Chapter 13
Chapter 13
Kuma hakan ya karawa Aisha kima a gurinsa domin yanzu dai yasan ko bbu komai yasan mlm abu ba zai taba mata auren cin fuska ko na kudi ba wannan ya nuna ita din mai daraja ce a gurin iyayenta Kuma ko da Allah yayi shi din ne zai aure ta yasan badan kudinsa suka bashi ba , kodan wani abu nasa ba . Abdullah yayiwa mlm abu godiya sosai ya nuna ya fahimce shi ya Kuma ji dadin yadda ya nuna yana kaunar sa ta bangaren Aisha kuwa zai cigaba da kokarinsa in Allah yaso da kansu zasu kawo kansu a daura musu aure .kasa tafiya yayi sai da yaga Aisha domin dai har lokacin jiyake tamkar zata kubuce masa ",Amman ko sanda tafito ya zuba mata idanunshi zuciyarsa na sake hango masa ita tare da wani wanda bashi bane " Abdullah yadan bata rai yakafeta da manyan idanunshi yayi kasa da murya yakira sunanta cikin kwarewa da harshe turanci Aisha waye wanda na ganku tare dazu ?tayi shiru ya sake maimaitawa ta dan dago kai cike da dakewa tace da shi wani ne. Abdullah yace Ok kina son kice min saurayinki ne "ina ganin ba mutunci ki bane kidinga tsayawa da namiji a waje kowa zai wuce sai ya kalleki .ita kam Aisha wannan magana dayayi ji tayi tamkar ya zageta ne dan haka rikici ya balle a atsakaninsu ,shi Abdullah da yaje da nufin shawo kanta gashi ya fito da kishinsa karara komai yasake tabarbarewa, dan haka da fada suka rabu . Amman cikin week din dole ya hakura ya dawo yashiga lallabata domin dai tunda yasan tana waje yanzu yasan batasa bace shi kadai . Haka Abdullah ya dinga iya kokarin sa akan Aisha a kalla kullum sai sanyata a idanunshi sannan zai samu zaman lafiya "ba dare ba rana muddin yataso daga office kai tsaye inna yake turawa dan aike ta turo masa Aisha haduwarsu da sakina ya zaman masa tamkar ya samu mai tayashi lallashin Aisha ne Amman bangaren sakina kuwa haduwarsu da Abdullah bakomai yajawo mata ba facce tashin hankali da da tsinkewar ZUCIYA . Bangaren mamin Abdullah kuwa magana hada yayansu aure ta zauna daran Amman har zuwa wannan lokacin Abdullah bai San da zaman zance ba" domin ita mami tarigada tasan sai dai idan bata ce ayi ba ,indai tasanar da Abdullah zance ya zauna mama hafsa mai niyyar yin 1 week a gidan mami sai gashi ta share har kusan 4 weeks domin ganin daula da Hutu dake cikin gidan "ya dada haifar da shantakewarta , musamman da yake yanzu cigabansu mami sake gaba yake cikin sati na biyar tayi kokari tabar garin kebbi cike da alheri masu yawa domin ko Abdullah sai da mami tasa yama mata alkhari fiyye da yadda batayi tsammani ba, hakan bakaramin kara ingizo ta yayi ba shi Kuwa Abdullah yayi haka ne dan yakara wanke kansa awajen maminsa . Mama hafsa diya ce gurin dan'uwan mahaifin mami domin mami ita kadai iyayenta suka Haifa asalin mami balarabiyar ce wanda har yanzu iyayenta suna Egypt ,karatu yakai ishaq kasar China yayinda itama karatu tajeyi suka hadu suka soma soyayya daga baya yabita gun iyayenta wanda da suka yarda suka yi aure shima dan diyartasu ta nuna bijirewa ne garesu" byn sunyi aure daf da dady zai gama karatun shi cikin ikon Allah mami ta haifi danta namiji , aiya rayuwar dady bai taba ganin kamanni mutane haka ba like mother like son Abdullah na matukar kama da maminsa anyi hidima sosai daban mamaki .bayan shekaru masu yawa mami tasake haihuwa ya' mace akasama sunan mahaifinsa ishaq wato amina baacike shekara uku ba tasake haifo Fatima dady na matukar kula da family dinsa sautari yana zuwa Nigeria sai dai da ya shirya da niyar zuwa kauyensu sai yaji gabadaya kmr gabobin sun sage yaji kmr ana cinawa jikinsa wuta haka zai tattara ya koma bayare da yaje ba,cikin ikon Allah dady ke sanar da mami yanaso sukoma Nigeria mami tace sam ita bata san da wannan zance ba bakaramin tashin hankali sukayi da dady ba dan har yakai ga cewa zai kwaishe yayansa yatafi dasu nan Kuma ta gigice tace tayarda sukoma Amman ba'anason ranta ba " zama yakawo kanin mahaifin mami Nigeria dalilin wani abokin karatunsa yataho Nigeria har yadu da wata bayarbiya yamata ciki a Lagos aka haifi mama hafsa baatashi kai mama hafsa dangin mahaifin ta ba sai da za'a mata aure Sannan yanuwa suka ganta anan sokoto take aure "to dawowar su mami kebbi yasanya suka kulla zumunci sosai kasancewa mami bata da kowa Kuma bata taganin wani danuwanta . Kwance yake a falon mami kan kujera da yammacin ranar asabar kwanaki uku kennan da tafiyar Mama hafsa duk wani abu daya bukaci yana son ci an zube masa teema na hadawa tana mika masa yana ci yayin da mami ke kallon tashar larabawa sai da ta bari ya kammala komai sannan ta rage karar TV tare da Kiran sunanshi ,batare da ya amsa ba ya mayar da hankalinsa kacokan akan mami ,mami tacigaba ina ganin yadace ka ajiye maganar wasa kasan abunda zaka kama . Abdullah ya zubawa mami ido yana son fahimtar abinda take nufi ,mami tace ina ganin next week zaka tafi sokoto gidan mamanka data wuce akwai diyart faiza daneke son kaje ku daidai daita domin yana da kyau ace ka rufa shekarar nan da naka iyalin.mami ta maida kallonta gareshi domin duk maganar datake idanunta na kan TV. Yacigaba da kallonta iya rayuwar sa ba zai tuna lokacin dayawa mami irin wannan kallon ba "kallonta yake sosai har yanajin wani abu na cracking brain dinsa cikin natsuwa ya sauke idanunshi batare da ya iya cewa mami komai ba" tayi tsai da ranta tana dubansa a wasu lokuta yakan bata mamaki a shekarunsa , ilminsa basirarsa kaifin hankalinsa yace ace zuwa yanzu shi da kansa ya bukaci yin aure batare da anfara yi masa maganar ba "haka nan rayuwarsa ita kadai tafi gane waye Abdullah sai dan cikin Yan kwanakinnan da suka wuce ta fahimci yanayin da Abdullah yake ciki haka kawai wani tunani ya darsar mata a zuciyarta ko dai dan nata bashi da lafiya ne da sauri ta kawar da wannan tunanin ,wanda a fili tace masa "banji kayi magana ba" ahankali ya dago da kansa tare da kakaro murmushin dole yace shi kennan mami Allah ya kaimu zanje .mami tayi murmushi ,duk da dai yadda ta fahimci sa maganar bata wani ratsashi ba tunda ya fito daga part din mami yake kwance akan gadonsa ,wanda tun safiyar yau yakeson yaje yasamu Dr sagir ,Amman maganar mami ta sanya shi yakasa kakkwaran motse gabadaya jikinsa rawa yake tamkar nazarin ya ja bargo ya lullube gangar jikinsa ya kamo lip's ya ciza da karfi ya zubawa ceiling dakinsa ido tamkar maganin damuwar sa na wajen ,babban matsala daya, kasancewa mami ce tafara yi masa zance wata ba tare da ya shigar da maganar Aisha ba,gashi shi kansa bai fahimci kansa da kansa ba sai da yahadu da Aisha ya rufe idanunshi da tafin hannunshi yana magana tamkar tana kusa dashi , Aisha duk ke kika bata mana lokacin inda kin fahimce ni tun farko da tuni mami
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62