Chapter 30
Chapter 30
idanuwansa sunkada sunyi jawur yace mami ta wuce ko.....? yadda ya fadan yasa minal taji tausayinsa yakamata ,yayi murmushin karfin hali dan wani dokawa zuciyarsa keyi a hankali yace minal a wasu lokunta sai ki ga abubuwa suna faruwa irin haka Allah yana kaddarawa bawansa wani abu yasame shi domin gwada imaninsa ,ciki muryar tausayi yace mami tayi fushi dani saboda ina son Aisha ,ta tafi tabarni bata San cewa nayi shr ne ina bawa zuciyata hakuri Aka rashin Aisha dazanyi ,zan auri duk wacce mami ke so batare da tawa soyayyar ba... Abdullah ya runtse idanunshi ya daga kansa sama hannushi daya ya daura tsaitin ZUCIYARSA kwallar dake idon minal ce ta karasa zubowa tasa bayan hannunta ta goge tana kallon danuwanta cikin halin tashi hankali bata da halin taimaka masa ...... MMN SUDAIS CE [3/12, 3:01 PM] Kaunace Sila: 💗💗💗💗💗 ZUCIYAR MASOYI 💖💖💖 💗💗💗💗💗 AISHA A BAGUDO Page 18 Ran dady yayi matukar bacci sosai game da bayanin da mami keyi masa ,shi duk bai san abinda ya faru ba Amman shi duk ba wannan ya Dame shi ba, lafiyar dan nasa ,kansa a caji yake ga rashin lafiyar Abdullah ga zirga zirga ta sha'anini kafa company dinsu da suka samu nasara a Denmark ga rashin Abdullah da gurbinsa daya bari domin wani abun dole sai Abdullah hakan bai hana dady tsallalakewa ya dubo lafiyar Abdullah din nasa ba bayan kwana biyu da dawowar mami... A sa'a dady ya sauka a Germany domin a ranar ake warwarewa Abdullah bandejin karayar dake kafadar Abdullah din hakan ne yasa dady ya sawa ransa Abdullah yana samun cigaba a lafiyarsa har ma yaji dadi sosai da yadda ake kula da shi dan haka kwanansa uku ya juyo tare da minal bayan ya kara sakin kudi sosai akan maaikatan asibiti akan lura da Abdullah ,dama dai bbu wani mai jiyya dake zama dan Abdullah kadai sai securities guda biyu RK da salis... Washegarin da dady yadawo daga Germany mama hafsa ta iso ita da faiza tare da shiryayen shirinsu duk akan Abdullah a rashin sa'a suka tarar Abdullah din ma na can gadon asibiti a wata uwa duniya .. To duk yadda mami tayi da dady akan tana san sake komawa dubo Abdullah dady yaki , Mama hafsa kawai ya sanyawa hannu akan taje duboshi , Amman faiza ta zauna ,faiza kuwa a yadda tazo a shiryenta taci alwashi bata kara komawa sokoto sai tare da auren Abdullah a kanta ,dan haka ko ba dade tana nan tana jiran warkewar Abdullah da dawowar sa.... Tun bayan gaisawa da Abdullah yayi wa mama hafsa bai sake tanka mata ba tun zuwanta ,komai tace sai dai yayi shiru koda maganar ta na bukatar amsa , saboda a ganin shi kamar yadda yaji daga bakin mami ita mama hafsa tana daya daga cikin wadan da suka haifar da rikicen dake kwalkwalwarsa ,dan haka tana barin gurin yabada umarnin bai san sake ganin wani yashigo dakin da yake idan kacire maaikatan sai dai ko daga cikin mahaifansa .... Bbu yadda mama hafsa batayi na san ganinsa Amman fur aka hanata ance yana bukatar hutu ta ciza yatsa na ba adadi. daganin wautarta tun farkon xuwanta saboda a yadda taga Abdullah laga laga a kwance shi yasa take son ta fara aiwatar da shirinsu , kmr yadda sukayi da faiza , Amman sai gashi daga gani daya tun bata fara aiwatar da komai ba ,an datse sake ganin Abdullah din ta buga ta buga Amman sam aka hanata ganin Abdullah" haka ta hakura domin visa dinta ya cika na dawowa dole ta taho batare da tayi komai ba daga cikin abunda taje da niyyar Yi..... Watan Abdullah biyu da kwanaki dady yasake biyo jirgi ya ganshi yadda yaga Abdullah yayi matukar razanashi ya tsorata tamkar ba'a asibiti yake ba , Abdullah ya rame sosai ta yadda har kwayar Idanunshi sun nuna haka , sannan ga wata muguwar kasunba daya tara ,dan ya hana a gyara masa tamkar ba Abdullah din dayasani ba mai matukar son tsafta da kyamkyami... Aranar dady ya gana da babban likitan dake kula da lafiyar Abdullah a office din doctor jack suke a zaune dady ke tambayar yadda yaga jikin Abdullah yakasance doctor jack kwararen likita ne da ya nakalci cututtuka da dama ,yayi gyaran murya yace shi duk wata cuta da Abdullah yazo da ita iya bincikensu ya samu saukinta koma ya warke musamman daakayi saa Abdullah din bai da kyan jiki to abinda yake damunsa a yanxun kirjinsa Amman akwai magunguna a yanxun daake son Yi masa amfani da su. Sai dai Abdullah ya hana zuciyarsa sakat da yawan tunane tunane,wanda iya bincikenmu Abdullah yana tattare da damuwa aransa wanda sakamakon yawan damuwar da zuciyarsa take har yasa ZUCIYAR ke barazanar kamuwa da wani ciwon na daban .,kirjin dady ya buga da karfi doctor jack yacigaba munyi kokarin ganin ya'ajiye duk wani damuwa saboda ganin yadda lafiyar sa take yin kasa ni kaina na zauna dashi ya kai sai hudu Amman har yanzu bbu wani canji ,shi yasa muka dakatar da shan maganinsa mai karfi dan gudun faruwar wani abu. doctor ya numfasa yace Amman yanzu abinda naga za'afarayi wanda zai ceto shi daga hakan a binciki abunda ke damunsa a kawar masa da damuwarsa dake damun zuciyarsa , Allah sarki dady kasa ko motse kasayi yayi akan kujera yace to doctor kmr yaya kake ganin za',ayi ciki harshe turancin duka suke magana doctor yace abunda yafi a bincika idan wani abu yake bukata ayi masa idan Kuma damuwa ce yake tare da ita a kawar masa da ita yin haka kadai zaisa yacigaba da karfan magani na karasa samun lafiyar sa ,domin duk kan masu yi masa hidima na bincike su bayani guda daya ne , kawai yake cewa abinda ya dame shi, ko yake bukata wanda Kuma bbu naganin sa asibiti .. Hankali dady a tashe yabaro office din doctor Abdullah ciwon zuciya INA..... yana ta nanata hakan a ransa to a dare sai da Abdullah yadawo tsaf da shi komai yayi neet a jikinsa , dady yana kallonsa yana cin abinci yana sake nazari akansa yana Jin tautsayi dansa har washegari suna manne tare duk wani zirga zirga ta sha'anini aiki bai kai mahimmanci zama da Abdullah ba a wajen dady ,Abdullah yasamu natsuwa kadan yaji dadin zuwan dady ,wanda har da kansa dady ya fahimci hakan ba kamar farkon da yasame shi ba ahankali dady ke bincikawa me ya sawa ransa har da yake son jefa shi cikin wani hali,ka tausayawa dadynka kasanar dani damuwarka bakada sama dani duk duniyar nan nima haka na jure abubuwan da dayawa game da rayuwa Amman bazan iya jurar rashinka atare dani ba ya kamo hannushi cikin nasa yana masa duban ina sauraronka Abdullah dai yasan dady yana da fahimta abu yana da Kuma saurin ganewa dan haka baiyi shakkan komai ba yadda yagayawa maminsa haka ya gayawa dady har zuwa jenyewar da yayi na auren Aisha dan ba yadda ya iya ....da kuma fushin da mami tayi dashi ... Dady ya zubawa dan nasa Ido sosai yake kallonsa ya damu da fushin da mahaifiyarsa tayi dashi , Amman bai sani ba itama mami tana can hankalinta da ranta suna kan
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62