Skip to content

Chapter 10

Chapter 10

Zuciyar Masoyi Book One Complete Hausa Novels 1 1,205 words 0 views Progress saved
Download Book

tayi alwala sai ga yaya Ali ya dawo Niki Niki da kaya ya zube yasake fita yashigo da wasu kwali guda uku ya kalli Aisha yace gashi nan wai Kuma ana miki sannu da shan ruwa ,ya fice abun sa cikin mamaki ta bishi da kallo to yaya Ali ne bbu fuskar, da ta dakatar dashi ta tambaye shi bata taba komai ba har sanda inna ta sanya aka kwashe kayan daga gurin mamaki bai gama sakin ta ba har zuwa byn sallah ishai ta fito wanka kennan mlm abu yashigo daga waje yace taje tayi bako . Cikin tsoron ya mamaye ranta kmr ta daura hannu akanta ta kurma ihu haka takeji haka ta shirya cikin sanyi jikin ta fita. Sanye yake cikin kananan kaya masu duhu colour din da suka sake fidda kyaunsa a fili ga jar fatar sai sheki take , tun fitowarta ya zuba mata idanunshi daman Kuma kofar gidan yake kallo har ta karaso garesa ta tsaya bai dauke idanunshi daga kanta ba yanajin yadda zuciyarsa ke tsalle kmr zata fasa kirjinsa ta fita lumshe sexin eyes din shi yayi sannan ya bude su fas akanta ta sunkuyar da kai kasa tana wasa da yatsun hannuta shima dai shr yayi yana sake kallonta San ransa,shiru yabskunci wajen na wani lokacin can dai cikin tsoro tace ina.....wu...ni yayi murmushin karfin hali ya bude baki ya amsa mata ,sannan yace Aisha kinyi kokari yin azumi yau ga rana banda kince indawo yanzu da zan barki kin huta ya sake kallonta tamkar wanda yake son ya dauke mata gajir azumin da tayi sannan yace wani abu ne a zuciyarta yakasa hakuri dole sai yazo yaga yadda kika Sha ruwa usman yace akwance kike da fatan ba wani abu ke damunki ba ,sannan yayi shiru ,kiris yarage Aisha tasa kuka shikenan dama tasan akwai shirin da usman yazo ya kulla mata tun dazu jikinta ke bata ,bata iya cewa komai ba illa har yanzu kanta nakasa taki yarda su hada ido dashi Abdullah ya zuba mata idanunshi ,da gani zatayi tsadar magana ,ya furta haka cikin ransa yakira sunanta cikin sanyi Aisha I you ok , ahankali ta daga masa kai ya koma lip's din shi na kasa yasoma cizawa ahankali........ MMN SUDAIS CE [3/12, 3:01 PM] Kaunace Sila: 💗💗💗💗💗 ZUCIYAR MASOYI 💖💖💖 💗💗💗💗💗 AISHA A BAGUDO Page 6 Tsaye take turus sai hawayen dake bin fuskarta bata san har yanzu yanan ba kawai sai taji badadi ko kadan ba nufinta tayi haka agaban shi ba ,bugu da Kari Abdullah ya girmewa babnan yayanta yusif dan sai taji tamkar tayi raini ga babba. Cikin Yan mitina da suka wuce da faruwar haka ta tsinkayo maganar babanta subuhanallahi waye yayi barin kaya anan "ya turo kofar tare da Kiran sunanta Aisha ta fito daga kicin , babanta yaci gaba da tambayar ta ,karaf hadiza tace kayan wani ne Abdullah yace yaya Aisha taje wai dan taki zuwa shi kuma yaki tafiya ya tsaya a tsoro an watsa masa kayan nasa yana gani ya tafi ya manta bai diba ba.cikin mamaki mlm abu yace waye ya watsa masa kayan?hadiza tace yaya Aisha mana "cikin murya mai nuna tsantsar bacin rai mlm abu ya dubi Aisha yace yayi kyau da abinda kikayi ina son da hannuki ki koma ki kwashe kayan da kika watsar .yashiga daki ,zuwa jimawa ya fito da abin sallah a hannusa bai sake ce mata komai ba ya fita ransa a bace "tabbas ta manta yau jama'a babanta yana dawowa Sha daya zuwa Shabiyu"ya sake fita saboda masallaci banda haka da tuni ta kwashe kayan kafin yazo,dan haka gabadaya a tsorace take ganin yadda ran baba yake a bace ,tun hadiza bata kai haka take son yarinyar saboda surutunta yana bata dariya ,anan makotansu take,gashi yau surutun hadiza bai Yi mata rana b.tun bayan saukowa daga masallaci yake daki bai fito koina ba ,haka nan salis ma cewa yayi yaje har sai ya nemeshi ,yasan Daddy ma bazai bukace shi a yanzu ba don haka ya kashe duka wayoyinsa hakan yabashi daman tariyo abinda da yafaru a dazu ,me sanya Aisha zata yiwa soyayyrshi mummunan fahimta ,shi da kansa ya amincewa kansa tun ranar da idanunshi suka fara ganinta har zuwa yau bai taba koda kallon dan yatsanta yaba sha'awa irin wacce ita Aisha ke nufi ba,sai dai ya kalla bashi Sha'awa irin ta birgewa wanda so ne kadai ke kawa haka Kuma koda ya aiyana wani abu da ita yakan kaddara wa sai sunyi aure , to Amman duk ya gane abunda take nufi da shi yana tattare da rashin son take masa"ya runtse idanunshi gam yanajin wani radadi na ratsa ilahirin jikinsa tare da fadin dole in hakura dake Aisha tunda da gaske kike bakya Dona,cigaba sonki zai sa in cutar da zuciyarki sannan ya bude idanunshi da suka gama rikedewa suka koma ja "Amman zan samu Dr sagir .wayar landline dake bedside dinshi ita ta katse daga duniyar tunani yana dagawa muryar teema ce ke cewa bros mami tace ko kana nan ,an Yi checking dinka a handset baa sameka ba . yace na dan kwanta ne tana son ganina ne yanzu?teema ta amsa da Eh yace OK am coming duk da yanayin sanyin garin ,sanye yake cikin karamar riga baka da kadan hannuta ta sauko kafadarsa hakan nan takama jikinsa sai bakin wando jeans shigar ta kara fiddo masa da sigarsa ta cikakken "da" namiji gashin kan nan sa ya kwanta luf kmr koda yaushe saboda gyaran dayake samu akai akai" cikin takun nan nasa mai birge duk wanda yakallesa Abdullah yashiga part din maminsa ,a falo ya sameta tare da kannesa sai bakuwar dayaga sunyi " yasamu waje ya zauna tare da daukar remot control yafara dadfanawa minal ce taajiye masa farfesun hanta da apply juice wanda mami da kanta tayi masa ,ta matso masa da stool gabansa ta zuba masa sannan suka fita dama unguwa za'a kaisu mami ta kalleshi ta jiho masa tambaya halan wani abu ke damunka yadan kalli mami kadan yace noting na dai gaji ne , bakuwar ta matso ta gaisheshi ya amsa batare da ya kalli inda take ba" mami tayi murmushi tace faiza kennan daga sokoto tun wajen daya ta sauka"Abdullah ya dan yadan kalli faiza ta kasan idanunshi"Wanda ita tun shigowarsa ta kafa masa ido , ya tabe baki ya mai da kansa gafe shi sai yanzu ya gane kallon da take masa tun shigowarsa ,wato itace mami ke son ya aura diyar mama hafsa ,a kalla zata girmewa teema haka kawai yaji bai son yawan kallon datake binsa dashi yaji duk yatsani wajen cikin shagwaba wanda shi bai ma San yanayi ba yace mami ina son inje in ga Dr sagir ,ya fada tare da duba agogon farin gold dake hannushi .namu tace to baka ci abinda aka kawo maka yadan can ciza lip's dinshi yace bazan iya ci ba kuyi dinner da ni aransa yace yaushe zan iya cin wani abu bayan akafe ni da mugun kallo mami tace mekaci ya lashi basasun lebensa yace coffee tace coffee ba abinci bane ok mami indawo zanci yafadi haka tare da Mikewa yayin da faiza ta bishi da Ido tamkar kura taga nama ita duk

Table of Contents

Chapters

62 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62