Skip to content

Chapter 23

Chapter 23

Zuciyar Masoyi Book One Complete Hausa Novels 1 1,182 words 0 views Progress saved
Download Book

yace idan mami tadawo zaizo ya dauketa ya kaita tayi mata gaisuwa ta amsa da to "Amman ita kam sai ta tsinci kanta tana mai tsoron shiga cikin family dinsu, Sun sake zama na musamman da dady akan maganar sa da Aisha ya shidawa dady ya sanar da iyayenta cikin satin nan zaizo bai dai samu mlm abu a gida ba Amman yagaya mata ta sanar da inna, ko gwaggo Laure da tazo haka tasa Aisha gaba da zance Abdullah shiyasa har daren ranar da dady zaizo din da Abdullah yazo sai da yasake tuna mata akan tasanar saboda yasan halin kayansa, sai a wayewar garin ranar lahadi mlm abu yafito zai fita suna sallama da gwaggo laure domin itama a ranar zata wuce sannan tashiga rumfar inna da Kyar take gaya mata inna ta hau salati ta fito tana sanar da mlm abu yakira Aisha yana Kuma tambayarta ta amsa da yau da yamma karfe hudu . Gwaggo laure tace ma'aiki anmabi Muhammad ke yanzu dan iskanci gidan sirikan naki zasu zo shine kika kiyin magana ? Inna zata kuma yin magana usman dakatar da inna yace ai mun godewa Allah ma da aka samu Allah ya matsi bakinta ta fada ,ai da sai dai anjima kawai Kuga baki, inna tace zata aika ai wannan yarinyar bansa halinwa ta dauko ba gwaggo laure ta rike baki tace miskili kafi mahaukaci ban haushi yarinyar kin zama sai kace harsashi acikin gida Aisha ta hade rai hade shigewa daki mlm abu yace aiko bai ga tafi ba nan da nan akashiga gyara gida ,dakinsu yaya yusif dake soro aka bude aka gyara da yake daya kofar ta fita waje gwaggo laure ma fasa tafiyar tayi yayin da inna tabawa usman kudin machine yaje yagayowa aunty Maryam ,tayi musu dan abun da zata tare su dashi mlm abu da kansa yabar komai ya tafi yagayawa alhj aminu domin a ranar zai Yi tafiya to haka nan alhj aminu yaji maganar daga sama dole dashi za'a karbi baki to shima din sai barin tafiyar yayi yana jinjina al'amarin Allah yadda ya kwallafa ransa akan yahada jininsa da yarinyar Allah bai nufa ba har sapani sukai ta samu da maidakinsa . Karfe uku aunty Maryam ta iso da kulolin snacks iri iri da juice dakinsu yaya yusif yasha gyara aka shimfida katuwar dadduma Aisha kuwa barin gidan ma tayi gabadaya . Dady yacika alkawari ya dangana ga iyayen Aisha anyi barkwanci musamman ga alhj aminu to duk yadda dady yayi tunaninsu sai yatarar basu kai haka ba ,sai dai karfin hali da rufin asirin ubangiji Amman ta ko ina bbu, sai dai yaji dadin ganin mahaifin Aisha dagani zai Yi datako shidai mlm abu zaune yake yana bin alhaji ishaq da kallo tsabar kamamani dayake hangowa a fuskarsa tayi masa kama da wata fuskar a haka akayi abunda za'a Yi dady ya tambayar ma dansa kuma Mafi soyuwa acikin yayansa auren Aisha alhj Aminu ne yaba da Aishar ga Abdullah cikin murna da farin ciki suka rabu . Bayan dady yadawo Abdullah zaune agaban mahaifinsa yayi shiru yana jiran daga dadynsa yaji mai zaice dangane da zuwansa dan gabadaya baya cikin natsuwarsa burinsa Bai wuce yaji mai dady zai ce ba . Dady ya yadan Nisa sannan yadago Ido yana kallon Abdullah sosai yaron nasa ke bashi tausayi ganin yadda soyayya tamai dashi cikin kankanin lokacin, wajen yadauki shiru zuwa na wani lokaci sannan dady ya iya Kiran sunanshi Abdullah ya dago yana duban dady ,dady yace Abdullah Aisha dai tayi Maka ko ? ya sunkuyar da kansa kasa yanajin yadda gumi ke bin jikinsa dady yasake numfasawa ya girgiza kai yace shikenan yanzu a yadda nike ganin a aika musu da dukiyar aure da duk wani abinda ya kamata Amman abari sai zuwa hutun karshen shekara sai ayi bikin ta yadda zaka samu hutun ka gabadaya . Abdullah yajin jina kai dady yacigaba sannan yace akwai bukatar a sai musu gida babba mai wadatar guri musamman saboda taron daurin auri sai mota Hawa ina ganin biyu ko uku zata musu sai maaikatan da zasu taimaka musu da gyara koina ,Abdullah ya dago idanunshi yana wa dady kallon murna yana sakewa dady godiya. dady ya girgiza kai yana lumshe idanunshi shi awajen sa Abdullah ya cancanci fiyye da komai agunsa domin Samar masa farinciki. Tun safiyar ranar litinin dady yasamu sakon da yake Jira daga South Korea suna neman su domin yin interview anan reshen su dake Denmark dan haka dady yasa hannu akan Abdullah ne zaiyi tafiyar wayewar garin talata kennan zai bi jirgin Lagos domin ta Lagos zai zasu tashi , yakasance Abdullah cikin uzuri yake har gurin magriba da Kyar ya samu bayan sallar ishai ya tafi gurin Aisha shi da salis yaya yusif ne ya fito yake masa baya ai tana can gidan aunty Maryam Abdullah ya duba agogon sa yana da sauran lokacin ,yayi sallama da Yaya yusif suka wuce. Tun yamma taje gidan aunty Maryam ita kuma tarike ta sai ta kwana dan haka sallar ishai kadai tayi ta nade a gado har ta fara bacci Aunty Maryam ta taba ta taje inji Abdullah ta Mike tana kallon aunty Maryam sannan ta dubi agogo tara saura kwata sannan ta Mike a hankali ta canza kayan jikinta . Da sallama tashiga falon bakin yana tsaye daidai kofar da zata sadashi da ita hannayensa rungume a kirjinsa ya langwabar da kai a jikin bango ,bata ji amsawar tasa ba Amman ta lura da yanayin kallon da yake binta dashi ta dauke idanunta dan tarigada tasaba da wannan mayataccen kallon nasa a hankali yazo daf da ita ya zauna suka hada Ido ya gane har tafara bacci ,ya lumshe idanunshi yana mai tabbatar wa kansa muddin yasameta zai ji dadin rayuwa da ita ya fada a kasan ransa komai nata bata cika daukarsa me wuya ba , hasalima ita ba komai yada meta ba,duka Bai fi rabin awa da mintina da idar da sallar ishai ba Amman har tayi bacci takan sauka kawa rayuwar ta akan abubuwa da dama ,hakan yasa take sake shiga ransa Sosai da sosai , yanayin kallon yake mata yasa kirjinta yarinka bugawa , Abdullah yakira sunanta yace Aisha I love you ,I really love you please tell me do you love me? ........ MMN SUDAIS CE [3/12, 3:01 PM] Kaunace Sila: 💗💗💗💗💗 ZUCIYAR MASOYI 💖💖💖 💗💗💗💗💗 AISHA A BAGUDO Page13 Tayi shr batace komai,tashiga wani yanayi na daban, tarasa gane kanta meke shinrin farawa da rayuwata ta furta haka acikin ranta , Abdullah nasan ruguzamata zuciya da wayan nan idanun nashi masu frigita ta ZUCIYAR duk wanda aka kalla dasu, ta takasa amincewa da farinciki take ciki ko tashin hankali a lokacin guda km taji kamar ta tambaye shi ko zai iya amsa mata tambayoyin da suke cunkushe akasan ranta masu neman tarwatsa mata zuciya da tsantsar jiki "da idanu take binsa da kallo tanason taganu ko shima yashiga makamancin halin datake ciki " shima ita yake kallo ,yayi murmushin daman yasan bazata iya furta Kalmar daya nema daga gunta ba " , acikin zuciyarsa ya furta" OH" ni Abdullah tawa tasamini nashiga one chance , ya zuba mata manya idanunshi yace gobe zanyi tafiya ta

Table of Contents

Chapters

62 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62