Chapter 44
Chapter 44
Yace Aisha dubi kigani ya nuna mata Inda Abdullah ke zaune" mijinki peticent ne daga gadon asibiti yazo daurin auren ku kinsa tun accident din da yayi kin sami labarin ko? Ta daga kai yace to har yanzu bai gama warwarewa ba likita yace daurin auren "na daga ciki abinda zai taimaka gurin warwarewarsa . Ko kadan ita batasan da wannan ba dan haka a yanzu ma dagowa tayi takalli inda yake 'dady yacigaba to kinga zai yiwu adaura auren Kuma yabarki anan ya koma shi kadai "kiyi hakuri kibi mijinki da taimakon Allah da taimakon ki zai karasa samun sauki hakan yasa gabadaya jikinta ya mutu ita duk batasan da haka ba.. Shi kuwa Dady kallonta yake sak maimunarsa tana karama Amman ita Aisha kusan har tafi ta komai ,yana jinjinawa al'amarin Allah , a ganinsa kmr tayi karama da tabi Abdullah din. bugu da Kari yana ganin kmr ta yiwa Abdullah yarinta ,sai dai ba,a nan take ba tunda daga kallonta zatayi hankali ,a fili ya sake cewa kiyi hakuri kibi mijinki ki duba shi kinji .. Ta daga masa kai yace yauwa Allah yayi miki albarka Allah yabaku zuria ta gari ya dade yana Yi musu addu'a sannan ya tambaye ta ko akwai wata matsala tace bbu yace taje ta huta .. Karfe hudu zuwa biyar zasu wuce ta amsa ahankali ta Mike ta shige ciki dady yabita da kallo yana girgiza kai ya koma ya jingina bayansa da kujera "ya Kuma jin tausayinsu na ratsa shi ,yace aransa duka abinda mami kewa rikici kennan "dan shi dady bai taba ganin Aisha ba sai yau haka ma mami "ya waiwayo ya kalli Abdullah ya kira sunnansa yace Abdullah Aisha ba suruka ta bace diyata ce ko bbu aure tsakaninku ni mai iya rike ta ne "tare da duk kan dawainiyar komai nata dan haka kai ma dan Allah ka rike amanarta.. To abangaren dady ya wanke ZUCIYAR Abdullah din tas domin ya yaba da Aisharsa ciki da waje. "byn tafiyar dady ya shiga dakinta ya sameta ta daga Ido tamkar wanda tayi kuka ganin da yayi zata yi magana yasa ya matso da saurinsa ahankali tace su innarmu basu san yau zamu tafi ba yadda tayi maganar ne tayi matukar bashi tausayi" ta sake cewa ga sister tun jiya bata zo ba. Ya kamo hannuta cike da kulawa yace bari yanzu naje gidan, me yiwuwa baba yabiyoni sai kuyi sallama Inna ce dai nasan da kyar ne" shi Kuma salis sai yaje ya dauko miki sakina To shima mlm abu addu'a yayi musu sosai sai dai su yaya yusif da umar da Ali ne suka biyo Abdullah dan dama ita aunty tabiya ta fadowa su Inna koda ma Abdullah baije ba daman za'a tura wani ,sai ga salis shima ya dawo wai sakina ta wuce zuru tun safe .. A falo Abdullah yabar ta da yanuwanta yaya yusif ya Mika mata sakon su inna ta duba taga har da dan karamin alqurani me kyau wanda aka taba bawa baba abu tsarabar saudiya ,suke ta rige rigen ita da usman ya basu kowa yana so baba yace abar masa abin sa shima yanaso, tayi murmushi ta rungume shi a kirjinta tace ina usman .umar yace ai tun jiya da aka tawo dake yayi kuka har zazzabi ya rufe shi har yanzu yana gida bai fita ba "idanunta suka ciciko da hawaye tayi murmushi tace aranta bazai san yayi tarashina ba sai nabar garin gabadaya.basu fi mintina talatin ba duk suka Mike . Abdullah da ya amsa wayar teema ,daga cikin wayar take sanar dashi mami ke nemansa nan da nan yadan Sha jinin jikinsa ko wani abun ne kuma ya faru tare suka fito da su Ali . A part din mami zaune yake kusa da ita kanansa duk suna zagaye dashi . ya dan sake musamman tunda su faiza sunbar gidan tun ranar daurin auren tun kafin adawo faiza ta hau iskar karya tana fizge fizge tana surutai tana hadawa da sunan Abdullah, Amman duk haukan nata bata tona irin abinda tayi ba. Da bai samu Abdullah ba". nan kallo ya dawo kanta mama hafsa naganin haka ta tattara ta suka bar gidan ko cikakkiyar sallama basuyi da mami ba" dama haka abin Allah yake idan Allah yariga ya tseratar da kai ka tsira. Mami tarinka kallonsa wata rayuwa ta daban dan nata zai shiga wacce acikinta girma yake shigar mutun" koda mutun bai shirya hakan ba .duk yadda taso da kasancewa auren nasa ba haka yazo mata ba. "ga Abdullah din zaune a gabanta matarsa a can wani waje daban wadda bata ma san ko wace kala bace "daman Kuma dady ne ya hana akawo Aisha gidan yace kai tsaye a wuce da ita gidanta ,mami ta jinjina kai Amman ita yanzu rayuwar dan nata ita tafi damunta, ta numfasa tace yanzu yau din kennan zaku tafi yadda yaga tayi maganar cike da kulawa ba kmr a yan kwanakin nan ba ,yasa ya ji ko mamin tasa ta fara saukowa ne . Ahankali ya dan kara matsowa kusa da ita yace dady yace yau yake so mutafi ta sake numfasawa tace tunda yace yau din ne nasan bbu fashi ta girgiza kai sannan ta Kuma cewa shikenan sai kun dawo Allah yabada zaman lfy .. kukaramin hakuri sakamakon rashin yimuku typing da yawa zuwa wani lokaci komai zai tafi yadda ya kamata MMN SUDAIS CE [3/12, 3:01 PM] Kaunace Sila: 💗💗💗💗💗 ZUCIYAR MASOYI 💖💖💖 💗💗💗💗💗 AISHA A BAGUDO Page 27 Da hanzari Abdullah yashiga dakin "har kan gadon inda take zaune a takure ya janyo ta jikinsa ya rungumeta tsam a fadadan kirjinsa" ahankali ya kai bakinsa cikin kunneta am sorry.... am sorry.... my Aisha na barki ke kadai ko tun safe na shigo kina bacci naje naga su mami ne "ya matse a jikinshi sosai har suna jin numfashin juna sannan ya dago fuskarta yana kallon kwayar idanunta duk batayi kuka ba Amman da ganin idanunta ya gane bata samu ishashen barci ba. ya sake saita bakinshi daidai kunneta ya rada mata wani abu wanda har yasa ta janye fuskarta daga hannushi . yayi dariya sannan ya ziro kafafunsa daga kan gadon tare da fadin kin shirya ko? Sai muje muyi breakfast Ahankali ya sake juyo wa yana mata kallon tsab idai har ba idonsa bane yake masa gizo sai yace tun kayan jiya datazo dasune ajikinta. Ya sake kallonta tabbas su din ne Kuma ko fitar da yayi bai sa ta tashi tayi wanka ta gyara ba .ya dan zubawa jikinta Ido zuwa wani lokaci sannan yayi murmushi gefen baki.a hankali yace wayyo Allah ita da kanta ma bata yarda da kanta ba, Kuma tun a jiya ya lura da kayan sun da meta. dalilin haka ma ya dada sawa ya bar mata dakin dan ta samu ta canza wasu yasa hannu ya kara jawota yana Yi mata dariya yasan lallai zai dan Sha wuya wannan yanayin Nata" yana matsa mata hannu ya kira sunanta bata amsa ba Amman ta dago da kanta yace idan munyi breakfast zanje gidan Dr sagir domin a yau din nan zamu wuce Abuja dan ta can zamu tashi idan na fita sai ki shirya duk da kaya biyu
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62