Skip to content

Chapter 22

Chapter 22

Zuciyar Masoyi Book One Complete Hausa Novels 1 1,190 words 0 views Progress saved
Download Book

sanarwa da mama cewa shi Aisha yake so ya hada da yasir ,mama tayi tsalle ta dire tace sai dai byn ranta Amman baza a hada" da" da wannan yarinyar mai kama da karuwai ba ,Abba yaji haushi har yamayar mata ai shiryuwar dan naki shine a hada shi da ita dan bakinsa abinda yake aikata acan ba, ai ko ta hau shi da maseefa yana zagin danta yace inkinga bai aure ba daman can ba matarsa bace aurensu shine kawai zai sa yadawo ya zauna ya daina tara matan banza a can ,ina dawowa zan sami mahaifinta kan maganar Aisha ta bugi cinyar sakina ta ce kai sister ina aka tafi ne tunanin kuma fa suka dariya ? Ta kalli Aisha ko wanka batayi ba Amma tamkar wanda ta tsala kwalliya kullun kmr sake kara mata kyau akeyi ,jiya da yamma sunka je salon ita da aunty Maryam itama an gyara mata gashinta sosai kanta bbu dankwali ta rataya dan guntun towel a wuyanta sakina tace dan Allah sister ki tsaya ahaka ta fito da Yar karamar camera tace zakiyi wallahi sai kin tsaya na miki hoto Aisha dan bata fuska tayi kai sister a haka zaki wan.... bata gama magana ba har ta dauka da yamma tashiga dakin Aunty dake cike da kawayenta yawanci duk Yan wajen aikin sune ta gaishesu,aunty tace ga sako nan Abdullah ya aiko miki zata dauko mata tace barshi kawai aunty sai zuwa anjima ,ta fita wata daga cikin kawayen aunty tace kai wannan kanwar taki zaayi yanga Maryam kinga da Kyar take magana tayi dariya tace wallahi ba yanga bane nature dinta ne kawai haka wata tace ai idan ma tayi yangarma zata ci riba tunda tana da kyau da abubuwan yin yangar. Alhj ishaq ya kalli dan nashi ya kira sunansa cikin sanyi yace Abdullah daman abinda ake so hali na gari ga kowane dan Adam to ALHAMDULILLAH anyi shedar yarinyar da iyayenta tun daga kan makwaftansu har zuwa can ka'oje inda aka haifin mahaifiyarta , mahaifiyarta itace kawai Diya sai dan uwanta wanda daba'asan inda yake ba wasu Fulani rigar dake can "sidi magaji )ne Amman duk da kakaninta na wajen uba ba'anan suke a ka'oje ba Killa ma da iyaye da kakanni suna nan raye da zasu San juna dan nima da kaganni asalin tushena kennan ka'oje cikin kauyen (sidi magaji) kmr dai yadda kasani sana'ace takawo mahaifinta nan mlm abu Shedarsa itace talaka ne mai godiyar Allah suna zaune da matarsa uwar yayansa itama kuma Anyaba mata sai yarinyar data Kare karatu a makarantar yan'mata dake federal gwandu abin farinciki ,nagarta kamun kai da kokarin yarinyar yasa har tayi suna da aka santa a makarantar sosai ita ta rike shugaban dalibai dady ya dan tsagaita to daman wannan ake so a duk wani iri da'ake nema . Dady ya janyo wasu hotuna guda biyu ya zuba masa a gabansa to Abdullah dai wani iri yake ji ajikinsa cikin sanyi jiki ya dauki hotunan yana dubawa hotunan Aisha ne sanye da uniform tare da yan'uwanta dalibai sai teacher dinsu sai Kuma dayan gurin wani daurin aure ne yagano mlm abu zaune a gefe shi da wani Abdullah dai yakasa magana dady yacigaba abinda na nunawa mamin ka kennan tun dazu ,nagarta yarinyar ta fito kuma shi zaisa a yada zuria ta gari dan haka tunda an samu wannan sai ature duk wani rashi tunda bashi ake bukata aure ba, ahankali yake kallon dady tamkar yasaka masa kuka farinciki haka yakeji ,dady na sonsa dan yadamu da damuwarsa alhaji ishaq yagama karanto hakan a fuskar Abdullah ya girgiza kai kasanar da iyayenta zanzo da kaina in ne ma maka aurenta murmushin Abdullah yayi dan tsabar farinciki, yana fadada murnarsa a fili yace thank you dady Yace bbu komai tashi kaje ya fita yana rayawa aransa dadynsa ya dauki Aisha'rsa da mahimmanci da kansa zaije ya nema masa aureta sabanin yawancin abubuwa sai dai ya wakilta aje . Tsantsar mamaki ne ya rufe mami to ita har yaushe Abdullah ya samu yarinyar dayake so batare da ita din tasani ba har zuwa yanzu dayake gabanta kallon mamaki take masa tace Abdullah tsawon wani lokacin kuke tare da yarinyar a garin nan batare da na sani ba Abdullah yayi shr ya fuskanci yadda mami ta dauki zafi akan maganar tace bazai yuwu ba dadynka yayi bincike akan yarinyar dole nima zanyi nawa bincike daban ,tashi kaje zan nemeka Abdullah yayi shiru kwance yake kan doguwar kujera a falonsa ya harde hannuwanshi a kirjinsa yana tuna maganganun mami ko me mami zatayi shi dai ta ceceshi ta amince ya auri Aisha shine kadai kwanciyar hankalinsa da samun lafiyar a rayuwar sa .to har yau dayadawo daga aiki yaje gurinta abubuwa biyu sun cushe masa farinciki da damuwa dady da mami ,yana matukar tsoron mami yadda tanuna rashin son ta akan Aisha yasan mami sosai idan ta nuna...... MMN SUDAIS CE [3/12, 3:01 PM] Kaunace Sila: 💗💗💗💗💗 ZUCIYAR MASOYI 💖💖💖 💗💗💗💗💗 AISHA A BAGUDO Page 12 Yana matukar tsoron mami yadda ta nuna rashin son ta akan Aisha yasan mami sosai idan ta nuna kin mutun a fili bbu wanda ya isa yasata dole ,ya kalleta idanunshi suka Yi ja yace Aisha idan aka ce za'a daura mana auren cikin satin nan zaki amince ? A frigice take kallonsa tana girgiza kai gabadaya tagama rikecewa tace nidai kayi hakuri ba dai yanzu ba ,ta zuba masa idanunta shima ita yake kallo yace yes na matsu A ce kinzama matata " tace nidai kayi hakuri idan Kuma ka damu sai yanzu to kana iya samun wata ni sai zuwa wani lokacin "yaji haushi maganarta Amman yadda tayi maganar yagane yarinyarta ta a fili ya zabga mata harara yana mai jan tsaki yace ai ba sai kin gayamin ni kadai nike haukana akanki ba nasan bakya sona , takalleshi kamar zatayi kuka kayi hakuri dan Allah ba haka nike nufi ba" bai sake ce mata komai ba ya juya ya barta anan . Sai taji ba dadi aranta daman Kuma ta lura tun zuwansa ta fuskanci kmr yana tare da damuwa . To har zuwa kwana biyu da maganar su da mami bata sake tada zance ba a iya nasa tunanin ko mami ta hakura ne" wani satin mami take sa ran tafiyar ta zuwa Egypt dubo mahaifinta dake kwance ba lafiya shine dalilin dayasa ta ajiye komai tabari sai ta dawo Amman a wayewar garin jumma'a labarin rasuwarsa ta same su dan haka cikin rashin shiri tayi tafiyar ita da su teema yayin da dady da Abdullah sai rana Saturday suka bi jirgin yamma suka isa, washegari uku dady yadawo Abdullah kuwa kwanansa goma suka juyo tare da su teema da minal saboda makaranta mami ta zauna saboda tafiyar bata kusa bace dole ta zauna har ayi arbain . Ko sanda ya dawo da washegari sai da yaje yaga Aisha ya rinka nuna mata yadda yayi missing dinta na kwana biyu da bai banga ta ba Aisha taringa kallonsa yanabata mamaki ko kadan baya da riko iya tunanin ta fushi da yayi ranar da yayi zuwan sa na karshe shi ya hanashi dawowa ,sai da yasanar mata da rasuwar da akayi musu. Tayi masa gaisuwa

Table of Contents

Chapters

62 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62