Chapter 41
Chapter 41
suka dariya Amman baza kaji ainihin abunda da suke cewa ba... Daga gun daurin auren kai tsaye reception aka wuce kmr yadda dady ya tsara . Usman yashigo gidan gwaggo Laure ta tambaye shi har andaura . Usman yacire hularsa ya ajiye yace wlh an daura kwarara igiyoyi guda uku . yashiga gaya musu yadda yaji sadakin to a haka ma unguwar ta dauka wasu ke cewa sun haifi arzikinsu yayin da wasu ke kallon arziki ajinin yarinyar yake hakan ce ta faru can gidan alhaji aminu inda aka mamansu sakina tayi shr abin yayi mugun tsuma zuciyarta" to daman haka abin Allah yake idan Allah yaso ka to kowa ma yakika ba wani abu bane .. Yadda ake ta ririta zance a unguwa ,su kuwa gidan mlm abu jikinsu ne yayi matukar yin sanyi ita kuwa amarya uwar tafiyar takara tsorace wa da al'amarin angon nata ... Misalin karfe daya ranar ne Dr sagir ya turo musu da motoci kmr yadda aunty Maryam tasa aka kira shi tayi masa korafin har yanzu baa san gidan amarya ba "gashi ana son kai kaya shima Kuma sai da ya kutsa cikin jama'a yasamu dady akan maganar shine yanzu aka turo musu.. Shi kan shi Abdullah bashida masaniyar ba a nan cikin gidan zai tare da amaryasa ba", sai a wannan lokacin wani shiryayen gida dady yasa aka tsara musu wanda duka bai fi part din Abdullah da rabinshi ba bbu wani nisa me yawa tsakanin su da gidan .zuwa karfe uku sai ga su aunty Maryam sun dawo dama dai daga ita sai aunty amarya sai kawar aunty Maryam din sai ko usman don wani abun sai da namiji gwaggo Laure kecewa Kar dai har kun gama jeran ... Aunty Maryam tace bari dai gwaggo ai haka muka dinga yawo da kayan mu a cikin gidan dan ko ina muka bude a shirye yake da komai a cikinsa daki daya muka samu acan karshe da bbu komai a ciki muka zuba su sai dai gidan ya hadu ya wuce tunanin mu abin duniya tamkar aba san ciwon sa ba. Ahankali ta motso ta shafa kan Aisha dake kwance awa ruwa ta shafawa diyarta dake hannun kawarta tace Allah ya yiwa yayanmu haka . wannan yanayi yasa mlm abu yasa aka sauke alqurani mai girma fata na gari kennan Allah ya zaunar da maaurata lafiya. Karfe takwas daidai Dr sagir yasake turo motocin dazaakai amarya,nasiha mai matukar ratsa jiki mlm abu yayi wa tilon diyarta sa wanda har ya hawaye ballewa a idanunta "babu yadda zatayi da auren Abdullah ,ita inda son ranta ne tun da dai auren ake son suyi to sun yi. Amman a kyaleta tayi zamanta agida ko boarding da take jin takaicin duk sanda zata koma sai taji nafila ne akan akai ta gidan Abdullah "a hankali mlm abu ke tambyarta abinda za'ayi mata da sadakinta ta dago jajayen idanunta tana kallonsa irin kallon nima ban sani ba tana langwabar da kai daga ganinta kasan tagama saduda da al'amarin. hawayen dake zube a idonta shi ya dada karyar masa da zuciyarsa yace kukan ya isa shi kennan . Inna ma tayi iyayinta sosai duniya nan kusan ita tafi kowa sanin halin diyarta dan haka itama takara yi mata nasiha har batasan innarta ta damu da ita sosai haka ba sai yanzu yadda tarinkajin tana maimaita cewa kiyi hakuri da komai duk ma wanda zai miki wani abu da ba daidai ba ki kalla kawai ",sai dai abunda kikaga zai wuce iyaka, sai a yanzu Aisha tayi magana me yuwa ma tun safe dataji a yadda aka daura aurenta bace ko uffan ba ,ta kalli inna murya a raunane tace innarmu to maman Abdullah fa?anan inna tasake kallonta kawai ta kasa bata amsa a haka aka fita da ita .. Hankali Aisha yayi mugun tashi gashi sakina ma tun magariba tace zata je gida yakai wasu kaya ta dawo Amman shiru sai duban hanya take yi ,ta kalli aunty data rike hannuta zata fita da ita tace aunty sister fa ?ta tafi bata dawo ..aunty tace sakina ba nima narasa meya tsayar da ita Amman tunda motocin da dan yawa Killa ta biyo wasu a haka aunty ta tafi da ita badan Aisha taso ba a raayinta taso ajira sakina ..aunty Maryam sai sauri take ganin tara saura .. Aisha dai tagama sadaukawar zuwanta gidan Abdullah koma meye zai faru daita tabarwa Allah komai.. ita takara karyawa aunty zuciya tasata hawaye da har ta zauna kusan karfe goma a gidan wanda sakina ce ya cancanta ta zauna wannan lokacin to ita Kuma kwata kwata tunda ta tafi bata dawo gashi kowa ya tafi shiru gidan har aunty ta fara ganin rashin hankali ta ,sannan suka jiyo karar shigowar motoci guda biyu Dr sagir ne da Abdullah sai salis da RK suka iso yayin da Dr sagir da Abdullah shigo falon salis da RK suka tsaya a waje wanda daman agidan zasu kwana da sauri aunty Maryam ta Mike shi kennan Allah yabamu alkhari Aisha ta rike ta gam jikinta har karkarwa yake aunty tace bakya son gobe na dawo kennan? tace ina so tace to sakeni Dr sagir ne yasoma dawo kai daidai nan Aisha tasaki aunty da sauri ta zauna ta kara rufe kanta Abdullah har da dan risinawarsa ya gaida aunty Maryam da sauri ta amsa tafita daman akwai deriban dake jiranta zai mayar da ita .suna shiga wani hotonsu da computer ta hada tamkar dai tare suka Yi ita da Abdullah ya doki idon Dr sagir yace kai friend za'a hafi hurul aini fa a gidan nan . Abdullah yadan kalli pics din bai ce komai ba yayi gaba yasa hannu ya kunna AC yana cewa kai zafi fa yana gyara labule Dr sagir to idan ita amarya sanyi take ji fa?ko amarya shr ba amsa shima Abdullah bai Yi magana ba ,ya dawo kusa da shi kan doguwar kujera ya dan shinhida wanda har yanzu bai kalleta ba ,Dr sagir yace idan Kuma akayi sa'a ita ma amarya haka take kaga sai ku yi ta zama a kasahen turai duk maganar da Dr sagir yake Yi Abdullah shr yayi yana ta danne danne waya .ita kuwa Aisha shigowarsu ta shiga wani yanayi musamman da ta tsinkayi kamshin turaren Abdullah wanda ko a ina be sai ta shida shi.kuka tacigaba dayi kasa kasa wanda shi Dr sagir bai gane ba Amman shi Abdullah ya gani ya bar abinda yake yana kallonta kukan yarinka shiga jikinsa har Dr sagir yana magana ba shi bai ji ba ya kalli shi yayi murmushi yace wel ni bari in barku ya Mike yana duba agogon hannushi yace to 11 yayi musu addu'a yace amarya kin ki muga idanunki..suka fito tare da Abdullah Dr sagir yace to a dai bi a hankali naga har kasoma birkicewa kasan dai Aishi dai she is young Abdullah ya zabga masa harara cikin murmushi yace Shari Kuma zaka min wani sharri kai da ka dade da barin duniyar da muke ciki sai dana taba ka fa ka dawo haiyacinka gabadaya suka tafa suna dariya Dr sagir ya wuce yana masa sallama yayin da shi Kuma ya leka salis ya tabbatar masa da arufe koina .....
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62