Skip to content

Chapter 33

Chapter 33

Zuciyar Masoyi Book One Complete Hausa Novels 1 1,196 words 0 views Progress saved
Download Book

sukayi sallama dady dakan sa sai da yaji gabansa fadi ZUCIYAR sa ta masa nauyi jin sunan mlm dahiru shine matsayin kawun mahaifiyar yarinyar da Abdullah ke so" yayi shr ya fada duniyar tunani mai zurfi da bai san tsawon lokacin da dauka zaune ba..... tabbas inda yadda Abdullah yasanar dashi mlm dahiru shima ai kawunsa ne sai kuma wani tunani na daban yazo masa.. Washegari wajen karfe uku sai ga yusif da mlm dahiru tare da su dady gabadayan su " dady kam asubanci sukawa garin ka'oje dan a can dady ya wuni duk yinin yau mlm abu bai yi mamakin yadda hakan takasance ba nan da nan Mlm ya turawa alhj aminu, shi kam mlm dahiru tun daga ganin zuwan dady al'amura suka karye daga gareshi, byn kowa ya hallara hade gaishe gaishe sannan suka fara abunda ya tarasu da farko dai dady ne yasoma magana hakuri yabayar sosai game da cin fuskar da akazo har gida akayi musu batare da nasaniyyarsa ba ,yace sai kuma dana ka'oje yau din naga kawuna shima yana daya daga cikin wakillan yarinyar duk da bansa yadda kuke dashi ba Amman hakan yamin dadi matukar da gaske , mlm abu ya numfasa sannan yace ai bbu komai haihuwace ta janyo haka sai dai maganar aure ne dai bbu shi a tsakaninmu domin ina son na tsirar da mutuncina dana diyata ko bakada komai yazama ka tsirar da mutuncinka dady yayi shiru yana sauraron sa Amman abun mamaki sam dady bai ji haushin kalaman mlm abu ba dan bai san iya yawan rashin mutunci dazo aka musu ba , dan ko shine zai iya yin fiyye da haka a yadda yakejin su teema aransa, mlm dahiru shiru yana kallon Mlm abu rashin kyatawa bai ma duba girmanshi ba to maye amfanin turo yusif dayayi Killa yayi haka ne dan ya tozartashi kuma da dukkanin alamu bai san kowaye alhj ishaq ba, da dangantakar dake tsakaninsa da matarsa yana son yayi magana Amman maganar taki zuwa masa shi kusan duk wunin yau da mamakin ya wuni wai Abdullah dan ishaq ne kuma shi ke neman Aisha da aure uhmmmm ikon Allah kennan alhj aminu ma yasa baki Amman sam mlm abu yace shidai abar masa diyarsa bawai dan baya sonta da Abdullah bane tunda dai mahaifiyar yaro ta nuna bata so gara a hakura gabadaya kar azo ayi abunda daga baya za'a yi danasanin , Aisha ita kennan gareni Diya mace idan wani abu yasame ta bazai iya yafewa kansa ba ,alhj aminu yayi shiru shi hakan ma dade ne a gunsa dan yafi son Aishar tazamo rabon dansa ce yasir ,, falon ya dauki shiru na wani lokaci yayinda kowane su da abunda yake kissamawa ransa " dady ne yayi godiya tare da mimika musu hannu sukayi musabaha sannan ya Mike yace zai koma Amman zai sake dawo..tare suka tafi da mlm dahiru yabada izinin amai dashi ....shi suka wuce tare da securities dinsa... koda mlm abu yashiga gida a daki ya tadda innarsu taci kuka har tagaji tsaye yayi kikam daga inda yake da sauri ta dago Ido tana bin mlm da kallo shima kallonta yake yana sansanin dalilin kukan nata yadda tamasa shiru shima haka yayi ya karasa inda kayansa suke ya canza zuwa wasu daban yace mata shi yafita sai yanzu tasamu karfin iya bude baki tace mlm...yadan ja ya tsaya tace har sun tafi ne?...da kai ya amsa mata kusan yasan mezata tambaya gaba shiyasa yayi saurin ce mata bari na dawo zammiki bayanin komai Amman kibar kukan nan haka .....tanan zaune har bayan sallar la'asar takasa tashi tajin kmr wani abu na shrin samun danuwanta sanadin hana Abdullah Aisha ko shi Abdullah din ,. , Jin shiru inna yayi bata fito ba Kuma alhalin tasan yau ba litinin ba ko alhamis saboda idan inna tana azumi bata fiyesan zaman daki ba. yasa Aisha shiga dakin da sallamarta ,zaune ta taddda inna tajingina bayanta da gadon dakin ta hade hannuwa waje daya idanunta na kallon celling dakin ta dade tana kallon innarta kafin daga baya takarasa kusa da ita ta zauna tana karewa innarta kallo kusan duk kwanakin ta lura kmr bata cikin kwanciyar hankali hakan yasa danganta hakan da maganar aurenta ne yasa inna shiga wannan hali, ta dade zaune Amman duk inna batasan da shigowar ta ba, ta bude baki cikin tsanyi. muryarta tace innarmu........jin amon muryarta yasa inna yin frigigib. tadawo haiyacinta da sauri tasa gefen zaninta taso goge siraren hawayen dake diga ta gefen idonta , Aisha ta girgiza kai tasa hannuta ta kamo na innna cikin nata kusan second biyar suka dauka a haka Aisha na kallon innarta da san sanin abunda kesata kuka sannan shine karo na biyu da taga zubar hawayen innarta runtse ido tayi cikin sheshekar kuka tace innarmu dan girman Allah ki daina sawa ranki damuwa akan zance auren nan nifa dama can ba wai ina son auren Abdullah bane balle ki damu kanki kuma da hakan ta faru ma nafi kowa Jin dadi rabuwarmu Amman kiyi hakuri nasan sanadina akazo har gida aka cimuku mutunci keda baba sai kuma ta fashe da matsanancin kuka mai rekitarwa ......itama inna hawayen take har yanzu ta dammke hannun diyarta da kyau tana jin tautsayinta komai nata bata cika damuwa dashi ba balle ya daga mata hankali, tace sam ba shine yake sani kuka ba kuka na daban, to innarmu me ke damunki tun kwanakin baya nike ganin cikin wannan hali dan Allah kisanar dani kinji.. ...ta marairaice fuska. inna tayi shiru tana nazarin diyarta ta tasa hannu daya tana share mata hawayen fuskarta tace kibar kuka tacigaba da goge mata hawaye, ta sauke ajiyir zuciya ta zubawa inna idanunta tajin kaunar mahaifiyarta na ratsa mata kowani gaba ta gangar jikinta ita fa banda soyayyar uwa da uba da yanwanta bata San wata aba soyayya ba.... inna ta numfasa har yanzu ita Aisha take kallo tanasan tasan damuwarta, ita da kanta zata so ta sanar daita dan bata da sama da ita ita rayuwar ta dan bata da kowa duk duniyar nan sai tarin yan'uwa inna ta kira sunanta Aisha..... sai kuma tayi shiru....nawani lokacin sannan tace ki kwantar da hankali bbu abunda ke damuna "in ma akwai kece mutun ta farko da zansanarwa duk duniya wa gareni byn ke banda yaya ko kanwa macce dazan kaiwa kukana dan'uwa daya gareni shi kuma yamin Nisa" dan haka tamkar banda kowa haka nikejin kaina" sai ku da Allah yabani dan haka bana son naganki cikin damuwa dan ke Yar dangi ce ga da tarin yan'uwa kuma masu tsananin sonki takarashe maganar ta tana dariya har taso bawa Aisha itama ko tadan murmusa tace yauwa diyata ko kefa maza tashi ki daura mana sanwa yamma tanayi ,a tare suka Mike suka fita Aisha tayi kicin dayake ita tarigada tayi sallar la'asar yayinda inna ta zari buta tayi make wayi...... Da dare byn sallar ishai kafin mlm abu ya fita waje, inda yake zama domin shan iska suna tare da inna a daki duk dai inna mlm abu take sauraro danji wani abu daga gareshi dangane da zuwan yayanta Amman yamata gum da baki har sai da taga yana niyyar sake fita sannan tace mlm kamin

Table of Contents

Chapters

62 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62