Skip to content

Chapter 7

Chapter 7

Zuciyar Masoyi Book One Complete Hausa Novels 1 1,187 words 0 views Progress saved
Download Book

Allah zai kawo yaran suyi karatu tunda shima daman akwai soyayyar karatun aransa Allah ne baiyi ba,a haka suka rabu A aminu yace zai nemeshi acikin kwana kin nan. Mlm abu zaune akan titi da suke kafa teburin takalma shi da makwabcinsa mlm dauda suna hira mlm abu yana dariyar mlm dauda yana bashi labarin iskar daakayi jiya cikin dare wajajen biyu saura shi Kuma a lokacin ya farka daga bacci ya tashi ya nufi bayi sai ya iske wani abu baki yana reto a kofar bayangidan, ya tsaya cak bai Yi auni ba sai iska ta fizgo abun yayo kansa aiko ya juya da gudu hannu rike da wando har yana bigewa da abun ya kusan hantselawa yashige daki yana kokarin rufe kofa ne abun ya sauka kasa sai yaga ashe ma bakar Leda ce ,mlm abu yana cikin dariya motar A aminu ya tsaya ya fito mlm abu yarasa inda zai sanya shi dan murna sai kujera ya aro can gaba da su suka samu guri ya sanya masa ya zauna sun gaisa mlm abu yake nuna mamakin ganin A aminu a daidai wannan lokacin domin duka goma na safe a lokacin, A aminu ya shedamasa yasamo masa aikin tuki a kamfan buga jaridu Amman sai idan akwai takarda shedar yayi koda primary ne mlm abu yadan jinjina kai wannan shine ga koshi ...... sannan ya dan dada matso da kujerar sa tamkar wanda bai son wani yaji abunda zai fada daga bisani ahankali yace ai alhj bbu wayannan takardun da Ake bukata kmr yadda nike gaya Maka ni ban taba shiga aji ba dan a koyamin boko ba . A aminu yace ai nasani nadai sanar dakai ne Amman ba wani abu akwai aikin share share ban ruwan da shukoki a maaiakatar fata shi wannan zasu daukeka koba takardu daman hannu biyu na raba abun, Amman shi albashin sa bai kai wancan ba . Mlm abu yace bbu komai ya kara godiya alhj aminu yaci gaba abun na biyu maganar Gona ina ga ka iya shawara da manya koda rabi ne sai a siyar tunda kace ku biyu ne gareta akalla kana da kusan kaso 3 aciki 4 na wannan Gona idan an saida rabin ragowar sai asamu mai aiki duk shekara anan biyansa ko yaya dai za'a samu abun bukata hakan kai km wannan aiki da kasamu In Allah yaso idan komai ya daidaita za'a samu abun rike iyali da shi. Yasake jinjinawa A aminu da wannan shawara mlm abu yakasa magana yayi murna matuka A aminu yatada motarsa ya wuce duka dai a wannan ranar rasuwar mijjn kanwarsa Laure ya samesu dan haka mlm abu ya hada kan yara suka tafi bayan share makoki mlm abu ya nemi kanin mahaifinsa da maganar saida gonar da abunda zaiyi da kudin ,yabashi goyan baya dari bisa dari sai da Kyar aka shawo kan iya ta yarda byn kwana biyu suka shirya suka tafi kaoje .a wannan zuwan ne da innarsu yusif tayi gida ta tadda labarin zuwan dan uwanta har da yayashi guda uku a inda masu sanar da ita labarin sukace yasha kukan mutuwar Nene wato mahaifiyarsu tunda daman mahafinsu ya dade da mutuwa, itama dai kuka tayi sosai saboda shi kadai yarage mata sai dangi ,kawunta yabata address din inda yake acikin birnni kwanansu biyu suka dawo zariyar Kala kala . Washegari daya dawo ya nufi gidan A aminu da tsaraba kauye irin su dinya da kadeyya , sai dai be iske sa ba ya bar sallahu tsarabar dayakawo masa ,duka dai a wannan Daren A aminu ya riske sa byn sallah ishai sun tautauna akan batun inda A aminu ya nuna baison yabashi bashin kudi a lokacin gara yakawo masa gidan sai byn wata uku mlm abu yakawo ya danka kudin a hannu A aminu a lokacin suna Tare da wani abokinsa tare da dillalin gidaje anan dai aka gama magana . A bangaren mlm abu bai taba tunanin gidan zai iya zama malkinsa ba musamman dayake abunda da ya hada ya bada duka baifi rabin kudin gidan ba wannan matsala shiyasa yasake kebewa da A aminu akan hakan nuna masa yayi ko kadan kada yasanya wata damuwa akan haka Allah zai bada yadda zaayi saannan yakara jaddada masa takwas nasafiya jibi litinin tayi masa a gidansa ,domin kai shi wajen da zai fara aiki tun satin da yagabata Ake neman sa da sanyi jiki mlm abu ya kara yi masa godiya. Da taimakon Allah mlm abu yasoma aiki km yana samun cigaba dan haka aka soma saka Maryam da yusif makaranta boko kafin daga baya aka saka Umar byn aikin share share mlm abu yasamu aikin gadi . mlm abu shi da abokin gadin nasa suke aiki haka Inka saleme sallah asuba zai tafi aikin share sharen sa da ban ruwa duka karfe goma batayi masa ya tafi gida ,inda abunda zaiyi a gida sannan ya huta mlm abu bayasamun wani Hutu sosai a dan wannan lokacin domin muddin ya dawo karfe goma yakan huta zuwa karfe daya zai tafi gadi haka rayuwarsu tacigaba cikin rufin asirin ubangiji . Innar su yusif zaune tayi ta gumi tana kukan Bakin cikin abunda matar dan uwanta tama byn tabi address din da kawunta yabata ta nemi idan yayanta yake duk ya karfeta hannu biyu hade da murnan ganin juna, Amman sai dai bata samu karfuwa a wajen matar gidan ba, haka tadawo jiki atsanyaye tana kuka da alkawarin muddin bashi ne da kansa ya nemeta ba bazasake neman sa ba har abada ga gida iya gida da daular da yayanta ke ciki Amman ita tana cikin kangin rayuwa . A wannan lokacin ne amarya A aminu ta haihu . Yadda mlm abu yadauki A aminu tamkar wani danuwansa km duk abunda zaiyi sai yayi shawara da shi, anashirya Aisha akwaita wajen kawarta sakina duk lokacin basu haura shekara 3 ba , su dade suna tare hakan yakasance ga mlm abu . Aisha suna da shekara hudu A aminu yayiwa mlm abu maganar sanya su Aisha makaranta shafe fagen shiga primary yace bbu laifi ai dukkan su naka ranar har da mlm abu aka tafi domin tun asuba yasanya inna yimata wanka .aji guda aka sanya sakina aminu da Aisha abubakar bahindi hakan nan makaranta ce ta ya'yan masu kudi . A bangaren mlm abu yana gwada iya kokarin sa akan duk abunda ya gano na ya'ya mata sai ya siyo biyu yakawo Aisha da sakina wani lokacin sakina na kallon mamanta zatakwace ta hanata amfani dashi tace anga masu ke ma bakauyiyace irin su ,a wannan lokacin suka shiga aji 4 a primary ko Aisha taje gidan tafi sake awajen aunty amarya hakanan mama na matukar kyashi akan makudan kudin da A aminu ke kashewa awajen karatun su gashi Aisha na neman tafi yarta illimi . A bangaren Aisha kuwa duk da yarinya ce a lokacin Amman ta fuskanci abunda Maman sakina ke nuna mata dan haka rawar jikin da sakina keyi na zuwa gidan su ita bata yi ,km har zuwa wannan lokacin inna batasan abunda ke faruwa ba Lokacin na dada ja rayuwa na canzawa kasuwanci A aminu na dada gaba domin zuwa wannan lokacin yadaina aiki gwanati sai kasuwanci da tafiye tafiye

Table of Contents

Chapters

62 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62