Chapter 43
Chapter 43
rigaka kwana dole ya rigaka tashi, dady yayi shr yana kallonsa yana sake nazarin tilon "dan nasa da sauri Abdullah ya canza hirar bakin da zasu tafi a yau. dady yace eh zuwa karfe Shabiyu motoci zasu zo wasu zasu fara yin gaba .. Har zuwa tara suna tare da Abdullah ya Mike yace zai je ya sake dubu maminsa ko ta tashi dady ya kirawo sunansa ya juyo yace idan kaga maminta ka ,sai ka koma gida ku shirya karfe biyu zuwa uku zaku wuce Abuja in yaso sai ku tashi tacan zuwa Germany Abdullah ya bude Ido yana kallon dady duk da yasan da komawarsa Germany ,Amman bai dauka da wuri haka ba. yayi sororo yana sake kallon dady yasan magana daya dady yakeyi dan haka ya amsa kawai ya fita ,sai da dady ya tabbatar Abdullah yabar gurin mahaifiyarsa sannan ya matsa intercom ta kiran mami.. mami tayi sallama tashigo fuskarta ba wani yabo ba fallasa ta nemi kujera ta zauna tare da gaisuwa tsawon lokacin dady bai Yi magana ba balle ta ran zai amsa gaisuwarta dady yayi tamkar bbu wani a tare dashi "daga can ya numfasa yace Abdullah zai koma gadon asibiti kmr yadda kika likita yace , Amman ki sani abu ne mawuyaci ya samu lafiyarsa" ko yatashi ko Kuma akasin haka .... A dan frigice mami ta dago tana kallon dady yayi kmr bai gane yadda tayi ba ya kau da kai gefe fuskarsa a hade yacigaba Amman ina son idan kin koma daki kiyi sallah rakaa biyu ki godewa Allah da ya baki "da "mai biyayya me hakuri me gudun bacin ranki ne"me damuwa da damuwarki ,wanda a wannan zamanin nasan tabbas irin su Abdullah basu da yawa "ya sauke ajiye zuciya saannan yacigaba Kuma ki godewa Allah Abdullah da ne kuma ya cika dan halak "Abdullah ya nemi da yayi auren Sunna Amma ke kinki yarje masa saboda wani dalili naki na banza mara tushe, bansani ba kodan Aisha daya aure ne kesani tun Gini tun zane kinyi kokarin rabani da yaruwata wacce ita daya gareni yayinda ke kike tare da naki family din" sai dai me Allah ya nuna miki ke bakowa bace shiyasa ya jarabi tilon danki mafisoyuwa a zuciyarki da son diyar yaruwata batare da sanin shi ba ,to ALHAMDULILLAH duk randa da Abdullah ya haihu da yarinyar nan tabbas ya tabbata jinina shi " Kuma bbu me kiran "dan"da "dan "titi. wanda a wannan zamanin ba wai wani abu bane agun namiji baligi musamman wanda yashiga matsalar aure irin haka .. Jikin mami yayi sanyi.d dady ya numfasa tsoro bakya son aurensa da Aisha yasa shima yace ya hakura ya zabi farincikinki ,akan nasa kisani yadda muke da hakki akan sa shima haka yake da haki akanmu, haka ne ma yasa na tsaya tsayin daka naganin nabashi farinciki sa da lafiyarsa akan ko ma me zai faru ya faru" abin takaici da damuwa duk gur biyu ya kamata atoshe masa .ga dai Abdullah ya auri yarinyar da yake so . wanda burin rayuwar sa kennan sai gashi rashin hadin kanki yasa damuwar dai har yau bata barshi ba bbu koma bbu komai Allah yaraya min shi idan Kuma sanadiyyar hakan wani abu ya faru dashi har narasa shi , shikenan sai kiji dadi ki samu wanda zaki aurawa wacce kike so, ya fadi hakan yana girgiza kai ya sake cewa bbu komai kmr zaiyi kuka dattijon ya koma kalar tausayi .. mami tasan ya kai karshe kennan tunda ya nuna haka ,tasan sa tasan halinsa, tsawon sama da shekara talatin da suka fara rayuwa tare. zuciyarta fal tsoron yadda yayi mata magana. ta kalleshi bai sake cewa komai Ba kuma tasan a yadda suke ko zasu Kuma kwana a haka ba zai sake mata magana ba" a yadda taga yanayinsa ta jima anan zaune daga baya ahankali ta Mike jikinta yayi mugun tsanyi kafarta kmr bazata dauketa ba ..koda ta koma part dinta ma tunanin duk ya hanata sakat ko dazu daya shigo ta lura yanayin sa. ya kara ramewa akan sanda ya dawo daga jinya maganar dady akan hanya take "yadda Abdullah ke ratsawa kasashen duniya yana ganin yan'mata iri iri na turawa ai da tuni labarin yasha bam bam bama zai bukaci yin auren ba. ita daman ta dan soma sadudu biris din da tayi dai shine ya Dame yaron. Kuma gashi yawan damuwa ita zata haifar masa da ciwon zuciya amatsayinsa na wanda bai gama samun lafiya ba. ta furta kalma na shiga uku ,haka kawai ina neman kashe dana da kaina ... Mu dai tafi hankali shin da gaske mami ta saduda kmr yadda tace ko kuwa dai tayi likimo ne "amsar ku naga Yar mutan bagudo ku dai biyoni a sannu ahankali dan kusha labari mai tsansar abin tausayiπππππ MMN SUDAIS CE [3/12, 3:01 PM] Kaunace Sila: πππππ ZUCIYAR MASOYI πππ πππππ AISHA A BAGUDO Page 28 Karfe daya da rabi daidai byn dady yayi sallah ana masallaci cikin gidan. biyu daidai kuwa a gidan Abdullah tayi masa Abdullah ya shigo dakin ita kadai yasamu domin aunty ta wuce tun dazun. Tayi kyau tayi gayunta kmr yadda yadda ya Gani. ahankali ya matso kusa daita ,yana murmushin ya sanar daita zuwan dadynsa ,a frigice take binshi da wani kallo cikin marairaicewar fuska tace me nayi Kuma . har taso bashi dariya Amman ya dake baiyi dariyar ba" yace bawani abu bane ina ganin dai kan tafiyar ne, ba dai kince bazaki bini ba sai muje kusanar dashi da bakinki "dan kar ya dauka ko daga gareni ne yasake hade rai ,ta sauke ajiye zuciya ahankali yayin da tacigaba da kallon Abdullah, baya ya juya yasoma barin dakin yace yana falo . Tabishi da Ido kawai ita dai da Abdullah ya tsaya sun sulhunta kansu zata bishi ba sai ya hada da dady ba" dan ita tsoro take ji ,batasan abune yafi karfin Abdullah din ba shi yasa ya sanar da dadynsa.. Tayi sallama ta isa falon ta nade jikinta da abayar har da dan kwali tamkar wata balarabiya cikin natsuwa ta nemi can gefe ahankali ta zauna ta takure jikinta waje daya . Dady yana waya sanda tashigo sai da yagama ya ajiye wayar sannan ya kalleta ta sunkuyar da kanta, kwarjinin dady ya cika falon ahankali ta gaishe shi ya amsa yace Aisha kennan yasake maimaitawa ahankali yace taso zonan ki zauna yanuna mata kan carfet dake gefe kusa dashi" sai da ya Kuma maimaita hakan sannan ta taso a dan tsorace wanda har kallon da Abdullah ke binta dashi kasa kasa yasa ta kusan faduwa a diririce ta zauna . Inda dady ya nuna mata. tare da sake sunkuyar da kanta sosai " poor Aisha dady ya fada akasan aran shi duk yadda ya dauketa ba haka ya ganta ba, dukkanta bata fi girman aminarsa ba ,ya kara jin tausayinta yashiga ransa matukar,a fili yace Aisha kun kwana lfy a gidan ko ?ta daga masa kai yayi murmushi madallah bayan dan shr yayi na wani lokaci sannan dady yace da gaske wai kince bazakibi mijinki ba "taji kmr kasa ta bude ta nutse ciki ta kara sunkuyar da kanta har ya gane tsananin nauyin data ji" yayi murmushi .
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62