Skip to content

Chapter 21

Chapter 21

Zuciyar Masoyi Book One Complete Hausa Novels 1 1,200 words 0 views Progress saved
Download Book

cikin kayan da Abdullah yataba kawo mata ne wanda ta watsa masa aunty Maryam na kallon sarkar tasan mahimmanci ta farin gold ne inna ma bazatasan matsayinta ba shine ita ta dauka ta ajiye agunta dan akalla zata kai haif million a wannan lokacin da suke ciki sarkar guda biyu ce sai zobe da dan kunne duka acikin gidansu. bakaramin kaya ya hado mata ba Kannan kaya mayuka bra da takalma tamkar mai shirin hada lefe kowa yaga kayan bby Aisha akema godiya ita ko Aisha har da kuka dan tun jiya aunty Maryam ta hanata sakat da maganar sa har yau da aka dase taruwa a gidan aunty ,tun aunty na nasiha har ta koma rarrashinta tana idar da sallah la'asar ta shirya zata gidansu sakina akace mata ga Abdullah yana jiranta a waje .jitayi kmr tayi tsunsuwa ta fice batare daya ganta ba ,in yaso ace batan don taso kwarai taje taga sister dinta ta riga ta shirya kawai ta fito gurinsa sanda ta sameshi a falon baki yana tsaye daidai kofar data bulla waje da waya a hannushi yana yi ta nemi kujera ta zauna tana dan kallonsa a kaikaice wai don Allah me wanna halitta shine ke bata lokacin sa akaina kalli yadda yake turancinsa a waya baza ka taba cewa yana jin hausa ba yana lura da ita da kallon datake masa Amman yayi kmr bai ganta ba yacigaba da wayarsa ya leka yayiwa salis magana sannan ya juyo kanta tayi masa kyau Sosai kwalliyar ta koda yaushe a saukake bakin less mai rawa har manne mata yake ajiki. iya tunanin sa shi tayiwa kwalliyar dan haka daf da ita ya zauna yana mata murmushin yana cizan lip's dinshi yace kinyi kyau Aisha like a bride batace komai ba ta sake hade jikinta ganin datayi ya zauna kusa da ita sosai a hankali ta gaisheshi yana jin dadin, hakan yana nuni ita din mai tarbiyyace sun jima a haka yace Aisha today is Saturday what about our discussion ta dago dara daran idanunta ta zuba masa ya amsa mata da idanunshi da suka gama rikecewa ita sam tun ranar inda suka gama maganar anan tabarta yace please Aisha sanar dani me ZUCIYAR ta yanke a kaina?to Abdullah dai yagama daureta ta koina bata da hujjar ce masa ta manta da maganar da sukayi kuma ko ba haka ba ita yanzu idan tace bata son sa tasan baki ma kawai ya isheta ta dago suka hada Ido kwarjinsa duk yacika gurin, ita kawai yake sauraro ta sunkuyar da kai ya kuma cewa please tell me Aisha ta dan ja numfashi ahankali har ta rufe idanunta tace shikenan idan Allah yayi sai ayi" ya karkata kansa kasa ya jefa idanunshi cikin nata suna kallon juna yace you mean inje in neme auraki in Allah yaso sai ayi ta daga masa kai, kawai bai San sanda murmushin ya subuce masa ba , komai nata sai taja masa aji yace thank you my Aisha Allah ma zaiyi da ikon sa jikina yana bani ke din rabona ce ,duk kuma sai taji ta takura awajen ta dan kalleshi murnar datagani a fuskarsa ko ranar daurin aure ce sai haka ya sake cewa na gode Aisha kennan kin amince kina sona zaki aure ni a hankali yake maganar don yadda yake maganar kasa kasa kmr maiyin rada har yasa Tarinka jin wani iri abu ajikinta ya kuma cewa kin amince nazama abokin rayuwar ki tana jin hucin maganar sa a saman wuyanta gabadaya ajikinta yagama mutuwa murus kawai ta tsinci kanta da rufe idanunta duk ya ruda ta da maganganun sa idanunta har sun ciciko Abdullah ya gane yanayin da tashiga sai yayi shiru ya kafe ta da idanunshi yanason tasamu natsuwa shi kam tun ranar da yasoma ganinta ya wuce wannan matakin datashiga, shr yabakunci gurin na wani lokaci duk da haka bbu wanda yayi kokarin cewa komai Abdullah ne yasoma magana sunana Abdullah kmr dai yadda kika sani nine "da" na farko awajen iyayena akwai sister ta me bimi Fatima sai auta amina haifeni a China Amman mahaifinta asalin Yar Egypt ce can nafara karatu daga baya kuma yakasance duk inda muka zauna sai nayi karatu nayi university a jami'ar Oxford ina karantar final art,nayi Nisa afanin saboda wani dalili yasa na canza Carrier na koma karanta business shine dalilin dadewata ina karatu bayan nagama ne yanzu nike aiki a I.M magariyya company a matsayin M D na company yadanyi shr sannan yacigaba teema tana university of aliero yayin da this year amina tagama secondary school tare kuka gama kennan yace bana neman mata Aisha sai dai nata ba shan giya sau daya Amman har yanzu ina yin smoking ina shan sigari sosai musamman idan ina cikin damuwa ko bacin rai kuma har zuwa yanzu dady da mami basu san ina sha ba sai dai su fuskanta domin nakan kiyayye lokacin haduwa ta dasu kafin na sha. sauran bayani Aisha idan muka kasance tare zaki sani.tan dan kalleshi a hankali can cikin ranta kuma tana mamakinsa ya kalleta yace uhmm tambayi abunda baki fahimta ba ta girgiza kai can cikin ranta tana tunanin matsayinsa danata bazai taba zuwa daya ba da Kyar ne yuwar abun da yake so Abdullah balarabe ne kennan ta tambayi kanta ina ita ina shi take ayyanawa sai Kuma taji ya birgeta daya fada mata gaskiyar halanyensa ... Washegari... MMN SUDAIS CE [3/12, 3:01 PM] Kaunace Sila: 💗💗💗💗💗 ZUCIYAR MASOYI 💖💖💖 💗💗💗💗💗 AISHA A BAGUDO Page 11 Washegari ma yazo sai dai bai wani dade ba ya tafi ,byn ya matsa mata akan me take bukata koda tace ba komai ya daure fuska gabadaya sai taga yanayi sa ya canza ,yace dan bata damu da shi bane shi yasa bata son wani abu daga gareshi ,da Kyar ta iya ce masa ko menene sannan ta samu lafiyarsa ya tafi Amman duk da haka bai saki ransa ba, dan shi ji yake tunda ta amincewa aurenshi duk wani nauyi nata yakoma kansa .ranar sunan aunty Maryam bby ta amshi sunan maimuna wato sunan innarsu tun alokacin ake kiranta da khairat . Tun wajen goma sakina tazo Aisha ko wanka batayi ba saboda bakin da suka agidan bandakin tashiga ta fito da ruwan wanka bayan gida tajata suka zauna akan kujera ta kawo mata dan abinda aka gama cikin jin dadi da murna tace sister Amman sai dare zaki tafi ko ? sakina tace nan da zuwa Shabiyu zan tafi shi yasa nazo da wuri zan raka mama unguwa ne tace kai sister sakina tace Allah kuwa namazo miki da albishir din result ya fito Aisha ta dafe kirjin ta ce dan Allah tace da gaske can kuma jikin Aisha yayi sanyi sakina ta tambayeta yana ga jikinki yayi sanyi" taja tsaki ni wallahi wannan Abdullah din shi zai takurani da Kyar zan Yi ma karatun.sakina ta kalleta kawai tacigaba da wata maganar daban dan batason jin zance Aisha ta lura da yadda Aisha tadan sauya akan Abdullah yanzu ,Amman itama sai tashare tacigaba dayi mata wata hirar sakina ta zuba mata Ido ,wani haka yake da sa'a a rayuwar sa ta tuna jiya gurmin da aka sha agidan su akan ita Aisha a dalilin abbansu ya

Table of Contents

Chapters

62 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62