Skip to content

Chapter 40

Chapter 40

Zuciyar Masoyi Book One Complete Hausa Novels 1 1,190 words 0 views Progress saved
Download Book

dan haka tacigaba da Jira ga sauro sai cizo suke sun samu nama" jiya tayi kwanan ha'ulai a kofar gidan boka mai gani har hanji gashi yau ma zata sake kwanan gidan sauro. baya da kugunta duk sun rike mata sai da takai ga zaman dirshan a wajen iya tashin hankali faiza ta ganshi agun dan har kwarika suka dinga bin jikinta ga bacci a idonta Amman dan jaraba da kafiyar irin nata ko gezau balle ta bar gun ita dai sai burinta ya cika " har sanda akafara kiraye kirayen sallah a wasu masallatai dake kusa da su tun tana karyata kunneta har taji a masallaci dake cikin gidan duk ilahirin ruwan jikinta ya kusa tsotsewa bata amincewa ranta ba har sanda taga kofar part din dady an bude dady ne da Abdullah suka fito a tare da alamun masallaci zasu je dan ca suka nufa nan duniya mutumin dake cikawa faiza Ido Kuma yake balain yimata kwarjini irin dady. Ban cin haka ai da tunin tayi gudu ta Tari Abdullah a wannan lokacin duk da tasan kaidar da boka ya gaya mata Amman tasan muddin ta doshi Abdullah a wannan lokacin tasan daga ita har mama hafsa kashinsu ya bushe dan sai anyi tambari da gabadayansu anyi sama da su .. Tun karfe bakwai Dr sagir ya iso gidan, dady ya turo da kayan da Abdullah zai sa hum maikaratu ba sai an tsaya kwatanta tsaruwarsu ba, tun safe kuwa manya manya da kusoshin gwanatin duniya suke cincirindo a gidan har police aka sanya sannan akabar Abdullah ya fito ya shiga motar zuwa gidan alhaji aminu kai daga kallon shigar manya kayan da Abdullah yayi kasan dole ce kawai tasa shi sanya su don hatta leben babbar riga a hannun salis take shi kuwa da kyar yake iya daga dayar ya mai da kan kafadarsa ... Hummmm ga dai Abdullah zaije gun daurin auren to jama'a ko ya auren zai kasance , to kudai biyo Yar mutan bagudo kusha labari🀝🀝😜😜 MMN SUDAIS CE [3/12, 3:01 PM] Kaunace Sila: πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’— ZUCIYAR MASOYI πŸ’–πŸ’–πŸ’– πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’— AISHA A BAGUDO Page 25 Aisha zaune a dakinta ta hada kai da gwiwa sai sharban kuka take duk da tun satin da'aka soma shirin bikin, take cikin halin tashin hankali, rashin sanin meyye makomarta agidan su Abdullah" tun safe datayi wanka wanda shima sai da gwaggonta ta sata a gaba sannan tayi ko byn da yashirya ma zaman tayi tasoma rizgar kuka tamkar wacce akace wa Allah yayiwa mlm abu da inna rasuwa "tun karfe bakwai daidai salis ke kofar gidan mlm abu yana jiran fitowarta Amman shr" kusan tsayuwar minti 30 yayi awajen bbu wani bayani dangane da fitowarta " can kuwa cikin gida ba yadda ba'ayi da Aisha ta fita ba, Amman taki sauraron kowa dan gani take kowa bai damu da halin zata shiga a sabuwar rayuwarta " gwaggo Laure ce tasake shigowa dakin tace kun ganarmin jairar yarinya mai daurin kan tsiya ke dai Allah shirye ki yashige miki gaba, dan wannan halin naki wata rana sai yakai ki yabaro mutun arinka yi masa magana sai dan bazan taurinka awa mutane farko " Aisha tasake barkewa da sabon kuka.kar all yasa ki fita kiyi tazama daurin aure ne dai ba fashi sai dai ki mutu,inna dake daki tare da baki tarinkajin motsawar zuciyarta ita ta fuskanci abinda diyarta ta keso "tashi tayi tsam tashiga dakin. yadda taganta sai da taji gabanta ya fadi hankalinta a tashe ta karasa inda diyarta ke zaune ta yakamo hannunta hade da kiran sunanta Aisha ta dago hawaye nabin fuskarta ai tana ganin inna ta fada jikinta ta fashe da wani kuka inna ta daura hannu a bayanta tana shashafawa ahankali har dai taji kukan nata ya dan tsaya "sannan ta dagota ta mai da ita mazaunin ta ido cikin ido inna ke kallon Aisha" murya a dashe tasake kira sunnanta Aisha kina son ki tozartani acikin jama'a gidan salon asamu masu cewa uwarki bata baki tarbiyar kwarai ba ? Aisha ta girgiza kai to meye dalilin rashin fita akai ki inda za'a daura miki aure" byn yau ranar farinciki ce garemu baki daya , ga mutun can waje tun sanyi safeya yake zaman jiranki dan tsabar wulakancin Kiki fita idan Abdullah ne baki so shi mayye laifinsa ciki "ai kifito kai tsaye ki nunamin ban isa dake ba. tunda ni na saki amincewa auren Abdullah bawani ba. cikin sarkewar murya tace wlh inna ba haka bane " ni dai haka kawai nake jin tsoro gashi ina yawan ji faduwar gaba" inna tayi shr dan itama kusan tun karatowar auren take jin haka Inna ta numfasa sannan tace to maza share hawayen nan bana bukatar ganin su" da bayan hannu tashiga gogewa inna tace addu'a zaki rinkayi a duk sanda kikaji haka ..bbu abunda yafi karfin addu'a "sai da inna tayi ta rarrashinta wanda daman abinda Aishar ke bukata kennan daga innarta "inna da kanta ta sake gyara diyarta "ta rakata har tsoron gidan sannan suka fita tare da yan rakiyyarta . Takwas ga watan uku ranar lahadi kennan misalin goma da minti biyar ,dubban jama'a suka shaida auren Abdullah I.M sidi magaji da Aisha abubakar bahindi domin sai da aka shafa fatiha da kusan mintina goma sannan shafarwa ta iso gurin wasu a dalilin cunkoson jama'a" don titi unguwar gabadaya police ne zagaye da gun .. Babban abinda ya tsuma ZUCIYAR jama'a wanda ya hana mutane saurin watsewa an daura auren yarinyar akan sadaki naira dubu hamsi wanda kudin abin a rike baki ne sosai a wannan lokacin tare da takardun gidaje gudu biyu hadi da motocin hawa guda biyar wanda alkawarin dady kennan "dan ka'idodin mlm abu yasa yamasa haka "saboda kwanakin abaya yaje har gida yawa mlm abu datayin gida ,su tashi dag gidan dasuke ga gida can yaba su. Amman fir mlm abu yace shi dai ya gode Amman yafi son nashi ,domin dashi yasaba dady yasan yanzu dole ya amshe su a matsayin sadakin diyarsa abinda ya ruda zuciyar mutane kennan .. Dady na cikin jama'a ana gaisawa cikin fara'a gashi yanata nan nan da mlm abu "musamman alhj aminu domin har sun saba shima mlm abu rashin sakin jiki ne da basu yi ba, an dauki lokacin kafin a fara watsewa sai da mutane suka ragu sosai sannan Dr sagir suka taso shi da ango suka dinga gaisawa da jama'a da likitoci abokan Dr sagir shi Kuma yana masa bayanin su.. Abdullah ya tsaya yana kallon kofar gidan alhj aminu yace salis yakawota nan din ne?Dr sagir yayi dariya yace wa kennan Abdullah ya dan Harare shi cikin dariya yace to amaryarta Dr sagir yasake darawa tun safe ya kawota tana ciki Abdullah ya ja ya tsaya Dr sagir yace ya ko amana magana da ita ne? Ahankali Abdullah yace kai dai bom....ne wlh 'wane ni yanzu kana jin tun satin bikin nan take kuka bare yau nasan duk fushin da haushinta a kaina za'a juye ..suka sa dariya , Abdullah ya dafe kirjinsa yace washi.... da sauri Dr sagir yace kai lafiya , Abdullah ya runtse Ido jikina ya nuna min kadarata ta cikin gida nan, tacan tana kuka,dr sagir ya ja tsaki wlh ka tsorata ni sauran

Table of Contents

Chapters

62 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62