai yanzu ya shiga juya kai yace yaya za'ace za'ayi haka mu da aka taimakawa aka bawa yaron mu ai mu yakamata muyu komai . Mlm abu yace sadaki ma dan shine aure in ba haka bbu abunda zan amsa a auren AISHA dady kuwa shiru yayi mutane nan sukara cika masa Ido irin mutane da suka zabi su tsira da mutuncinsu ne ba su tsira da dukiya ba ,a fili yace to haka ma mun gode kwarai Amman maganar gurin da za"ayi taron daurin auren fa? Daman shi alhj aminu tun ba yau ba yake da burin matukar Aisha bata zo gidansa amatsayin surika ba to shine madaurin aurenta domin Allah ne yahada su da mlm abu Amman silar haihuwar ta hakan kuma ya taba gayawa mlm abu ,sai dai maganar hadata da yasir yabarwa ransa "dan haka yayi saurin cewa ai in Allah ya kai muna numfashi nike da waliccin yarinya dan haka a can gidana za'a daura aurenta ..Dady yayi dan tunani sannan ya girgiza kai bbu komai mu dai muna sake godiya a yadda aka tsayar da maganar daga ranar jumma'a kennan za'a yi daurin auren ...cikin Raha sosai wanda dady yakara kima a idanunsu har mlm abu ya yarda da maganar matarsa ,tabbas alhj ishaq mutumin kirkine sai dai kawai bai Yi sa'ar macen kwarai ba" to mlm dahiru dai yayi shiru yana nazarin mlm abu ganin bashi da niyyar sanar da dady kusancin sa da mai dakinsa shiyasa ya gyara zamansa hade da gyaran murya yace yana fuskanci dady da kyau yace sannan kuma akwai magana mai mahimmanci dana zan sanar "gabadaya falon ya dauki shiru suka maida hankali su gunsa inban mlm abu da yasan me mlm dahiru yake son fadi dan shi gabadaya yama manta da wani zance can " nan dai mlm dahiru yasanarwa dady da komai har zuwa inda yace masa maimuna dai kanwar itace matar mlm abu ya nuna mlm abu da yatsansa kuma uwa ga yarinyar da Abdullah naka yake so "nan take jikin dady ya dauki rawa banda zufa bbu abunda ke tsatsafowa masa gabadaya jiyayi kmr ba haka yaji mlm dahiru ya ce ba "yasake duban inda mlm dahiru ke zaune da kyau "yace in kana mamaki ne ko tantama tashi mushiga ciki kaganewa idanunka ...jiki a tsanyaye dady ya Mike tsaye yana jin yadda zufa ke sake karyo masa , jikinsa yayi sanyi matuka bai taba kawowa ransa hakan ba duk da yaga da mlm dahiru acikin lamarin" ya dai dauki hakan da wani dangantarka ce tadaban ta hadasu da mlm abu, a tsaye yake kawai Amman gabadaya yazamo mutun mutumi yayin da mlm abu yayi gaba sannan mlm dahiru sai dady dake biye da bayan su sannan sauran har suka shiga cikin gidan bai san ta yadda kafafunsa suka iso ciki ba ,da idanuwa yake bin koina da kallo yana karewa gidan kallo tsaf yana alwadai da kansa da masu hali irin nashi yanzu acikkn wannan dan a kurkin yar'uwarsa take rayuwa mlm abu ya leka dakinta yakirawo sanye take cikin hijab kmr tasan zasu shigo tafito cikin tsanyi jiki dan kusan ma ita Aisha ta dauko wajen tsanyi ,ta gaishe su, shi ko dady kasa dauke kansa yayi daga gareta ya dai amsa mata gaisuwarta, maganar mlm dahiru ce ta tabbata tabbas itace dai a gabansa , yanzu yasan yayi babban kuskure a rayuwarsa kuma yasan ya aikata laifi Mafi girma". da kyar dady ya iya bude baki yakira sunanta mai..mu..na !ta amsa da na'am yaya ya bayan rabuwarmu ya girgiza kai kawai yana nasawa aransa yanzu baizo neman Yar uwarsa
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62