Chapter 4
Chapter 4
shige abunta salis yadafe kai yayin da abdullah ya cije lebansa yana mai runtse idanunshi,salis yace ta leko ta hararemu ta wuce abunta . Hade da cewa kai dagani madam fa za'a dama daita . abdullah ya dubi agogonsa muje kawai salis ai munga inda tazo yashiga suka wuce . Tana shiga aunty Maryam tace me kika manta tace bakomai wlh aunty, irin banzayen kwarorin nan kawai" sukayi me kwarorin?inji aunty su dai nagani awaje aunty Maryam tadanyi dariya hum kedai baki da kara akan Maza . Yana idar da sallah yashiga part din maminsa yasame ta itama ta idar da sallah duk da agajiye yake yadan zauna kusa da maminsa ,sister dinshi amina ta Miko masa fresh milk a Kofi ya karba ya Sha ,ya bata cup ta wuce kicin yace mami zandan fita bazan dade ba dan ita mami irin mutane nan ne dabasason arabeta ko ita tarabi mutun haka ko mijin bata barinsa ya sakewa da kowa inba ita da yayanta ba,mami takarasa jan carbi ta shafa ta kallesa tace Amman kasan salis yatashi daga aiki ko,ko a haka zaka fita daga kai sai musa yace ni kadai nike son fita ba direba mami tace no abdullah banason fitarka kai daya ga dare gashi kai bawani sanin gari kayi ba sosai" kayiwa salis waya kawai yazo ku je tare abdullah yadan langwabar da kai yace mami banason takurasa cikin iyalinsa ,tunda yarigada ya tafi a kyaleshi nima ba dadewa zanyi ba ta kada kai ,shi kennan Amman banso ka dade a waje" yayi murmushin ya Mike bazan dade ba har zai fita tasake cewa yanzu kai kadai zaka fita kennan ahankali yace don't worry mamina I can drive my self tace agaida sagir zatonta can zashi taci gaba da abunda takeyi yayi murmushin ya fita ,. Cikin natsuwa yake tuki cikin dark green din benz har ya iso badariya dai dai kofar gidan dazu yayi parking cikin sa'a mai gidan ya tarar tare da wani bako ya isa yayi musu sallama tare da gaishe su , sannan yadan koma gefe basu jima ba sukai sallama bakon yashiga motarsa ya wuce . Abdullah ya matso ya sake dukawa kusa da mai gidan cikin natsuwa yayi masa bayanin bakuwar data zo gidan tazu" mai gidan bai fahimce ko wacce ba daga baya yayi wani tunani sannan yace yana zuwa yashiga gidan bai fi minti biyar ba ya fito a nutse ya karfafa kallonsa ga abdullah wanda tun tafiyar sa zuciyarsa ke wassafa masa abubuwa da yawa M .Auwal mijin aunty Maryam ne "ita Kuma aunty Maryam Yar kanwar mlm abu ce uwa guda uba guda ,yadanyi gyaran murya tare da cewa malam.....koda yake bansan sunanka ba cikin sanyi yace I'm Abdullah M .Auwal yace ashe abdullahi ne madalla bakuwar yarinya da tazo dazu ai AISHA ce ,a AI.....SHA.. ya maimaita sunan a ransa M auwal yace kanwar matata ce Yan dakika da sukayi da abdullah ya nakalci wani abu hakan ya sanya ya warware masa cikakken inda zai samu Aisha gidan iyayenta da unguwar da suke zaune Abdullah yayi godiya sosai tare da Yi masa sallama . Da fari yayi tunanin ya bari zuwa gobe tunda salis yasan gari sai su nemi unguwar da gidan haka nan zuciyarsa taji ba zata iya Bari zuwa gobe ba "a kasada yayi nufi yaje , ance mai tambaya baya bata sai ga shi a unguwar ,nesa kadan da lungu da akayi masa kwatance yayi parking sannan ya fito ya gaisa da mutanen da yasamu a gurin sannan ya kulle mota ya karasa . har yashige lungu da wayarsa yarinka haskawa saboda ya rike lokacin da M auwal yake masa kwatance mota baza ta shiga lungun ba hakan koda zai tarar bbu wuta yayi ahankali da kwatami idan yashiga lungun" yana magana yanasake duba jikin Abdullah to anyi dacen akwai wuta Amman duk da haka Abdullah nasake haska wajen da wayarsa gudun Kar ya sanya kafa acikin kwata byn yayi sa'ar shige kwatocin ne ya karasa kofar wani gida yara na wasan guje guje ya kirawo daya daga cikinsu ,yara 2 ne suka taho ya tambaye su gidan mlm Abu ko gidan su usman da sauri suka ce ga gidan can ya nuna masa da hannu abdullah yace na gode ya fida kudi cikin aljihun wando sa na baya ya basu ai ko suka shiga murna abdullah ya nufi inda yaron ya nuna masa wani datijo ya samu a kofar gidan kishigide yana kokarin kamo tasha abdullah ya isa yayi sallama sannan ya risina ya gaishe shi malam abu ya rage radio ya amsa ganin da yayi Abdullah bai sake cewa komai ba yana Kuma tsugunne ya sanya malam abu ya sake rage radio sosai daga bisani yace masa kana son gani wani ne ? Ahankali yace E nazo gurin Aisha ne ko kadan Mlm abu bai kawo haka ba iya tunanin sa cikin yayyen Aisha yazo nema wani cikin su to bari asa a kirawo ta,ko bata kwanta ba dan bata da wuyar bacci ,Abdullah yadan sunkuyar da kai kasa don yasan duk laifin zuciyarsa ne data danace da son ganin Aisha a yau "a daidai lokacin da taran dare ke neman Yi "M abu yayi kira cikin gida kanin Aisha ne yafito , Amman idan baka sani ba zaka dauka yayanta ne saboda girman jiki gareshi yayin da ita Kuma Aisha bata da jiki. usman shiga ka turomin Aisha tayi bako baban ya fada . usman Kuma ya juya ciki mintuna kadan suka shude yayin da malam abu yake nazarin Abdullah da tsabar kamar dayake dawani ya sani ya sanyashi ya zauna a gefen dakalin dake kofar gidan , usman ne ya katse shiru da cewa gata nan fitowa ,haka kawai Abdullah ya tsinci kansa yana tausayi wayannan bayin Allah don haka tun fitowar Aisha yake mata wani irin duban da yakejinta har cikin ransa, yayin da ita Aisha ke masa kallon tsoro karara a fuskarta jikinta har bari yake , Abdullah ya lura da hakan Amman sai ya dake hannushi duka cikin aljihun wandonsa ya hade mata fuska da Kyar ya iya bude baki may be an tasoki kin fara barci ?bata iya cewa komai ba duk da tana kokari son yin magana Amman bakinta yakasa furta wani abu, yawan duban hanyar waje da take ya sanya Abdullah yadan rage murya cikin sanyi jiki yakira sunanta a frigice ta sake kallonsa ,jin wani tashin hankali karara wai har sunanta ya sani ta fada a ranta ga wani babban tashin hankali babanta da kansa ya sanya Akira ta Kuma har yanzu yanan a kofar gida banda haka da tuni ta ruga gida ,kmr ya shiga zuciyarta ahankali ya sake kiranta Aisha ko na tafi ne gobe na dawo da sauri ta daga masa kai murmushin gefen lebe yayi ya dubi agogonsa nima ina son in wuce din tunda naganki da inda kike . har yanzu fuskarta nan nashi ba yabo ba fallasa kallon tsoro take masa yace yes haka nike nufi ya dan ciza gefen lip's dinshi ,shikenan gobe na dawo ya zuba mata idanunshi masu rikita kwanyar duk wanda ya kalli cikinsu kallonta yayi son ransa sannan a hankali ya juya ya fice gabadaya ,ta saki ido tana binshi da
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62