Skip to content

Chapter 29

Chapter 29

Zuciyar Masoyi Book One Complete Hausa Novels 1 1,195 words 0 views Progress saved
Download Book

kirayen sallah asuba sannan dady yatashi ya sak e wata alwala , bai tashi ba har sallah asuba ya dade yana rokon Allah yatada masa dansa ya bashi lfy kamar da ,to daman dai dady ba daga baya ba wurin ibada .... Kwana da yini sannan Abdullah ya farfado cikin sa'a da nasarar aiki ya dawo hankalisa da natsuwa, daga mami har dady suna tare dashi ,a ranar Abdullah yana kallon suna ta tattalinsa sosai a zuciyarsa yace ni duk bawan tattalin nike so ba ni dai kubani Aisha kawai yana kallon mami abubuwa suna sake masa yawo tamkar mafarki wai bazai auri Aisha ba ...... Cikin kwanaki biyar jikin Abdullah ya fara kyau sosai wanda har dady da kansa ya amincewa hakan saboda haka yayi shirin komawa Nigeria ya bar mami a gurinsa domin ayyuka da dama sun tsaya bbu shi bbu Abdullah ranar da Abdullah yayi sati biyu yabaro Germany bayan ya sakar musu kudi sosai ta koina hatta likitoci sun san da zaman Abdullah a asibitin kwanan dady uku da tafiya su teema suka biyo jirgi dukkansu sukazo ganin Abdullah , Amma kwanan su uku teema ta juya tabar minal .. Jikin Abdullah yayi kyau sosai illa dai har yanzu baya Jinsa daidai kmr da musamman kirjinsa saboda buguwar da yayi karayar kafadar ita ma ana san ran kwancewa cikin kwanaki kadan masu zuwa Asibiti shikadai yake cikin daki dan basa son dan jinya dan haka mami da minal da suke tare da shi sai an basu izinin shigarshi sannan suke ganinsa ,dan haka kowane dare Abdullah bai iya runtsawa ta koina ya juya Aisha tana manne da zuciyarsa shi ahankali yake tunano maganar da tayi masa daren da zai tafi ,..nasan zakayi nasara in Allah yaso.... Ya lumshe idanunshi tasan shi fiyye da yadda yasan kansa kennan ,ya tabbatar zata iya kula da wasu al'amuransa idan ya aure ta , Amman duk hakan da ya gano ita mami bata gane ba ,mami bata son Aisha kennan .....yaji . gabansa ya fara faduwa kmr kullun idan ya tuna hakan yanzu idan mami bata hakura ba shikenan ba zai auri Aisha ba? ya sake tuno kalmarta ta karshe gareshi I will miss you too....to ko daman tasan shikenan su rabu baza suyi aure ba shi yasa ta fadi hakan ,da sauri yayi jifa da magunguna da suke zube a gabansa yasoma juya kansa NO I can believe this i can believe this ....da sauri nurse tashigo tana tambayar sa me ya faru nan da nan ya natsu ya dawo haiyacinsa yasa tafin hannushi duka ya rufe fuskarsa dashi ....yawanci idan ya kwana da tunanin irin haka da safe km lokacin da su mami suka zo yake samun bacci .. To yau idansa biyu har an samu suna hira da mami minal a gefensa ahankali mami take tambayarsa yadda abun ya faru Abdullah ya dago yana kallon mami ya fahimci shi take sauraro sannan ya sunkuyar da kai yana wasu wuraren na budewa a jikinsa bai tsaya boye mata komai ba tun daga yadda sukayi da mlm abu har zuwa sanda ya shigo mota ya taho gida baya cikin natsuwar hankalinsa saboda tunani har sanda ya lura daf din katako a gabansa tana yimasa hon yayi kokarin dauke kan mota Amman ya makara , mami ta xuba masa Ido har sanda yagama sannan shima ya jefo mata tasa tambayar , cikin tsanyi murya yace mami wai da gaske ba Kya son na auri Aisha ...kince a aurar da ita gawani ?.... Gabadaya ZUCIYAR mami ta gama hautsina a tun labarin sa na farko,tamkar mami ta manta a inda Abdullah yake ta daga masa hannu tana nuna shi da dan yatsanta tace kai Abdullah yanzu dama a dalilin diyar wadannan banzayen mutane kake neman kashe kan ka ..... Gaban Abdullah yayi mummunar faduwa a kunnenshi mami ke zagin mahaifan Aisha,ka tayarwa kowa hankali kasa mutane cikin wani hali , to bari kaji muddin ina raye bazaka auri wannan banzar yarinyar ba lallai na yarda da maganar hafsa da tace sungama da kai..... Duk wata jijiya ta jikin Abdullah sai da ta sage ya kurawa mami Ido tana magana idanunshi ya fara kadawa a yadda yake Jin tashin hankali yafi karfin ayi masa kuka sai dai jan Ido a hankali ya zamo da kyar daga kan gadon da yake "ya zube a gabanta mami me yuwa so yasa Abdullah ya manta ida yake kuma ya manta gaban wa yake yace komai zakiyi min kiyimin mami Amman dan Allah kiyi hakuri ki tsanya hannu a aura min Aisha karki ce dan Allah mami wallahi mami Aisha bata da wani aibu tun ban kai haka ba nake rokon Allah ya samin son matar da zan aura kadai to tun haduwata da ita nasan itace wacce zanyi rayuwa da ita....mami ta kalleshi shekeke tace idan da gaske kai asirin su yacika mu bai cimu ba idan baka cikin nutsawarka to ni ina cikin tawa kai baka da Ido ne baka lura bakasan abinda yadace da rayuwarka ba ,mami tashiga juya kai tace "Oh"my God wlh Abdullah ka makance kaban mamaki duk wayewarka ka tsaya ajin wannan yarinyar kuma nasake Jin kamin zance banzar yarinyar nan uhmm ta jijjiga ka sannan tayi shr tanajin wani iri a ranta kmr tayi kuka shikenan asiri yayi tasiri akan danta mafi soyuwa acikin yayanta.... Hakan ce yasa Abdullah sake Jin tamkar wata cutar ce ta dada shigarsa ya kara wargajewa nan gaban mami tana lura da shi ranta yasake baci ,tace Abdullah ba cuta ba koma meye sai dai kayi Amman aure tsakaninka da wannan yarinyar kasawa ranka bbu shi har abada ..ya sake motso mami yana girgiza mata kai dan Allah mamina karki min haka ki duba halin da Abdullahnki zai shiga sadin rabasa da ruhinsa ta waro idanu waje tace bari kaji ko zaka sai dai......sai kuma tayi shiru tana jijija kafarta daya basake cewa komai ba ,ya kuma dada tabbatarwa ransa yarasa Aisha kennan tunda yakoma kan gado ya rufe idanunshi bai sake motsawa ba idonsa a rufe bai sake magana ba har sanda mami tagama maganganun ta na bacin rai....har washegari haka yake kwance tamkar mutun mutumi da yayi sallah sai ya koma ya kwanta ya runtse idanunshi ,ran mami yayi matukar baci akan halin da Abdullah yake shirin jefa kansa ,Abdullahnta da baya iya koda musu akan duk wani abu data yanka masa "Amman yau Abdullah ya fara canza mata akan wata yarinyar can yadda yake Yi yanzu ya kara tafasa mata zuciya cikin fushi mami ke cewa zata koma gida tabar shi in dai kan wannan yarinyar ne yake haka sai dai yayi duk ma abunda zai yi ita dai bazata yardar masa da auran yarinyar ba. Idan ba wacce ita da kanta ta amincewa ba. Komai ya dada kwance masa a daren mami tabaro Germany ko kadan bai dauka mami zata taho tabarshi ba hakan yasa yakara sanin dolensa ya hakura da Aisha......itama mami ba da san ranta tabaro dan nata ba dan bazata juri ganin Abdullahnta cikin damuwar da tasan bazata iya masa maganinsa ba... minal kawai tarage masa atare dashi itama tun tafiyar mami duk taji bbu dadi Abdullah ya wai go ya kalleta yana jingine da gadon dakin

Table of Contents

Chapters

62 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62