Skip to content

Chapter 8

Chapter 8

Zuciyar Masoyi Book One Complete Hausa Novels 1 1,185 words 0 views Progress saved
Download Book

. Lokacin da suka Kare primary suka ci makaranta daban daban dole A aminu yanemi canji inda aka maida sakina tasu Aisha domin ita Aisha ta kwana taci federal gwandu yayin da sakina tace army day tare aka musu komai da komai da kansa yakai su makaranta boarding ,yana matukar yabawa da hankali Aisha ko kadan bbu wauta a tare da yarinyar tana da natsuwa tun bata kai haka ba ko tsalle tsalle yara suke ita kuwa tana zaune a gefe abunta tayi shr tana kallonsu ,ita zuciya ba me mata dole banda haka yayi matukar yiwa dansa yasir shaawarta wanda shima satin da yagabata ya tafi karatu indiya sai dai yabar abun aransa kawai . Rayuwar boarding ta kara haifafa shakuwarsu komai tare suke Yi , abu daya ne kawai sakina tafi Aisha A bahindi shiga mutane domin ita Aisha idan bata ga dama ba zata iya wuni a daki bata fita koina ba tana karatu sai dai sallah ko cin abinci ya tadda ita ,cikin yarda Allah a cikin shekaru uku a makarantar kwana Aisha ta dauki jarabawar science sai gashi hutun da suka dawo zasu shiga aji hudu jarabawar tafito Allah yabata sa'a taci makarantar yanmmata ta science dake wannan lokacin sakina Aminu har da kuka tayi mata akan ta hakura kada ma ta fada a gida to itama Aisha batason rabuwarsu inda suka iske principal da matsalarsu suna so ita Aisha tayi zamanta anan basu Sha wuya ba aka amince musu Aisha ta zauna a science class yayin da ita sakina take art class . Suna aji biyar mmansu sakina taje akin haji dan haka har suka dawo hutu suka koma basu hadu ba, sai byn da suka dawo hutun daga shi sai aji shida suka risketa dayake tunda suka fara makarantar idan sun dawo sai anfara sauke Aisha daga bisani a wuce da sakina gida" ya sanya sai byn kwana biyu da dawowarsu Aisha ta shirya taje yiwa mama sannu da zuwa,sakina ta taro ta da murna kmr ba a satin suka rabu ba ,suka isa falon mama suka tadda ta, ganin Aisha sai da ya tsorata mama , yarinyar ta koma sai kace wata aljanna don tsabar kyau duk yadda tayi zaton Aisha ta wuce hakan ga wani shegen less a ajikinta ya dace da ita sosai km ya zauna ajikinta tamkar dan ita akayi shi,tabbas shine less din da sakina ta nuna mata A aminu yayi musu da sallah babba lokacin da batanan mama takasa cinye fushinta da kishinta har ya fito Fili ,wanda tunda ta amsa gaisuwar farko ta hade girar sama da ta kasa tayi murtuk ganin haka ya sanya Aisha fita ta koma dakin Aunty amarya aiko mama kmr an zugata Aisha na daga falon aunty amarya Amman tana jiyo balbalin fadan mama ,kin bari wacan kinibibiyar yarinyar tagama kanannade miki kurwa jikinki har bari yake idan tazo ni bansan yadda kukeyi a makarantar ba duk da alhj aminu ne ya cuceni da ya hadomin ke da ita, na rasa yadda zanyi dan wannan idan kika samu saurayi tsab zata kwace shi,ko aure kikayi taje inda kike sai ta kwace miki miji da wannan idon nata irin na Mashya . Sakina ko sai juya hannu take tana rokon ta dan Allah tayi hakuri tayi shiru kada Aisha taji karshe mama korota tayi daga falon ita tashi tayi tashige dakin, tabarta nan idan kan yarinyar nan ce gayar kauye masu gadon tsiya to tabbas zanci ci mutunciki ,. Ta dafe kai hawaye na zubo mata taji antabata daga baya tana juyowa taga Aisha ga mamakinta murmushin Aisha take tare da girgizamata kai tasa hannu tana share mata hawayen tare da fadin ni zan wuce . Cikin sauri sakina tace to ai.... To kibari a kaiki . Tace Aa barshi da kai nazo ai sakina tace bari nazo narakaki ta dafa kafadarta na gode sister ki zauna ki huta ta fice da sauri ba yadda bata yi ba dan gano bacin ranta Amman takasa gano komai dan Aisha bata nuna bacin ranta har Suka koma makaranta duk yadda sakina tayi kokari tausasa mata akan abunda ya faru sam Aisha ta nuna mata batason maganar Amman agun Aisha bata taba haduwa da abunda yamata ciwo irin kalaman maman sakina gareta ba ,ta dai bar abun a ranta domin abin yafi karfinta bata da yadda zatayi . Sunshiga shekarar karshe a makaranta Aisha ta kwatarmusu school dinsu a wani debit daakayi na English sosai ta kware da amfani da manya kalmomin turanci kmr ma baa school din tafara gogewa dashi ba,haka nan sun buga quez akan scientific abinda bata zataba sai gashi ita tasake karbar school dinsu . Sakina ce tazo ta sami A bahindi a wani dare tace sister zoki ga wata drama taja ta har wani hostel abinda ke faruwa wasu yaran GSS 3 zuwa ss1sukayi group a yadda suka samu cikinsu suka zauna mutun biyu daga cikinsu suka tashi kowace tana gwada tafiyar A bahindi ana ihu daga can Kuma wata Yar aji hudu da duk tafi su zakewa ta Mike ita har da dressing din A bahindi na riga da siket sune ajikinta hakanan Kuma colour da A bahindi tafi so ta fito tana gwada tafiyar A bahindi har da maganar ta idan takeyi kmr zatayi kuka duk sai da yarinyar nan tayi duka gurin akasa ihu ana kidi da botikan robo , Aisha ko ta zubawa sarautar Allah ido can yarinyar ta buga kafa tace da kawayenta nice da komai irin na A bahindi kusan daman ni ina maseefar sonta momy . Ragowar suka ihu sakina ce tasa tafi tare da cire hijab din da tasa very good ta taso ta nufi inda suke kafin ta karasa kuwa sai fliin gurin tuni suka tarwatse domin basusan shuka sukayi akan idon makwafta ba. Malamin physic dinsu yanuna yana matukar son Aisha Amman tunda ta fuskance sa ta dauke masa wuta haka malamai da dama suna nuna suna son ta Amman ita sam basa gabanta . Sun gama karatun su cikin sa'a, da yawa kawayensu an Sha kuka domin wadansu shikenan , ranar da suka gama last paper ko hostel basu koma ba akazo aka dauke su suka tafi. Watanni kennan dagama school din Aisha yayin da kaninta usman ke aji biyar a secondary ,su yaya yusif na da shekara ta hudu ajamia sabida matsala kudi yasa karatunsa yabata lokacin , ,yayin da ya'ya Umar keda shekara 2 da shiga ita dai aunty Maryam tun bayan gama secondary tayi aure tacigaba da karatu a school of nursing yanzu haka aiki takeyi shi Kuma Ali army school yake son zuwa . A bahindi babba barinta bai wuce tacigaba karatu a jami'a kmr yadda sakina ma ta kwallafa rai akan karatu mlm abu yacewa Aisha sai abunda A aminu ya yanke akai inzaiyuwo suci gaba to idan Kuma bai amince ba shi kennan . Wannan shine cikakken tarihin mlm abu . Yau kmr jiya tun shabiyu yashiga meeting da sauran maaikata sai karfe biyu ya fito duk da sanyi AC dake dakin meeting din hakan bai hanashi jin zafi ba ya fito zuwa nashi office din yayin da salis ke biye da shi da Yar saman court dinsa byn ya shiga ne ya

Table of Contents

Chapters

62 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62