Chapter 36
Chapter 36
zagin faiza hade da tsine mata a zuciyata ,daman wannan sirrin da za'a yi yanzu shine wanda zai karkato musu da hankalinsa domin duk wadancan da suka zo da su na da ,sun tashi daga aiki wa'adin su yakare tunda ba su aiwatar da su ba a lokacin da ake so sai gashi yau din ma abun yana neman fin karfin su domin dai bbu yadda mama hafsa zatayi hatta abinci ma a gaban mami yaci ai kuwa faiza ta sha zagi iri iri gurin mama hafsa sai dare suka dawo dan daga inda suka je ma wani gurin nufa..... Abdullah yayi matukar mamakin yadda ya tarar da mami ba tare da wata damuwa ba har ishai suna tare da dady sannan ya umarce shi da yaje ya huta shikam ba haba ya so ba ... Sai a wannan daren ne dady ya zubewa mami katunan daurin auren a gabanta kuma yake sanar da ita yace kada ma tasamu damuwa duk inda take tunanin zata aika shi tunin ya riga ya aika yana tunanin ma wajen gobe wasu zasu fara wuntsulowa gidan .. Da farko dai mami bata fahimcesa Sosai ba sai daga baya ta kalli dady tamkar zatayi kuka tace daman abinda kuka shirya min kennan kai da danka dady yace bbu ruwan Abdullah ciki shima yadda kika tsinci maganar haka yaji ta.. mami tayi shr tasan wata fuskar tafi gaban mari".banda haka wlh da baza ta yarda da wannan auren ba komai zai faru , dan yanzu ta soma tunanin da wuya in dady yasan ko wacce yarinyar "da Abdullah zai aura" ta sauke naunauyen hadiyar zuciya sannan tace yanzu ko Abdullah ba jinina bane ya dace ace sai yau za'a sanar da ni yinin gobe da jibi ,gata kuma daurin aurensa maganar taso hassala dady dan duk abunda ta shuka agidan yaruwarsa yasane yashare bashi da niyyar tunkararta da maganar Amman tana neman harzuka shi dan haka shima cikin zafi da kausasa harshensa yace bayan kin dauki zafi da yarona in ma ansanar miki me zakiyi? baya ki damawa mutane lissafi sannan yadan sausauta murya ya shiga gaya mata yadda sukayi da doctor jack mami ta numfasa dan jin bai sako wani zance can ba, tace yanzu idan Abdullah yaro ne bai hango ma kansa abinda aka hango masa ba kai ba zaka hango masa ba irin gidan da Abdullah yadace ya nemi aure kennan tana kallon cikin idon dady, duk da a tsorace take . maganar sakamakon kallon dataga yana jifan dashi ... Dady yace uhmm anzo gurin ....da hanshi ya dakarta daita...... daka malama banason shirme da shashanci "kar fa kidauka bansa komai ba , alhalin ina sa ne da abunda nike kawai dai ina raga miki sanadin abubuwa dayawa Amman na lura baki san da hakan ba ,ok diyar yaruwarta wa ce bata dace da dana ba, sai ta hafsa yarwarki ko? jikin mami ya dauki rawa taso ma inda inda aa..Aa..ni fa ba haka nake nufi ba ok ya kike nufi" fahimtar dani ina son sani hankali yayi matuka tashi". shikenan abunda take gudu ya afku ya zuba mata Ido alamun ita yake Jira .. ... MMN SUDAIS CE [3/12, 3:01 PM] Kaunace Sila: 💗💗💗💗💗 ZUCIYAR MASOYI 💖💖💖 💗💗💗💗💗 AISHA A BAGUDO Page 22 Dady Ya sausauta murya yace haba mamin Abdullah wai me wayan nan bayin Allah suka Yi miki kodan sun kasance su bawasu bane ? Hanjin cikin su ne kawai ba a caje ba "Amman komai nasu sai da aka bincika Amman ajiye yan'uwantaka kina tsammanin kai tsaye zan bar Abdullah ya nemi aure ai ance sai kayi kuskure a filin yaki ka tsira Amman idan kayi kuskure gurin neman aure ka fadi mami ta numfasa to me yasa sanda na kawo maka zance faiza baka Kuma bi takai ba me yasa ita ma ba'a bincika an ga nagarta ta ba" saboda ita ba family dinka bace ..Dady yayi murmushin a zuciyarsa su fa mata duka sunansu daya ,a fili yace Abdullah fa ba yaro bane yasan ciwon kansa. experience dinsa ya wuce ace za ai masa wani zabi sabanin son zuciyarsa yana da kyau kiyi masa uziri a matsayinsa na da namiji.ita fa wannan yarinyar na bincike ta tun bansa wacce ba dan ki ajiye duk wata dangantaka abinda Abdullah ya nuna yanaso shine farincikina "har karfe daya na dare dady da mami ba su runtsa ba duk akan maganar Abdullah ,domin taji zafi abinda akamata sosai ganinta ammata fin karfi ne kawai shi da kan sa dady yasan ammata laifin rashin sanar daita zance auren tun farko shiyasa ya dinga lallashinta saboda Abdullah din dai daga jikinta ya fito dan haka akwai ciwon sa a tare da ita, Amman in bayan haka me yuwa sai daita hangi Abdullah da ya'yansa suna shigowa gidan..... Washegari da safe tun kafin isowarsa part din mami ya hangi faiza kan barandar su teemah ta xuba masa Ido gabadaya yaji ransa yayi mugun baci dan shi ya tsani irin kallon datake binsa dashi kamar ya juya ya koma haka ya ji" Amman ina matukar yana cikin gidan to dolensa duk safiya yasa mahsifiyarsa a Ido kafin ya fita ,ya fara ganin lafiyar ta ,ya karasa ya shiga falonta yayin da RK dake biye dashi ya ja ya tsaya a waje ...ita kadai ya samu a falon sai teemah dake table tana duba settling breakfast yadda ya karanci maminsa sai da ya razana daf da ita ya zauna bisa kafet yana gaishe ta mami ta dade tana kallonsa tamkar mai tunanin akan sa. sannan tace jibi jumma'a shine yakama za'a daura maka aure da wacce raayinka ya kwanta da ita " yadda ta fadi maganar sai da cikinsa ya kada dan tsabar fargaba yarasa meyasa maminsa ke kin Aisha bai san kiyayyar Aisha takai haka a gun mami ba sai yanzu dayake tsugunne gababta Kuma har abun yashafesa ..zai yi magana ta daga masa hannu ni ba magana nike so ba kaje kayi auren ni na yafe mata kai ita da uwarta sai su zame maka madadina. Gabadaya jikinsa ya dauki zafi ji yayi tamkar an zuba masa ruwan zafi " idansa ya firfito waje yace dan Allah mami kiyi hakuri indai akan Aisha ne zaki yafeni na hakura da ita na dade da cewa ki aura min duk wacce kike so tun kafin haduwata da Aisha ... Mama hafsa ce ta fito ta zauna akan kujera" Abdullah yacigaba da yiwa mami magiya da ban hakuri Amman mami ko gezau zuciyarta take raunana ita dai kawai son take abar mata danta ta zaba masa wacce ta kwanta mata arai "anan mama hafsa ta fara fahimtar abinda ke faruwa ta shiga tambayar mami AV kawai ta janyo ta Mika mata jikin mama hafsa har bari yake tana karantawa dole ka iya kiran mama hafsa da cewar ta makance a gurin dan batasan sanda ta zura wata uwar ashar ba wanda gabadaya gurin aka zuba mata Ido Kuma har kallon da ake mata bai sa ta farko daga makantar wucin gadin data same ta ba .ta shiga kwallawa faiza kira ,faiza wacce tuni ta sauko ta labe a kofar dake daf da falon ta karaso inda mama hafsa ke zaune kmr an dasa ta ta Mika
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62