Skip to content

Chapter 24

Chapter 24

Zuciyar Masoyi Book One Complete Hausa Novels 1 1,193 words 0 views Progress saved
Download Book

dago dara daran idannuta ta kalleshi yasake yin murmushi yace a kallonki nagane tambayar ki , Aisha ni bazan yarda da wannan shr naki ba idan munyi aure kidinga kinmin magana ba gaskiya ya fada har da turo baki batasan sanda murmushin kufce mata ba shima dariya yayi Amman nasan abinda zan dinga miki zaki dinga yimin magana sosai ,ni kadai nasan abun. Tasake yin murmushi yana kallonta kaunata na sake huda masa zuciyarsa, yadan gyara murya cikin natsuwa yace Aisha zanje interview a Denmark gobe zamu wuce Lagos ta can zamu tashi nan da kwana uku zan zauna interview Aisha kiyimin addu'a samun nasara ,dady ya zabi da inje in zauna masa ,har inajin tsoro Kar inyi disappointing dinsa ya fada yana kallon kwayar idanunta yanason tace wani abu ta fahimce abinda shr nasa yake nufi ta dan girgiza kai sannan ahankali tace zakayi nasara ya dan kalleta yace meyasa kika ce haka tace nasan zakayi nasara in Allah yaso "ya lumshe idanunshi yana mai jin tsanyi na ratsa kowani sashi na gangar jikinsa ko ba komai yau tazo masa da abubuwa masu mahimmanci daga gareta yace to Allah yasa Aisha bbu igiyar aurena akanki Amman ina da matukar kishi most especially akanki sati biyu kawai zanyi Aisha dan Allah kada kibari wani yashiga tsakaninmu Kar ki Amince da duk wani abu da zai bata tsakanimu a yanzu haka nasan ni ba wani zaunanne ne a ranki ba Amman ina sa ran idan muyi aure zaki soni , Aisha inajin tamkar in tafi dake idan muje can a daura mana aure Aisha ina son Allah yabani ikon Yi miki abunda zaisa ki so ni idan muyi aure . Yadda yake maganar ya dada sa kirjinta yacigaba da bugawa.. . wuraren daban daban na halittar jikinta ke bude suna karfan sakoninsa" a zuciyarta tanason ta furta masa koda kalma daya ce mai mahimmanci da zai tafi dashi Amman hakan ya gagareta sai binshi take da shanyayun idanunta yayinda take sake kashewa Abdullah jiki , Abdullah ya dubi agogon hannushi karfe goma ta shige yace wai Kar aunty tayi fushi dani pas ten Aisha ta Mike cikin sanyi jiki uhmm har sauri kike ki tafi kibarni ko, ta sunkuyar da kai shima ya Mike yace akwai zanen company da guest house da zanyi acan shine Nike ganin zai tsayar dani har tsawon sati biyu ban da haka da next week zan juyo "tsaitin datake tsaye nan ya tsaya suna kallon juya ,ya suke hannuwanshi duka acikin aljihun wandonsa kara step uku yayi zuwa inda take har suna jin bugun zuciyoyinsu ya xuba mata idanunshi shidai yana son ta har bai san yadda zai misalta ba ,ita din wata sashi ce ta zuciyarsa yasake tsareta da Ido yace Aisha me zaki bani zan tafi ? Tayi shr takasa cewa komai ,yace to ke me kike so daga gareni ?ta girgiza kai yayi murmushin yace gobe salis zai kawo sako har da Nasu yaya yusif dukansu ,ta kalleshi tana tunanin shi baya gajiya da kyauta ne ,ta tuna kyautar kudin da yayi mata ba a kai sati guda ba har tsoro suka bata da sauri ta rufe ledar ta wurga su bayan akwatin kayanta har zuwa yau bata kuma bi ta kansu ba. hakan nan bbu wanda yasan dasu yanayinta ya kalla ya gane tana son Yi masa godiya ne kawai ya share ta yacigaba yasake duba agogo yace let me go Aisha please say something for me wanda zai yimin rakiyya da ragemin yawan kewarki da zanyi har tsawon sati biyu ya zuba mata idanunshi yace I'm gona miss you Aisha please ya maimaita kusan sau uku kicemin wani abu mana ..... still tana tsaye kmr an sassakata ,yaga alamun bata da niyar yin magana yace ba zaki gaya min komai ba ko haka kike son na tafi ya furta hakan yana mai langwabar da kai to muje har gaban aunty nace ta roke ki kigayamin abinda zai dinga tayani bacci , ahankali yake matso ta tana ja da baya har ta mannu da bangon dakin yayin da zuciyarta ke dokawa tana harbawa gabadaya jikinta yagama mutuwa murus kafafuwa sungaza tsayuwa akaran kansu da Kyar ta iya tattaro dukan wani kuzarin dake jikinta ta furta I will Miss you too........ Hade da lumshe idanunta tana jin wani tsanyi na ratsa sansar jikinta yasake motsata sosai ya tsaya kawai yana kallon bakinta da yadda ya hudu ya furta Kalmar sai yaji kmr ya daura bakinsa akan nata mai abin sha'awa ya zuba bakin Ido yana mai cizan lip's dinshi gefenshi ta bi zata wuce dan baza iya jurewa kallon dayake binta da shi ba,ya kamo tafin hannunta cikin nasa ya matsesu gam wani shock suka alokaci guda yana musu yawo ajikinsu sakamakon haduwar da tafin hannyensu ,kokarin cire hannunta takeyi daga nasa batare da sun kalli juna ba sausauta rikon ta yayi ta zame hannunta ta saya dai dai bakin kofar ciki tana kallonsa yadda yake kallonta ne yasa tarinka jin wani abu atare da ita nan da nan ta juya ta shige dan bata son irin abun da tafara ji a game dashi din bata San iya lokacin da ya bata kafin yatafi ba, . Tafiyar Abdullah da kwana shida maminsa tadawo Nigeria to abinda ta tarar ya maseefar gigitata domin dady yagama zartar da komai na batun auran Abdullah abin ya daure mata kai tana can dady na nan yana shirin yiwa Abdullah aure batare da itama an tuntubeta ba "tsawon kwanankin dayawa da dady ke nuna mata me za'ajira tunda Abdullah din yadamu da yarinyar kuma ta kowani bangaren yarinyar tayi illa daya gareta shine su din bawa wasu bane "ya nuna mata wannan ba wani abu bane tunda Abdullah yana son yarinyar bbu abunda zai gagara"mami tace Amman auren farko daza'atabayi a gidan nan yadace ace Yar manyan mutane zai aura koma ba haka ba a samu wacce akasan halinta ciki da waje ba irin wannan ba dan ni halin danaji daga bakin mutane batamin amatsayin matar da Abdullah zai aura. Dady yayi murmushin to ke bakisan mutum da shi da kansa bai san yadda halinsa yake ba sai mutane sun fada ,to duk yadda dady ya bullo mata sai tace ba haka ba ,akarshe yace shi kam yariga ya gama magana ,in Allah yaso Abdullah bashi da wata mata sai zabin ransa sai kuma idan bangaren yarinyar ne suka ki. Ran mami in yayi dubu to ya baci kwata-kwata a wannan taki jinin yadda dady yake mata musamman akan Abdullah Dr sagir ta fara sa aka nemo mata ta tunhumeshi akan maganar yarinyar da Abdullah yake nema iya abunda yasani shi ya fada mata to shi din yana da sauran kima a idon mami "Amman salis kuwa fata fata tayi masa ta kuma rantse akan idan har ta kamashi yana da hannu a hadin Abdullah da yarinyar nan to ya kawo karshen aikinsa . domin wannan karon bada salis Abdullah yayi tafiyar ba tare da security din dady sukayi RK da Immanuel shima (SS)ne na dady hatta part din Abdullah mami da kanta taje bbu wani abu data samu na game da yarinyar . Mami na cikin wannan tashin hankali mama hafsa ta dira a kebbi tazo yiwa

Table of Contents

Chapters

62 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62