Chapter 20
Chapter 20
shida saura suka shigo birnni kebbi taso ace sai dare suka shigo , Amman ko sanda suka sauka daga mota Ido CA akansu musamman ita da Abdullah daman Kuma abunda bata so kennan gashi biye yake da ita jakar ta ma tana hannushi nan da nan tarinkajin tamkar ta nutse dan kunya yanayin ta ya sauya jikinta har rawa yake hatta Dr sagir sai da ya lura da yanayin da tashiga har kofar gida suka rakata suka Yi sallama da Dr sagir , Abdullah ya Mika mata jakarta ta juya zata karba ya lura hatta idanunta sun cika da kwalla ya rike jakar yana kallonta ya kira sunanta cikin sanyi murya Aisha..... are you alright .....?ta daga masa kai are you sure tasake daga masa kai sannan a hankali ya Miko mata jakarta tare da fadin I will come back letter ,ta amsa ta juya ta shige gida ya tsaya yana binta da kallo bbu halin yabita ya rarrasheta ya karaso inda Dr sagir yake yana ganinsa ya fashe masa da dariya yace kai friend be a man duk kabi ka susuce akan karamar yarinya "tension ne kawai ta samu na rashin sabo na gane irinsu duk kabi kawani rude Abdullah yayi murmushin karfin hali dan shi kadai yasan halin da ya tsinci kansa lokacin da suke tare Dr sagir ya bugi kafadarsa yace my friend a dage da addu'a .dan yarinyar taci ayi komai a kanta Abdullah ya mika masa hannu suka tafa yace thank you doctor ... kamar yadda ya fada washegari karfe hudu da rabi suna Tare daga cikin soron gidansu ,simintin ciki a share yake tas Abdullah na zaune kan kujera har sanda tafito bai ji isowarta ba ,sai da ta taba kujera zata zauna sannan ya dago ya dubeta kallo daya tamasa tagane yau cikin serious dinsa yake sosai duba da yanayin fuskarsa ,byn ta gaisheshi ya zuba mata idanunshi yana kokarin sanya kwayar Idanunshi cikin nata kallo daya tamasa ta dauke kanta ya kira sunanta yace Aisha tun jiya byn rabuwarmu zuwa yau sau nawa kika tuna ni ?taji tambayar wani iri ta juyo ta kalleshi murmushi ya sakar mata yace ko sau daya ko na amsa miki ,ita ma dan murmushi tayi" yayi shiru na wani cikin lokacin tamkar mai nazarin ta inda zai fara yayi dan gyaran murya ya sake Kiran sunanta yace magana nike son muyi please ina son ki bani hadin kai, tai shiru batace komai ba ya zubawa yatsun kafafunta dana hannunta Ido yakanyi mamakin yadda suke kmr nashi yayi jin yana sake nazarinta sannan yace please Aisha ina son ki amince min inzo neman aurenki a gurin baba ina bukatar ki kinzama matata ta aure Kuma uwar ya'yana , maganar tashige ta ta dago Ido tana kallonsa shi dinma ita ya zubawa Ido sun jima a haka yayin da take kallon Abdullah wato yana son yazama wani sirri na rayuwarta kennan ,ita da kanta bata taba zama ta tuna wata rayuwar aure da sirrin dake ciki ta ba,sai ayanzu da Abdullah ya haskota da hakan shiyasa take masa kallon wanda zai iya sanni sirrinta kamar wacce ta farka daga mafarki da sauri ta dauke idanunta daga gareshi ,yayin da shi kuma kallon da ta dinga masa ya sake rudashi yanemi yafi haiyacinsa idanunta tamkar wanda ta fara bacci ta farka take masa kallon tsoro da maganar da yayi mata har sanda ta dauke Ido Amman shi ita yake kallo har yanzu yanajin yadda kaunarta ke sake tsumashi "shr bbu wanda yasake cewa komai ,ya kamo lip's dinshi na saka yana cizawa ahankali ya hade rai gudun Karta kawo masa wasa cikin lamarin ,yace nasan komai yana bukatar nazari ko na barki zuwa gobe sai in dawo naji abinda kika yanke . kawai taji kalmar gobe ya fitowa daga bakinta yace Eh mana gobe Sunday shine Nike da time sosai da har zan fahimci maganar da zamuyi in ba haka ba sai zuwa rana irin ta yau Amman me kika gani ta sake kallonsa batare da tace komai ba yace banason nayi miki gaggawa idan kince indawo zuwa next week ne sai na bari ,ta daga masa kai cikin sanyi jiki yace to shikenan yana sake karewa mata kallo . Anyi hakan asabar lahadi litinin aka kai aunty Maryam asibiti tun safe suke can gabanin magrib ta haifi diyarta mace washegarin talata aka sallemesu Inna bata dawo gida ba sai ranar laraba ita Kuma Aisha aranar larabar tashirya kayanta ta tafi gidan da yamma Abdullah yataso aiki tanan gida ya biyo yaga sanyin idanunshi Amman bai sameta ba sai usman ne yayi masa bayanin inda take a ranar duk yadda yaso ganinta hakan bai samu ba dan dama idan yashiga gida mami bata wani amincewa da fitar dare idan dai ba Dr sagir ne yazo suka fita ba,. Amman washegari da wuri yabar office ya sameta can gidan aunty Maryam yadda Abdullah keji tamkar ya dauke ya gudu da ita yace Aisha ko nema na ba'ayi Kuma kinsa hanyoyin da zaki bi ki ganni ko kiji murya ta tadan saci kallonsa ta sunkuyar da kai tana tuna ranar da ta dawo daga ka'oje cikin jakarta ta tsinci complement card din shi guda uku aciki , address dinsa numbers dinsa da matsayinsa na aiki a jiki a tsakiyar wani littafinta ta zuba su bata kuma bi takansu ba yayi murmushinsa mai sake fidda tsantsar kyaun da Allah ya masa"meyasa magana take baki wahala ne ,ina aunty Maryam tana ciki baki daukomin bbyn taki nagani ba ta dauka da wasa yake sai da sake tabbatar mata Sannan ta Mike ta shige, zuwa jimawa ta dawo dauke da bby a hannunta ta Mika masa ya karba yana kallonta yace ina son bby mace Aisha tana birgeni da dadin wasa tajima a hannushi daga baya tasoma motse Aisha ta karbeta ta mayar da ita ta dawo da juice da snack da aunty tayi masa tun zuwansa ya zame daga kan kujera yace kai nagode wa aunty kamar tasan inajin yunwa. Aisha tamasa wani irin kallo kmr mai jin tausayisa ,yana kallonta ta sunkuyar da kai ya gane kallon da ta masa kawai yayi murmushin gefen baki anan sukayi sallah magariba har salis yace tama aunty Maryam barka zaizo gobe in Allah yaso ta amsa ta shige yabita da kallo, a kasan ransa ya furta har yanzu bata fara damuwa dani ba . Washegari bai zo da wuri ba sai gab da magrib bai dade ba yayi niyyar tafiya sai da zata tafi ne yace idan tashiga ta turo a dauki kaya a bawa bby aunty da nata Aisha tasanar da aunty salis ne yatarasu a falo kasancewa falon baban saifu ya bulla waje saboda baki . Kayan sun kusan tsoro ta aunty domin dai duk wadatar Abdullah akace an Yi masa haihuwa a gidansa idan yayi wannan sayayyar sai anjin jina masa balle ita daya kawowa Aisha bata bi takan kayan ba tayi alwala ta shigewarta daki ,ba bby ba hatta mai jego tasamu rabonta a ciki jakar kayan Aisha kuwa tana fara dubawa ta rufe tana kwalla mata kira tace wannan yarinyar idan baki auri wannan mutumin ba mun banu sai Allah yakamamu ta fito da wata sarka Aisha ta gane ta
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62