Skip to content

Chapter 27

Chapter 27

Zuciyar Masoyi Book One Complete Hausa Novels 1 1,179 words 0 views Progress saved
Download Book

yayin da kirjin Abdullah yacigaba da bugawa kmr ana buga masa guduma "kamar yadda akace tsiya ce tasa muke haukan son hada ka da banzar diyarmu to a haka nakewa Allah godiya har nan ka Tako bazan manta ba kozo neman ta.. dan haka duk haukan tsiyarmu da mukeyi sai da kazo sannan muka fara , saboda haka ni mlm abu nace kaje can ka nemi diyar masu arziki ka aura Amman ba dai diyata Aisha ba...... ZUCIYAR Abdullah CE ta tsaya cak tadaina aiki na wani lokaci sannan dagabaya tacigaba da bugawa da sauri da sauri sakamakon Jin maganar da mlm abu yace , duk wani kuzari da karfin jiki bbu shi atattare dashi hankali atashe yake bin mlm abu da kallo kawai yake Yi " mlm abu ya jijiga masa kai alamar haka zance sa yake .... Sai yanzu Abdullah yasamu yayi magana cikin sarkewar murya tare da dunkule hannuwanshi duka waje daya yace dan grman Allah baba kar kamin haka idan akai haka wlh komai zai iya faruwa dani ... Mlm abu yayi murmushin takaici yace sai dai kayi hakuri , saboda mahaifiyarka ta Raina yadda Allah ya ajiye mu cewa tayi zata bamu million goma domin in raba diyata da kai ...dan haka ko kai kadai karage mata a duniya gara ta zauna jiran wani da na baka ita" saboda haka duk wani cin zarafi da cin mutunci da aka zo akayi mana har gida wannan munbarshi akan haihuwace ta tajawo mana haka .Amman halaka ta aure tsakanimu bbu shi har abada. in Allah yaso ni da kaina zan zaba mata miji da yayi min kuma daidai da ita ... Abdullah ya zubawa mlm abu idanunshi jikinsa har karkarwa yake tsabar tashin hankali dayake ciki musamman da ya karanci hakikanin gaskiyar mlm abu yake fada masa ,yace to.....sai kuma yayi shiru yana juya kansa cikin sanyi jiki yace baba bari na koma gida gurin mami wallahi zata yarda idan naje zata amince in ....aure .. Aisha dan Allah kar kabawa kowa ita ni kadai ne mijinta ... Mlm abu ya kalli Abdullah ya gane duk a rude yake da maganar.. ya dada fuskantar yadda yaron yake son Aisha Amman hakan da yayi shine kada zai sa su tsira da mutuncin su , yace Abdullah idan kaje ka samu mahaifiyarka da zamce ai asirin da ake fada munyi maka za'a sake kallo da har yanzu yana cinka , dan ma banda mahaifiyarka ce Amman yadda aka zo har gida aka keta mana haddi muka dauki hakuri,kaima hakan ya kamata dole kayi hakuri da Aisha.... Abdullah ya hadeye wani dunkulalle abu dayake Jin sa a makogaronsa yana kallon mlm abu daya fara nade tabarma dayake kanta ,tare da daukar radiyonsa ,idonsa suka yi jazir ya zube gwiwarsa a kasa yace na gode baba Amman dan ka taimake ni naga Aisha koda ganina da ita na karshe kennan ... Mlm abu ya masa duban tsab kmr wanda yake son ya karya masa maganarsa banda ma darajar sa data mahaifinsa ai da yanzuya kore shi daga kofar gidansa ".yace wannan kana maganar wani al'amari ne da ya shude ya zama tarihi a game da fitowar diyata wajenka ina fatan idan ka koma zaka sanar da mahaifiyarka in Allah yaso gobe suzo su karfi komai na aurenka in kuma basu zo ba yana kan hanya , sannan mlm abu ya juya zai shiga gida. Allah sarki Abdullah bawan Allah rasa yadda zaiyi yayi ya Mike a hankali tamkar ma baya cikin hankalin sa kmr ya manta dawa yake magana yace to baba idan kashiga kacewa Aisha ta taba cewa zatamin addu'a kuma nasan tayimin to yanzu ma dan Allah tayi min addu'a akan dukkan abinda zai faru a kaina a dalilin ta...sai da mlm abu yagama ji hakan sannan ya shige gida maganar Abdullah ta tsaya masa arai , musamman yanayin sautin daya fadi hakan dashi ..... Abdullah ya zubawa kofar gidan ido mami ke kallon yafi karfin Aisha Amman shi tun daura idanunshi akanta da yanayinta yake ganin kmr zatafi karfinsa ,a duk zuwan da yake gurinta a hakan yake kallonta har gashi a yanzu yake tsaye a kofar gidan su ya dada gane da gaske Aisha tafi karfinsa ... Ya jima yana kallon kofar gidan jitake kmr ya shiga har inda take ya daukota ya gudu da ita, kowacce kasa a daura musu aure in yaso idan ta tasamu ciki ko ta haihu sai ya dawo da ita su bawa iyayensu hakuri" a sannan bbu mai raba su , hannushi duka biyu ya soke cikin aljihun wandonsa ya zubawa kasa Ido tare da tura lip's dinshi na kasa a baki ya dago Ido yana sake kallon kofar gidan idanunshi sun jazir dasu sannan ahankali ya juya ya soma tafiya cikin sanyi jiki shi kansa bai san a wani irin yanayi yake ciki ba ... Tun tara da yan mintina ranar da mai gadi ya sanarwa alhj ishaq rashin ganin dawowar dan nasa gida hankalinsa yake a tashe har yanzu da gari yawaye ya sanar da police haka nan securities dinsa sun bazu koina ,ko mami basu sanarwa ba sai byn sallar asuba domin yasan ita bata wani hakuri akan ya'yanta don haka ya kyaleta ,sai da rana yadda mami ta dinga Yi kamar Abdullah kadai ne danta ..... inda mami sukayi magana da alhj ishaq akan aure ,daman abunda dady ya guda kennan ,to har zuwa karfe uku na safiyar ranar bbu wani bayani akan Abdullah Allah sarki dady har kasa zama yayi sai karfi goma da mintina sannan ya amsa wayar police da daya daga cikin wayoyin Abdullah, cewa yazo teaching hospital sir yahaya da gaggawa an tsinci Abdullah cikin wata benz baka mai dauke da number I. M sidi magaji yayi hatsari.. sai da dady yayi da gaske sannan mami ta hakura da binsu dan kusan tafi dady gigicewa .......... MMN SUDAIS CE [3/12, 3:01 PM] Kaunace Sila: 💗💗💗💗💗 ZUCIYAR MASOYI 💖💖💖 💗💗💗💗💗 AISHA A BAGUDO Page 16 Alhj ishaq ya isa asibitin tare da securities dinsa yayin da police suke tare dashi har cikin dakin da aka kwantar da Abdullah yakarasa kan gadon " Abdullah dinsa ne kwance bbu inda ke motse ajikinsa da oxygen a hancinsa sai bandejin dake daure a tsakanin kafadarsa da hannunsa sai kansa daure shima da bandage har yanzu jinin dake zuba a wajen kansa bai dai na zuba ba... ,... Dady ya runtse ido sannan ya sake budewa tabbas Abdullah din nasa ya sake gani acikin wannan halin" kwance rai hannun Allah ya juyo yana tambayar doctor daya karbe shi Likita ya soma masa bayani yadda abun yake Abdullah ya bugu sosai ga kariyya a kafadarsa sakamakon kokarin fitowa daga motar bayan ya bude kofar lokacin da abin ya faru sai raunikan dake kansa da kafadarsa sai buguwa da kirjinsa yayi har ya janyo masa matsalar fitar numfashinsa ,.. dady ya sake zubewa a gefen Abdullah har yanzu baisan ida kan sa yake ba "dady yace Abdullah dina ne da duk wayan rauninkan ya runtse idanunshi yana karanto duk wata addu'ar samun natsuwa ,ya Mike ya fito police suka biyo shi abaya suna sake mishi bayanin yadda al'amarin ya faru... A ranar dady yasa aka masu visa zasu fita Germany

Table of Contents

Chapters

62 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62