Skip to content

Chapter 58

Chapter 58

Zuciyar Masoyi Book One Complete Hausa Novels 1 1,152 words 0 views Progress saved
Download Book

yace me kika tanadar min kinsa ina matukar son kasancewa kuma ni maye ne akan kaunarki . ahankali tace to ni ka sausauta min yace da me fa ,tayi shr yace talk to me now ya danyi murmushi dan fahimci abinda take nufi . Ina cikin damuwa wlh jiya ban samu isheshen bacci ba . gashi yau ma da kyar zanyi tunda sai na karasa aikin. ana son shigar dashi kafin tafiyar dady . Yayi kasa da hannushi yana taba cikinta kin ci abinci kuwa cike shagwaba tace naci sauran kai yace munci tare da dady duk su teema suna gaishe dake ta sake narke masa ajiki yadda take mutsu mutsu ajikinsa yarinka jin tamkar tana tsokonusa ne .tayi murmushin tace na godewa su teema yace irin wannan shagwabar da wannan idanuwanaki .su kesake birkitamin brain fa su barinka jina a duniyar sama please...Ina neman wata alfarma ta dan kalleshi hade da gyara kwanciyarta ajikinsa alamun tana jinsa yace kice kina sona koda kuwa sau daya zan ji dadi .. kuma bazan Raina ba . Amman tayi shr buris dashi taki cewa koma. Ya sake cewa yace please now ... still taki magana da yake yasan halinta Yar ra,ayi ce haka yagaji ya hakaru ya watsar da zance . ahankali ta Mike zaune daga jikinsa saboda sakinta dayayi. Tace muje kayi wanka yayi shr shima ya dauko system dinshi ya fara shigar da ragowar aikin tace ni dazu dama gida ka kaini naga su inna. shiru ba kowa sai ni kadai fa . Amman gobe zaka barni naje ko ? bai kalleta ba yacigaba da abinda yake . yace ki bari na kammala da tafiyar dady sai na kai ki da kaina . ta dan kalleshi tayi murmushin tace Amman kwana zanyi idan naje ko ? Ya bar abinda yake ya zuba mata manya idanunshi. ya tsare gira sosai yana nazarinta sannan yace well..idan za'a bamu dakin ya umar ai shikenan . sai muje har ni mu kwana. dan ina da mata ba zai yuwu na kwana gwaro ba . Ta rufe bakinta da hannu tana dariya yacigaba da abinda Yake. kuma shi iya gaskiyar sa ya fada . Washegari tun bakwai Abdullah ya fita a saboda karfe goma ya kira meeting wanda da kyar ya iya barinta ita kadai . hakan badan yaso ba ya fita yana tunanin yadda zai rinka zuwa akinsa ya dinga barinta . Karfe goma daidai yashiga meeting din. har dashi kansa dady. Abdullah ya dau zafi sosai akan barnar da akai musu a company. ta hamdame miliyoyin nairori. dan haka a natse yake bayaninsa dalla dalla yadda kowa zai fahimta. dama kuma da yawa ana shakarsa saboda mutun ne da ko kadan baya son zalinci . cin amanar bai faru ba sai byn da baya nan . Dady ya zubawa Abdullah Ido yana ta bayaninsa a natse. yayi frash dashi yakara wani irin kyau tamkar bashi ya kwanta a gadon asibiti watanni baya ba. ya tabbatar aure ne ya fara karbarshi yayi murmushinsu na manya yana alfahari dan nashi daya fito ta tsatsonsa a yau ma ya dada Gane zurfin illimin da Abdullah din yayi ne ya yiwa .godiya yayi wa Allah . tare da jijinnawa Aisha lallai tacire tuta .kuma taci kyauta a gurinsa na musamman . dan Abdullah har yaso yafishi da kaifin illimi. karfe daya suka fito meeting yayinda karfe biyu daidai jirgin su dady zai tashi daga nan ma Abdullah I M Siri magaji company ya wuce . Aisha kuwa dake zaune a bedside dinsu tana amsa wayarsa inda yake sanar daita tashin dady suna gama waya dashi tayi bakuwa. bata taba ganin fuskarta ba sai sai a hoto dan haka ta gane daya daga cikin kanne Abdullah ne. direban daya kawota ne yake tambarta sanda zai dawo ya dauketa tace sai around 5 pm . Dukkan su sunyi murna da ganin juna musamman Aisha . da take zaune ita kadai ta kasa kiran sunanta dan bata gane kowacce ba cikin teema da minal dan ganin da ta musu a hoto dukkansu suna kama da juna sai dan hasken fatan da Abdullanta ya fisu. . Amman hatta yanayin kallonsu iri daya ne dana Abdullah . Aisha fa tarasa inda zata sakata karo na farko kennan da wani daga ciki jinin Abdullah suka ziyarceta. ta Mike tace ina zuwa tashige kitchen . Minal ta zuba mata ido tace wow irin kawayen da tafison tayi kennan a duniyarta . duk yadda ta dauki aunty tasu ta wuce yadda aka fada musu . sai taga gabadaya taji birgeta. haka a dalin mami na da bakuwa ne yasa yau ta zamo jiki tazo ta ganta . Sun sake sosai da juna ita da Aisha duk rashin son maganarta . a ranar ta dage tana yi da bakuwar suna ta dariya har la'asar suna tare . Dan har abinci tare sukayi wanda wannan lokacin shine karo na farko da ta suma shiga kitchen . da sunan dafawa miji abinci da zai ci . tun suna Germany da tayi maganar dafa abinci ita ko koya mata ne yayi irin wanda yake ci . Amman yace shi Sam bai sanda wannan zance ba. Shi kam ba abinci akace tazo tayi ba. cewa akayi tazo ta kula dashi . tare da minal sukai komai ta koya mata drinks kala hudu wanda Abdullah ke matukar son Sha. sai ko abinci , byn sun ci sukai sallah la'asar suka sake shiga kitchen dan yin abincin Abdullah kala biyu ta gane yadda ake yinsu sosai . suna shirin yin na uku sai ga Abdullah ya dawo ta kasa barin mina ta tafi gunsa "to itama minal din a waye take . dan haka tace ta barshi taje gun bros zata Jirata da kyar ta bar kitchen din ta tafi minal tayi murmushin tabi bayanta suka gaisa da Abdullah. Abdullah ya nuna jin dadinsa sosai yace thank you minal ashe kinzo kin debe mata kewa . teema fa minal tace taje school yace ok kefa tace na gama registration na gama komai sun bani masa com next week zamu fara daukar lecture yace very gud ya shige ciki itama ta koma kitchen . Ahankali Aisha tabi bayansa tana shiga ya janyota ta fado jikinsa gabadaya yace a gajiye nake fa bacci naxo muyi ta zuba masa idanunta a tsorace take girgiza masa kai . dan tunda taji haka tasan abinda yake nufi sarai. ahankali tace ni bana jin wani bacci . yace karyarki tasha karya yarinya . dolenki kiyi bacci bari nayi wanka nazo . ko minti goma bai yi ba ya fito daga wanka da kyar da rarrashi tasamu ya ci abinci da suka yi masa . yace ya koshi ya sake jawota suka zube kan gado ita ko gabadaya hankalinta na can kan minal . Tana can tana jiranta tana son yi masa kuka Amman ya hade fuska yace wai meyye haka ne kinsa fa rabonmu da juna tun a abuja aiki ya hanmu sakewa . nazo kuma yanzu kinki sakin jikinki dani . ta kalleshi ahankali tace minal na nan fa ya dubeta a dan fusace yace so what idan minal na nan shiyasa baza a kula dani ba ko me kennan .. ta girgiza kai tace please kayi

Table of Contents

Chapters

62 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62