Chapter 14
Chapter 14
tasan da zamanki ya bude idonsa a hankali yaga hoton zanenta wanda yayi shi da hannusa ya kafawa hoton ido shi kam kusan komai ya nema gurin Allah yana samu , Amman yarasa me zaiyi wa Aisha ta soshi ,duk wata dabararsa na neman karewa a wannan bangaren ,a fili yace mami nasan Idan kika ga Aisha zaki so ta sosai nasan duk abunda nike so kema zaki so shi .to cikin satin daya gabadaya wanda shine mami ke sa ran tafiyar Abdullah sokoto kamar yadda suka yi da mama hafsa sai gashi tafiyar tasamu Abdullah zuwa kasar Dubai domin nemo wasu sinadari da kamafaninsu ke bukata ,su biyu sukayi tafiyar shi da RK ,sai salis kwanansu hudu suka juyo tun ranar juma a ,sai talata don haka shima satin cikin aiki yake dole bbu maganar tafiya sokoto .duka karfe goma na safiyar juma'a cikin kamfanin nasu dike yake da maaikata kowa ya maida hankali akan aikinsa yayin da ba a fi mintina goma da shigowar MD Abdullah ba, yayin da Secretary dinshi yashigo ya gaisheshi sannan ajiye files akan makeken table din dake gaban Abdullah yadan rankwafa sannan ya juya ya fita ,salis yashigo da coffee cikin karamin cup ya ajiye a gabansa ya fita yadda yake neet haka komai na office din yake haka Kuma yake gudanar da aikin nasa ,bai fi mintina talatin da fara bincike files din dake kan table din wayar sa da ke ajiye agefe ta hau sauti mai ratsa jiki Abdullah ya dago ido yana duban system din wanda zanen hoton Aisha ne a bayyane ya furta ahankali Aisha kennan wasu na shekaru talatin da tara zuwa casain wasu sun gama shekarunsu sun tafi ke sai yau kikai 18 ya fada tare da kashe komai ahankali ya Mike zuwa kofar shigowa ,ta tsakanin glass din da ya ratsa kofa yake hange mutane dake bukatar ganinsa har sun Karu akan sanda ya iso hakan yasa yaji bai iya tsallalakewa yabarsu ya dubi agogon dake manne da hannushi goma da talatin da biyar uhummmmmm yaja numfashi Aisha wata abace mai mahimmanci a gareshi don haka akwai bukatar yaje yaganta koda na minti ashirin ne ya matsa intercom secretary yashigo , Abdullah yace zanyi off zuwa na da wani lokaci yana son komai yacigaba sannan adakatar da masu San ganinsa haka duk wanda yasake zuwa yayi hakuri sai zuwa Monday wanda suka riga suka zo sudan Jira shi,sannan yace yaturo masa salis , secretary yace Ok sir ,ya juya ya fita bai jima ba sai ga salis yashigo. Yasanar dashi bukatarsa nason fita Amman dole sai ta kofar baya domin masu jiransa bazasuji dadi ba idan suka ga fitarsa, kofar baya salis ya bude suka fita salis ya kwaso wasu ledoji guda biyu yabiyo dashi yana mai jinjinawa Abdullah da irin wannan halin nasa nason kyautatawa mutane da sauri musa yataso yayi da Abdullah ya daga masa hannu yace ya zauna zasu je da salis yanzu zasu dawo musa ya girgiza kai hade da hanzarin bude musu murfin mota suka shiga sai suka biya yakara mata siyyaya har dasu greeting cards "kai tsaye gidan su Aisha suka wuce basufi minti uku da tsayawa a kofar gidan mlm abu ba wata yarinya da bata fi shekaru bakwai ba zuwa takwas ta fito daga gidan cikin sauri abdulla ya kirawo ya tambaye sunanta tace hadiza yace yauwa hadiza Maza jeki ki gayawa inna Abdullah ne yazo yana son ganin Aisha yarinya tace ai inna bata nan tun jiya Abdullah yadan ciza leban sa , sannan yace usman fa. Hadiza tace duka suma basa nan usman yaje makaranta ba kowa agidan sai yaya Aisha Abdullah yadanyi shiru sannan yace salis ajiye kayan yaje mota ya jirashi , salis yayi yadda yace tun bai wuce ba yaji yana cewa yarinya ta dinga daukar kayan da daya da daya tana shiga da su , sannan idan tashiga ta turo Aisha yarinya ta kwashi Leda biyu da karfinta tashiga dasu ta ajiye cikin zumudi ko Aisha batayiwa magana ba tadawo ta kwashi ragowar ta shige ,sai byn ta tara kayan guri guda take gayawa Aisha taje inji Abdullah . AISHA dake kusa da famfo tana wanke wanke ta dalla mata harara tace shine ya hanaki kisiyomin Omo dana aikeki . hadiza tace A'a sannan cikin sanyi jiki ta Kuma fita ,aiko sai gashi tasake dawowa wai yace dan Allah kije yanzu zaki dawo Aisha ta kalleta tace kice masa aiki nake Kuma ke nake jira da omon fa . hadiza ta fice haka ta gayawa Abdullah sannan ita Kuma tashige dan gaba da su ta siyo Omo tana yi tana waigensa Abdullah ya dafe kai game da duba agogonsa yana mai sauke hadiyar zuciya ,kai tsaye zuciyarsa ta raya masa ya shiga da kansa dan haka ya shige soron farko yashiga na biyu shima a gyare yake kmr na farko yana karasawa tsakar gidan zai shiga dan haka yadan tsaya daf da ciki ya leka Aisha ce zaune abunta hankalinta kwance akan kujera tana wanke kwanuka a gaban famfo ta gama sauran tukane har yashigo bata sani ba Kuma bata ji motsen komai ba shi Kuma bbu akan abunda idanunshi ya sauka a cikin gidan sai kan damuwarsa bbu ruwansa da wani yanayin na cikin gidan shi sam bai lura da komai ba sai Aisharsa ,tayi masa kyau sosai bai taba ganinta a daidai irin wannan lokacin ba, dan hasken ranar da ya haskata yasake fito mata da sirrin kyan da take da shi. kananan kayan dake jikinta ya dada taimakawa wajen fito masa da kyawunta da bai tabaSani tana dashi ba , hakan yasa tasake daukar hankali matuka, bai taba tsammani ta iya dressing irin haka ba" ya zuba mata idanunshi da sukarigada suka gama rikecewa ko kiftasu bayason Yi, yakarasa sannu ahankali yadan tsugunna daidai inda take zaune motsen tsugunawarsa ne yasanya ta dago a tsorace sukayi 4 eyes dashi ido cikin ido suke kallon juna sai ayau ya kara tantance sexy eyes dinta kullun idanunta a lumshe kmr maijin bacci. yayin da Aisha numfashi ya tsaya cak na wani lokaci kafin daga baya yasoma circulating zuciyarta ke dokawa da sauri da sauri sai da ta saita kanta da kyau sannan ta iya bude baki tayi magana tace manene haka abun naka yawuce waje har cikin gidan iyayena. Abdullah yayi murmushin nan nasa mai mai daukar hankali har dimple point dinsa ya fito yace today is 14 that's your birthday Aisha ta fiddo idanu waje tana zaresu dan tsoro Anya Abdullah ba aljanini bane " ji wani sabon balai har ranar haihuwar ta yasani ta fada akasan ranta wanda a fili ta sake daure fuska sosai tace kayi kuskure idan kana tunanin zan taba fahimtar ne ,ok kasamu labarin bakowa shine kashigo domin kasamu abunda kadade kake so, to kayi babban kuskure domin ni din bairin ka bace kaje can ka nemi irinka ba ni Aisha ba Abdullah ko kallonta kawai yake ,tace tun farko daman nagane nufin ka shiyasa bazan taba amincewa da kai ba kaje kanemi irin wayan da zaka yaudara in yaso daga baya sai ka gudu kabarsu ,kan Abdullah ya daure yaji maganar kmr ba daga bakinta take fitowa ba tace Abdullah kabar mana gida kadama
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62