Skip to content

Chapter 19

Chapter 19

Zuciyar Masoyi Book One Complete Hausa Novels 1 1,198 words 0 views Progress saved
Download Book

natsuwa , Aisha ta sauke hadiyar zuciya ta dan sake kallon gefen da yake Abdullah ya gane tana son ta tafiya ne ya dan ciza lip's dinshi yana mai duba agogon dake daure a tsintsiyar hannushi yace bari in tafi sai zuwa gobe a nutse take magana tace ai gobe bana nan Abdullah yaji gabadaya ya rikice shi fa baya kaunar yaji zata fita ko yaganta awaje ya dube ta sosai yana mai kafeta da Ido zaki je ina kennan? Tace zamuje ka'oje yasake maimaitawa ka'oje ....... Yasake cewa Kuma ke kadai zaki tafi tace da yaya Ali , Abdullah yayi shiru yana tunanin throughout gobe cikin busy yake a office bbu halin ya subuce ya kaita ya girgiza kai yace shikenan akwai maganar dazamuyi dole sa kin dawo kennan" Amman zan ga yaya Ali kafin na wuce "tayi shiru ta kalleshi daga baya ta gane me yake nufi ta Mike ahankali Ta shige ciki yabita da kallo yana addu'a Allah yanrantsar da rabonsa atare da ita ,har sanda ta fito yana zaune tace yaya Ali bai nan"yayi shiru sannan ya Mike tsaye cikin sanyi jiki yace to Aisha sai kin dawo kennan.yadda yayi maganar cikin shagwaba da langwabar da kai tamkar yaro karami , kamar ba hakan yaso ba shi ya kusan bata dariya sai kawai tayi murmushi ta juya ta shige ,yaji tsanyi aransa yau duka sa'ar a gurin take ciki fara'a yasa meta yau ta dan sake dashi ",har tayi magana mai dan tsayi dashi gashi har da kyautar murmushin da yafi bukata atare da ita ya lumshe idanunshi bai ki ace a daura aurensu a daren yau ba saboda gudun kada ta Kuma rikice masa yau tazo masa da abubuwa da dayawa masu mahimmanci........ MMN SUDAIS CE [3/12, 3:01 PM] Kaunace Sila: 💗💗💗💗💗 ZUCIYAR MASOYI 💖💖💖 💗💗💗💗💗 AISHA A BAGUDO Page 10 Ita dai bata San waye ya kai su ka'oje ba, Amman ta gane type din motar da suka shiga limousine ce bbu abunda bbu na jin dadin rayuwar dan Adam a cikin motar daga ita sai yaya Ali sai direver haka Kuma da suka isa direver bai juya ba sai da mlm dahiru ya tsareshi yayi sallah yaci abinci sannan yabaro ka'oje . Duk wata ayar Allah dake raunana ZUCIYAR dan Adam sai da mlm dahiru yasanya aka rubuta mata ita , inna hajo tasa ta a gaba ta shanye tsawon kwananki uku ranar alkhamis suka je har zariyar Kala kala sukaje Suka dubo iya har gidan gwaggo Laure suka je kwanan su biyu suka dawo ka'oje washegari tun safe Aisha ta shirya a tsammaninta da wuri zasu taho ,yaya Ali yace sai an sauko daga masallaci dan haka shigewa dakin inna hajo tayi kwanciyar ta,koda ta tashi tayi sallah komawa tayi "can cikin bacci taji inna hajo na tashinta "anyi baki daga kebbi duk da gurin a gyare yake Amman sai da inna hajo Ta shiga sabon gyara mlm dahiru yashigo da sauri yace ya tura kasuwa a siyo musu kwaryar nono da kwan zabi ta bayar da kwano me kyau za'a diba a damo musu fura cikin rawar jiki Inna hajo ta Nemo kwanuka biyu sababbe ta Mika masa ,ta tura yaya Ali yayi maza ya karbo zabbi a gidan kaninsa yakai can gidan su innarsu a gyara yanzu ta fito da sababbin tabarmi a karkashin gado ta aika dasu waje ta shimfida daya anan tsakar gida .duk Aisha na kallonta ta Mike ta nufo inna tana tambayar ta ita ko sai hada wancan da wancan take ,sanye take cikin riga da wando na wani material na kasar India mai kalar orange abokiyar aikinsu aunty Maryam ce taba ta tsaraba yayi mata kadan shine ta bawa Aisha ta tura gashinta cikin farar hula , Amman saboda yawan gashin sai daya burtso ta baya da wanda yabi gefen fuskarta tananan tsaye taji murya mlm dahiru yana Bismillah. Juyawar da zatayi idanunta suka sauka akanshi tare da wani suna shigowa kamshin turaren su tuni ya game gurin cikin shiga ta alfarma,"sanye Abdullah yake cikin farin voyal mai ratsin gidan sugar dinkin doguwar Riga zuwa gwiwa kallo daya zaka masa kaji yayi matukar birgeka , cikin sanyi jiki Aisha ta juya ta shige daki,abdullah da Dr sagir ne a zaune kan tabarma suna gaisawa da inna hajo tace ai bangane mijin nawa ba acikin ku,naga duk kun shawo min kwalliya Dr sagir yayi dariya ai kowa so yake ki zabe shi , sannan ya nuna Abdullah . Abdullah ya sunkuyar da kai "Inna hajo Tace Af to kai me ya tsaya birge ka da wannan mai karamin bakinta koko muryar ta ne mai kama da ta gyare ce ta dauki hankali ka ,sukai dariya gabadaya tace Allah in kuma ma jar fatar ce kai ma ga ka nan da ita" Dr sagir yace kodai ya fasa da ita ne ya dawo gunki tace ashe dai kagane ". suna zaune akarinka shigowa da kayayyakin tun daga bahun Hunan shinkafa taliya makaroni sabulai abun dai tamkar za'a bude shago"tsarabar su Abdullah kennan mlm dahiru yarasa inda zai saka bakinsa dan gaskiya ya yaba da Abdullah yaji ya kwanta masa a rai cikin lokacin daya "kyautar kudi kuwa Abdullah tamkar wanda yake da injin bugo su agida "mlm dahiru har kasa magana yayi sun sha fura sunci zabbi da aka soya musu anan sukayi la'asar sannan sukayi shirin tafiya Aisha dai tana daki tamkar ta fasa ihu da Kyar tayi sallah ko abinci kinci tayi ta sanya dan guntun hijab hular kanta ya sauko mata iya kafadarta ,farin takalmi tasa sai farin handbag data makale a hannunta ,a haka mlm dahiru yakarayi mata nasiha ta fito dan hasken ranar da ya nufi gabas zai fadi tana fitowa shi ya hasketa tasa hannu ta Kare fuskarta ,Dr sagir ya kallota ya girgiza kai yayin da yadan zunguri Abdullah ga madam nan fa. Abdullah ya kalleta tsab yayi murmushin a hankali yace ai aganinta duk mun matsa mata ne fa,suka sa. dariya ,lafiyayyun motoci tamkar na wasu shugaban kasa aka bude mata daya ta shiga ta gane direban da ya kawosu ne,ashe Abdullah ne ya turo shi,mlm dahiru na tsaye har sai daya ga tafiyar su tare da tsaraba man shanu nono fura kwan zabbi musamman dayake lokacin sane.salis da yaya Ali sune a motar gaba sai musa dake tuka su a dayar mota kuma shida Aisha a baya yayin da Dr sagir a gaban gurin me zaman banza Dr sagir ke ta kokarin janta da hira wani ta amsa wani tai shiru shi kuma Abdullah inda ka ganshi tamkar wanda akayiwa gafara jin sa yake kmr ya aure ta ne sun fito yawon ziyara yasa hannushi ya dauko jakarta dake kan cinyarta tana kallonshi batai magana ba har ya bude bbu komai a ciki sai kayan make up dinta yayi murmushin ya Ciro wani passport dinta na makaranta da uniform a jikinta har da dan kwalin perfect akanta ya zubawa hoton idanunshi sannan ya dago ya kalleta itama anyi sa'a ta dago da niyyar ta saci kallonsa ai kuwa suka hada Ido ,Ido cikin Ido suke kallon juna ya kashe mata idanunshi daya yayi murmushin ya zura hoton a aljihunsa , Aisha ta dauke kanta tacigaba da kallon hanya

Table of Contents

Chapters

62 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62