Chapter 2
Chapter 2
dai gane Maza ne su uku biyu a gaba yayin da dayan yake biye da su ,sai da suka wuce sannan ta rufe sakina baya suka shiga mota direba ya hadu zuwa gidan biki . Doctor sagir ya bude office dinsa su ka shiga yayin da salis ya tsaya daga bakin kofar sagir yace bisimilla abdulla zauna ka Sha dan lemo ,wani fayal make son bincikawa yanzu zamu wuce har ya juya zai zauna yace please Dr cewa salis ya kirawo yaran da suka wuce yanzu abdulla ya fada . Dr sagir yadan karamci abdulla kadan sannan cikin hanzari ya leka salis ka tsai da yaran da muka wuce yanzu don naga hanyar fita sukayi . Salis ya juya da hanzari , abdulla ya zauna ya jingina da kujerar ya dan daga kansa sama , Dr sagir yayi Yar dariya yace Sha yanzu magani yanzu kennan ungo ni rike yana Miko masa lemon exotic daya tsiya masa a Kofi karba yayi yadan bata fuska meye Kuma na fassarani dan nace a kiramin yara salis yashigo yallabai sun tafi daman wani direver ke jiransu sannan ya juya ya fita kallo abdulla yabisa dashi bai sake cewa komai ba sakamakon bugawar da zuciyarsa keyi ya runtse idanunshi Dr sagir yace ni sam ban lura dasu sosai ba da zan so naga bby dake kokarin samun gurbi da sauran mata basu samu ba abdulla yadan ja tsaki tare da kallon agogon dake daure a tsintsiyar hannushi a ransa ya kiyasta dai dai lokacin sannan ya dan tabe baki game da yin murmushin sai karfe bakwai saura suka bar hospital .gidan Dr sagir sukayi dinner duk da abdulla sam bai iya cin abinci sosai saboda shi sam bai fiyye yame yame a acikinsa ba hasalima ba kowane abinci yake iya ci ba ,dukka wata cimarsa mamin sa tasani . Dr sagir natayi masa tsiya a gaban matar sa hafsat kinganshi shekaru kusan hudu rabona da shi tunda na bar shi a Oxford ,shi ya karasa karatunsa Kuma sanda muka rabu bbu me address din wani acikinmu sai yanzu da ba a fi wata wata biyu da haduwarmu ba wai watansa biyar a garinan sai yau yazo ya ganki . Hafsat tace ai ya Yi kokari yau din ma kai kila ma baka je gidan nashi ba . abdulla yayi murmushin thank you hafsat Dr sagir yace naje na gaida mami dai Amman wannan tuzurun ina yaga mata da zai Yi gida kila Kuma mata ce tayi kiransa agarin nan ,kaga kaza tajanyo zakara kennan . Abdulla yace kai dai anyi dan bazan yaro suka kwashe da dariya kaji hausa da yawa ko madam ke koya Maka ,ka iya Karin magana sosai ita ma nima koya mata kazo in koya Maka don wannan hausar taka idan ka auri cikakkiyar bahaushiya wata rana sai tayi Maka dariya abdulla yadan tabe baki game da kada kafadarsa so what idan tayi ,si ba na jimma zan iya aure a garinan ,ina son wannan farin kebbi sai dai yayi zafi dayawa akwai rana . Very gud English man inji doctor to mami ma randa naje sai da tamin zance tanason taga kayi aure cikin dai wannan lokacin Amma lake tunanin bazakayi a garinan ba zaka gudu kennan .wayar mami data shigo ita ta katse su abdulla ya amsa wlh mami muna tare da doctor sagir tun 5 salis ma yana wajen Dr sagir yana kallonsa yana bashi sha'awar maminsa na matukar kula dashi da dukkan wasu alamuransa hakan yana birgeshi soyayya uwa da da, to mami gani nan bisa hanya ya kashe wayar mami na gaishe ka tare da mikewa . Aunty Maryam ce tayi sallama ta shiga gidan a gajiye take lis tana jan kafa ga tirtsetsen ciki a gaba Aisha tasa mu a tsakar gida tana aiki ajiye aikin da sauri ta riko mata jakar tana dariya kai aunty sai kace yanzu ne haihuwar da Kyar kike tafiya fa . Usman kanin Aisha shi ya ruga ya dauko tabarma ya shimfida anan tsakar gida ni dan Allah ban ruwan ranar na n Shi nake ta begen tunda na karaso ta tashi ta Miko mata byn ta Sha ajiye kofin tace inna batanan ne tana daki lazimi take yanzu zata fito taji zuwanki aunty ina su saifu suna gida . Yaya Umar yashigo ya'yan Aisha la aunty da yammamnan yana gaishe ta Aa ai ban amsa gaisuwarka Umar sai dai mu hadu gaban inna kaninka yafika kirki ranar jumma nan ma yusif yazo Umar yayi dariya ai shi yaya yusif daga masallaci ya biya tace ko daga arfane ai ya fika usman yasa dariya inna ce tafito bakin yamma kennan ku dai ba a cika ganinku ido naganin ido aunty Maryam tasa dariya daga gurin aiki ma na biyo nan inna tace aikin kuma ? Eh wlh so nike watan kubi watan haihuwar sai in dauki Hutu Aisha tace Aunty Hutu ,zasu yadda ki dauki Hutu naga Baku dade da fara aikin ba . Tace duka wata biyu kennan zasu bani hutun haihuwa ai dole ne nafi so sai na kusa don in karfi Hutu dan in huta idan na haihu . Yaya Umar yace Yi sauri Aisha ki dauko min kayan dana baki jiya . Tashiga dakin ta Miko masa ya karba ,ya fita yana dariya aunty yanzu zan dawo tace adawo lfy usman yace yaya Umar din ne akwai tsabga bai jima da fita sai ga yaro da rake dayawa wai gashi inji Umar na aunty ne yasan tanason rake nan da nan ta fara Sha , inna ta tashi tashiga kicin rake dai rake dai ni me kike so In Miko miki kafin agama abinci aunty tace Allah yasa tuwan dawa zakiyi inna tace Aa mu faten tsaki masara muke sai dai tuwan ma za'a iya miki sai ki wuce da shi tace Aa inna kibarshi fatan ma zanci inna tayi shigewarta kicin Aunty Maryam tace tare zamu tafi fa Aisha ki tayani gyara daki an kawo min furniture's shekaranjiya ni gobe ma bazan fita ba . Aisha ta kalleta , Aunty Maryam tace gobe zaki dawo muna gamawa naga kina kallona sarkin zaman gida wannan basan yadda zamuyi ba idan aka tashi miki aure kullun kina jikin inna kai nasan inna dai tana shan fama. Usman yace wlh kuwa Aisha ta Harare shi tana dariya tace sun inna azumi take ni zan karasa mata abin shan ruwa gashi nayi wanki dazu zanyi guga da daddare gobe nazo da wuri aunty tace azumi inna naga yau talata tace Eh gobe da wuri zan gama ya n taho aunty Maryam tace na bari yanzu haka ma baki za ayi da daddare kaga ba halin Bina ko usman . Usman yadan mirgina kai ai aunty inajin yaya Aisha sai an hada da rukiyya tun yaushe nike bawa innarmu shawara taki kulani aunty ta kwashe da dariya yace wlh ko gaisawa kuke idan kace kana sonta shi kennan ta daina ganin ka da kima bare kulawa Kuma akwai su baadadi ,can yasa dariya kinsa ma abinda abokina shamsundeen yace cewa yayi shi wlh yaya Aisha tana matukar birge shi komai mata yana bashi Sha'awa shi daace irin abokin su yaya Ali ne sai yace yana sonta . Aunty
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62