Chapter 28
Chapter 28
dashi domin can ne kadai dady yake ganin zasufi duba masa Abdullah dinsa da karayar daaka ce yayi ,,, har daren ranar yana tare da Abdullah Amman bai farfado ba Mami ma takasa hakuri sai da taganta asibiti su duka ,sanin idan suka wuce da Abdullah damuwa zatasa mami ita ma kamuwa da wata cutar yasa dady ya shirya visa har da ita washegari ranar da safe suka bar Nigeria yayin da akabar su teema a gida ..... Koda mlm yashigo Aisha na tare da inna ta Mike shi kuma mlm abu ya zauna yana wa innarsu bayanin zuwan Abdullah da maganar da suka tsayar kan gobe za'a mai da musu da komai nasu na aure inna tayi shiru tayi tagumi da hannuta daya yayin idanunta ke kan mlm abu tashiga matukar tashin hankali wai Abdullah dan dan uwanta kennan danta ne halak malak ita ko yaushe zata bari a ayi auren nan gara dai ayi hakuri da abun kawai "wata zuciyar tace to in kuma wani abu yasame shi tasadin haka tasan dole zai shafe dan uwanta ita kuma batasan ganin tashin hankalinsa,alahakikanin gaskiya ita me son yanuwa ce balle shi kadai gareta duk da bai damu da ita ba tasake Jin sukar wani wasu hawayen da duka fi na dazu ciwo"" Amman takan mai uziri saboda rashin bai dace da macen kwarai ba, mlm abu ya jijjiga kai yace narasa gane kan ki tun zuwan iyayen Abdullah gidan nan ,kinki sanar dani damuwarki. munsaba raba farincikinmu tare haka ma akasin haka to meyasa zaki boye ?"duk da cikin duhu ne hakan bai hanasa ganin hawayen dake bin fuskarta ba, sannan cikin yin kasa da murya dan batason Aisha tajo mai zata ce dan tasan idanunta ta biyu " nan dai inna tayiwa mlm bayanin komai tun daga zuwan ta gidan alhj ishaq din bayan wani zuwa da sukayi ka'oje , mlm abu shima yashiga rudani matukar maganar ta jijjiga sa kwarai kasa cewa komai yayi sai ma shigewa daki da yayi yana mamaki da alajabi wannan hadin sai yanzu ya iya cewa ikon Allah kennan .... Tun bayan shigowar mlm abu da kmr awa daya har yanzu idanunta biyu hakan nan duk da tana kwance bata da wani cikakken kuzari ajikinta tun byn faruwar abun har zuwa yanzu takasa raba kanta da dogon tunani ,komai akan idonta da kunneta aka fara aka gama dan haka duk wani tashin hankali da iyayenta suka shiga sai dai ta bawa wani labari "abin yaki wuce mata arai ko dai dai da second daya zubar hawayen inna a dalilin aurenta ,wanda tun randa tazo duniya bata taba ganin ba ,ta yarda idan tashin hankali yayi yawa hawaye ma basa zuwa dan haka ta gwammace da ma kukan tai tayi da abunda ke damunta a zuciya,ita daman tun zuwan Abdullah gurinta ta gane wani karan tsaye ne a rayuwarta duk wannan maseefar da yawan tunane tunanen da take Yi bai hana bacci lallaba idonta ba ya fige ta na mintina uku ....wata mumunar faduwar gaba ce ta farkar da ita ta Mike zaune ta dafe kirjinta hade da mai da numfashi sama sama gabadaya jikinta rawa yake Amman duk da haka gabanta bai dai na harbawa ba "a hankali ta dinga karonto innalillahi wainna ilaihi rajiun...ta jima tana maimaita wa sannan ta dan samu sauki da natsuwar zuciya. iya tunaninta batasan me yasa gabanta yayi irin wannan faduwar ba , haka nan jikinta baya bata wani abu na shirin faruwa da ita tunda bbu wanda tayiwa laifi sai dai ko daga Allah ne tashi tayi ta fito a hankali ta dau buta tayi alwala taxo ta shimfida pray,mat tafara nafila.... Duk motsinta akan idon innarta ne ,tana Jin tausayinta dan tasa damuwa sosai aranta ,har ramewa tayi inna tasawa ranta hakuri da dangana dan ko ba komai Abdullah bata ba yadda zatayi kallon da inna take wa Aisha yanzu yasake sawa ranta kiyyayar maza fiyye da da dama can tana kukan targade sai ga Karaya.... . aunty Maryam takan aiko Aisha taje Amman da ta lura idan taje tana yawan mata zance Abdullah sai ta daina zuwa ko ta aiko saboda ita yanzu haka kawai taji ko sunanshi bata kaunar a ambata a gabanta .... Su mlm abu basu samu damar zuwa gidan alhj ishaq ba a washegari da Abdullah yazo kmr yadda mlm abu ya shedawa Abdullah sai bayan sati daya saboda zuwan da mlm dahiru zai yi daga ka'oje ... Tun a get din gidan abin yasake kwancewa mlm dahiru kai yayinda mlm abu yake sakawa ransa yanzu duk wannan tambatse tsen gidan na yayar matarsa ne Killa daman can wata manufa da yaudara ce akazo neman diyarsa dashi .... masu gadi suka tare su ko ciki ba'abarsu sun leka ba bare su hangi cikin gidan byn gaisuwa mlm dahiru yayi bayanin suzo neman mai gidan ne , to Amman tun daga yanayi kallon da masu gadi suka yi musu Jin cewa me gidan gabadaya da kansa suka zo gani suka sha jinin jikinsu bbu wani cikakken bayani da masu gadi suka musu daya daga ciki yace to kujira zaku ganshi sannan yayi shigewarsa ya rufo get dayan ne ma yamusu bayanin yace gaskiya zan sanar daku ba'a zuwa ganin me gida kai tsaye sai tare da wata sheida ,ko da shidar ma sai anyi waya an sanar da mu in yaso idan kunzo sai musanar aciki ,a halin yanzu da ake ciki mai gidan baya ma kasar sabida haka dan Allah kuyi hakuri ku canza wani bangaren .... Su mlm abu sukayi masa godiya suka wuce kowane zuciyarsa da abin da take sakawa... Magana dai akan bbu me sake taka gidan ,ko ba dade dai sun zo neman kayan aurensu sai dai idan suka ji shirun yayi yawa ,abida mlm dahiru ya yanke kennan duk da mlm abu bai sanar masa da kowaye mahaifin Abdullah ba yafi son sai komai ya warware tukun .... To shima dai alhj aminu a dawowar dayayi ya riske yadda al'amarin yakasance mamaki ne yacika shi,shi kam cewa yayi kada abiyewa al'amarin mata kawai ajira daga uban yaro dan ko ba dade zai waiwaye su ......... Manage please may be ku sake jina anjima MMN SUDAIS CE [3/12, 3:01 PM] Kaunace Sila: 💗💗💗💗💗 ZUCIYAR MASOYI 💖💖💖 💗💗💗💗💗 AISHA A BAGUDO Page 17 Likitoci sun rufa akan Abdullah tun saukar su Germany,hankalin dady na matukar tashin idan yakalli Abdullah da halin da yake ciki shi kadai Allah yabashi da namiji Amman ya fanshe masa abinda ya'ya zama goma zasu Yi ,Allah ya albarce shi da tarin dukiyar da shi kansa bai zai iya cewa ga iya kacinta ba, wanda a kalla da yana wasu ya'ya ashirin maza to kowannesu akwai bangaren da zai kama" yana sane da maganganun da mutane ke masa Amman sai yayi kmr bai sani ba "domin dai fuskarsa ce kadai akan abin sai kuma yanzu da Allah ya taso masa da Abdullah ko kadan ba raayinsa bane ya daura mace akan wani part na dukiya ,burinsa kawai ya basu illimi ya aurar dasu ,dan haka ko a daren da akawa Abdullah aiki a kafadarsa,ko kadan alhaji ishaq bai runtsa ba. neman tsarkaken guri yasamu yayi sallah nafila ..sai da aka fara kiraye
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62