Chapter 18
Chapter 18
haka faiza taso ba taso abarta daga ita sai shi a mota, sai da suka shiga mota ita da amina sannan ya fito daga part dinsa da waya a kunne yana magana .faiza ta zuba masa Ido sosai ita dai kamar ita kadai take ganin kullun gari yawaye sai yakara kyau da kwarjini fiyye da ko yaushe Yar rashin kibar da bai daita, yasa kowace shiga yayi take masa kyau " sanye yake cikin kananan kaya masu colour ja da baki sai farin glass daya manna a idonsa yakaraso jikin motar tare cire wayar sannan ya kashe salis ne ya bude masa dayar mota yashiga ya rufe yashiga ya tuka yayinda musa ya tuka su faiza suka biyo bayan su gabadaya ranta ya gama baci ita da taso Abdullah din ne ya tuka su daga ita sai shi "sai gashi kusan mutun hudu akan uzirinta daman ita sam jininta bai hadu dana salis ba saboda yadda taga yana kaf-kaf da Abdullah din duk inda yasa kafa yana binsa "shima Abdullah yaso yadda ni'imar garin tayi masa dade yakasance cikin nishadi da tarin farinciki Amman duk ransa a bace yake tun fitowarsa daya lura da mayataccen kallon da faiza ke masa Abdullah daga cikin mota ya zubawa waje Ido ai ko idanunshi yayi arba da wasu dattijai guda biyu suka shige su yace salis stop the car . Salis yayi gaba ya daidaita yayi parking ganin su tsaya ne yasa musa tsayawa Abdullah ya murda kofar ya fito ya karasa inda suke yana cewa musa suyi gaba kafin su karaso salis yakaraso da wata jaka ya mikawa faiza ya koma mota yayin da Abdullah ya dubi dattijain, har suka kure faiza na waigensa tana mamaki musamman da taga bai koma mota ba yacigaba da tafiya . Abdullah ya riske mlm abu da abokinsa bbu wani abu da ya Dame su ,suna tafe suna hira kamar daga sama mlm abu yaga Abdullah yakasa boye mamakinsa yana dariya Abdullah shima murmushin kawai yake ya rusuna ya gaishe su sunan tsaye har salis yakaraso da mota da hanzari shima ya fito har kasa ya gaishe su Abdullah ya karbi kayan hannun mlm abu ya bude musu mota yace Bismillah.mlm abu yace ai munzo gida ma Abdullah yayi murmushin yace kuyi hakuri baba ku shiga mukarasa daku . A mota hira sosai tsakanin su har sanda aka sauke mlm dauda yayi godiya mlm abu yayi su sauke shi shima anan" suka ki har gida suka kai shi ,salis yayi parking a gefen titi sannan ya dauki ledar baban yayi gaba yayin da Abdullah da mlm abu suka Tako ahankali suna hira har zuwa kofar gida,mlm abu yace kadakata a kawo maka taka tsarabar nima ya'uri mukaje tun jiya . Abdullah yayi murmushin yana girgiza kai ni na gode baba. Aisha kuwa tun azahar taje gidan aunty Maryam ta karbo sako saboda gobe zasu tafi ka'oje aunty Maryam tabata kayan su saifu tace abawa kannen hadiza makotansu dan haka tana isowa kawai tashiga tabawa babarsu hadiza bata wani bata lokacin ba ta fito har tazo soro hadiza tabiyo ta ahankali tace yaya Aisha da daddare idan mamana tayi baccin nan nata zan dibo kayana in kawo miki da safe sai in zo kawai mutafi ko bata sani ba.bata tsaya jiran amsa ba ta ruga da gudu ta koma kan aikin da akasa ta"Aisha na dariya ta fito kawai idannuta suka sauka akan Abdullah shima yana dariya mlm abu yadage sai ya tsaya an bashi tsarabar sa. ba idanunsu ba hatta zuciyoyinsu sai da suka Yi clashing suka neman tarwatsewa" duk sai ta dabarbarce saboda da bazatan da Abdullah din yamata yayin da shi kuma ya xuba mata idanunshi yana jin yadda zuciyarsa ke dokawa idan har ba dan kamamnin gidan ba ba zaka taba cewa daga gidan mlm abu ta fito ba , sanye take da saukakken less mai design din apply ajikinta tayi masa kyau matuka fiyye da yadda take a baya , gaisuwar usman ce tasanya ya dauke idonsa akanta ,ta sunkuyar da kanta yayin da takasa motsawa tana jin yadda numfashinta ke barazanar barin gangar jikinta , zuciyarta tasoma aikin nata wato motsa kunjin halitta da Allah yayi mata ta tsinci kanta cikin wani yanayi da ba San ko menene ba"usman yashiga ciki gida yayin da salis yayi murmushi shima ya juya ya koma gurin mota , Abdullah yabishi da Ido ,bbu wanda yace uffan a tsakanin su haka Kuma bbu mai niyayar barin dan'uwansa , usman ne yasake fitowa soro, yashige dakinsu yaya yusif sai gashi ya fito da tsofafun kujeru guda biyu ya ajiye musu cikin soron ya fita , Aisha tabishi da kallo zuciyarta ke beating dum... dum ...dum..ba karamin karfin hali tayi ba wajen yiwa Abdullah nuni da yashiga ya zauna ta hanyar nuna masa da hannunta , Abdullah mai niyyar da sun kawo baba zasu bi bayan su faiza" Amman bai San meyasa ba sai ganin sa yayi akan kujera ahankali itama ta karasa ta zauna , shiru yabiyo baya har zuwa na wani lokacin bbu wanda ya iyayi magana cikin su"kowane yana gudun yin abunda zai taba ran dan'uwansa ,balle ita in ta tuna da maganar babanta akanta game da Abdullah " a boye take sauke hadiyar zuciya kasa kasa tayi magana cikin sanye murya ,kalma daya ya fahimta Kuma ya gane gaishe shi take Yi yaji dadin haka matuka har cikin ransa zuciyarsa tarinka kai kawo a tsakanin kirjinsa da Kyar ya iya tattaro duk wani kuzarin dake jikinshi yace Aisha how you doing "a motsen bakinta ya gane ta amsa ,yadan saki face dinsa kadan yayi murmushin so dai daya ne a rayuwa duk ma wani abu da tamasa ganinta a yau yasa yaji tamkar ya zube agabanta ya roketa ta so shi dan Allah kada tasake jefa shi a irin halin da tasashi abaya ya zuba mata idanunshi ji yake kmr ya fizgota gareshi "duk ta takura da kallon da yake mata ya ta rasa yadda zatayi sai ta dago idanunta sai taga har yanzu ita yake kallo , a kallon da yake mata yagane tashiga wani yanayi gashi kmr tana son Yi magana ya kira sunanta ahankali Aisha what do u want say,? Ta dago dara daran idanunta ta kalleshi cikin sanyi ..muryar na rawa tace kayi hakuri yace me akayi yana sake tsareta da idanunshi "murya kasa kasa tace abinda ya faru gabadaya ya gama kewayeta mata zuciya" dan bbu abunda takeji banda idanunshi dake yawo ajikinta wanda yasa har tasake dagowa ta kalleshi "tabashi tausayi Kuma ta birgeshi Kuma dada shiga ransa wani irin kallo yake mata shi kadai yasan yadda yake jinta a jinin jikinsa "yace wuce Aisha ke ma kiyi hakuri nashigo muku gida ba yadda tsari yace ba"yaci gaba da kallon yantsunta masu kusan kama da nashi wanda itama din su ta zubawa Ido "yace Aisha 21 days rabon da muga juna sai dai kin canzamin kin kara kyau . Aisha ta dan sace kallonsa kadan yayin da ya sakar mata murmushin har dimple point din shi na lotsawa " Har cikin ransa haka yagani yayin da ita Kuma taji haka a matsayi. Dadin baki ne kawai,a zuciyarsa yarinka karanto duk addu'a data zo masa game da samun
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62