Skip to content

Chapter 9

Chapter 9

Mikiya Book One Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
Download Book

zaure" Dammmm gabana ya bada sautin bugu baffa kuma yake ƙirana a irin wannan loƙacin kuma. Jiki babu ƙarfi na miƙe ina fita tare da nufar ɗakin zauren. Da sallama na shiga ya amsani tare da nuna min wurin zama, zaman nayi tare da gaisa shi ya amsani a nutse, "ko miye dalilin daya sanya Maryam ƙin amincewa Md firar da ake son yi da ita?" Kaina sunkuyar ina wasa da yatsun hannuwana cike da ladabi na furta, "Videon kai tsaye ne za'a haskaka ma duniya!, shi yasa sammm naƙi aminta da hakan, domin acikin sharruɗanka babu ɗaukar video!" Wani gwauron Numfashi ya kawo ya sauƙe tare da dubana, "A gaskiya banyi tunanin haka abin yake ba amma kije babu komai kije ayi firar kariyar Ubangijii yaci gaba da tabbata a gareki, Allah Miki albarka tashi kije" Da saurin umman mariya ta ɓoye bayan bishiyar dake kofar fita a dakin, domin dama badai iya laɓe ba, Ni kuwa banma san tanayi ba tunda cikin yanayin dana kasa gane masa na baro dakin. *AK* Ahankali cikin nutsuwar sa yake saƙkowa daga upstairs nashi zuwa wangamemen parlourn gidan, loƙacin sha ɗaya da minti sha biyu, kunga kenan minti uku ya rage masa. Zamani tv Duk da kasancewar yau kwata kwata bata niyar zuwa wurin aiki, amma haka ta danni zuciyarta ta fito tun sha daya saura, gudun kada tayi lettt, sai gashi kuma har yanxun wajen sha ɗaya da minti goma shiru shiru babu labarin zuwan nashi. Ɗan madaidaicin Agogon Rolex ɗin dake hannunta ta shiga dubawa ganin har sha ɗaya da mintinan ashirin da biyar tayi bai iso ba, hakan yasa ta jan ɗan ƙaramin tsoƙi, domin jira na ɗaya daga cikin abinda tafi tsana a cikin rayuwarta. Na miƙe kenan ina fita daga cikin department namu wasu irin fitattun narkakkun motoci guda uku suka sanyo kansu cikin coumpaund na gidan jaridar namu, hakan ya sanya ni ja baya ina komawa cikin dakinmu inda mardiyya ta shiga tsokana wai kwana biyun nan kamar wacce akama turen rashin son magana, nidai ci kanki ban ce mata har zuwa loƙacin da Md ya ƙara so cikin department namu, cikin wani irin rawar jiki sai faman zazzare idanuwa yake ya tsohon maye. A kaina ya fara sauƙe Idanu, cikin rawar murya ya furta, "MEERAH da dukkan alamu wannan baƙon namu wani ƙusar ne ke kinga wasu irin rantsantstsun motocin da yazo dasu?, tare da wasu samudawan escort, baki ɗayan sa tun daga ƙafarsa kamo fuskarsa a rufe suke cikin wasu haɗaɗɗun suit baƙaƙe ke hatta takalmin ƙafarsa abin kallo ne, maza yi sauri ki fito, kana ki tabbatar kin cire wannan liƙabin da kika kwama a fuska" Ko amsata bai ji ya fice harda haɗawa da ɗan gudu gudunsa, yake zai shiga kenan ya kusa cin karo da hancin bindigar dake hannun miles, wani irin zaro Idanu Md yayi, domin shifa sai yanxun ma ya kula da uban manyan bindugun dake hannuwansu, kuuuuuuu cikin sa ya bada sauti, gumi na keto masa, miles dake zuƙar cigarettes Samm bai kula da yanda ya tare hanyar da bakin bindigar saba, hakan ya sanya shi saurin janye wa yana tsare Md da firgitattun idanunsa da suka kada sukayi zajurr. A gujeeeeeeee MD ya zura har yana neman hantsilawa "innalillahi wa'inna ilair raji'un, me yake shirin faruwa damu kodai kidnapped namu aka zo yi " Ya faɗa a bayyane amma sai ya daure yana ƙaraso cikin Office ɗin nasa. A ƙalla Saida na ƙara wajen 10 mint da fitar Md ɗin, kafin na fito, Nima dai ganin wannan samudawan hannuwansu riƙe da manyan bindugun Saida ya razanani, amma na dake don nasan matsoraci baya taɓa zama gwani. Haka na ratsa tsaƙiyarsu na fice cikin takun daya fi kama da a ƙira shi dana yanga, saidai sammm ba haka bane haka Allah ya halicceni, zuwa wannan loqacin tuni wanda yake zaune harya fara fusata da zaman jiran yarinyar da murya ta kaɗai yaji, don ko photon ta bata yarda ta taɓa ɗaurawa a media. Wani irin mahaukacin ƙamshim turare ne ya fara welcome nawa, tun daga bakin ƙofar, a nutse na sanya zara zaran yatsuna ina tura ƙofar Office ɗin, ya ɗago kansa da Nijar yama Md magana yaci karo da zanen jan lallein yatsun hannunta, kafin na bayyana kaina cikin qaton hijjabina da kuma niƙab ɗina. Cikin ƴar siririyar muryata nayi sallama wanda Md ne kaɗai ya amsa ni banda mutumin dake haƙimce saman kyakkyawar kujerarn da nayi tunanin daga ina Md ya samo ta, don dai nasan Bama da irinta cikin kaffff gidan jaridar namu. Banko damu da yadda duk mutanen dake cikin Office zubo min Ido ba, domin duk da ko ina na jikinsa a ɓoye yake amma sai suka gaza samun sukuni. kujerar dake pacing dashi naja na zauna,kasancer nasan shine nawa mazaunin. sai table ɗin dake gabanmu wanda ya raba tsakanin mu, an ɗaura glass cup guda biyu masu ɗauke da ruwa, sai dai an rufe su da ɗan ƙananun fai-fai. Ta ƙasan ido na ɗan saci kallon sa dan koda na zauna ban tanka musu ba, ban kuma zare niƙa ɗin fuska na ba. Haka naci gaba da ƙare masa kallo duk kuwa da cewar bana iya ganin komi nashi, har yatsun hannuwansa kuwa abinda zan iya faɗi kawai shine da ganinsa ba karamin mutum bane, ko daga yanayin zaman da yayi irin na shahararrun sarakunan nan ba muna sarki ba, sai hujin dake kunnensa ta ɓangaren hagu ya sanya wani diamon ring barima color'n gold. Ɗan taɓe baki na nayi tare da janye idanuna dake kansa, Cike da ladabi Md ya ƙaraso tare da maƙala masa abin magana a jikin jacket suit ɗinsa. Nima ya miƙomin na maƙala a jikin hijjab ɗina, Sai da aka tabbatar mun gama kimtsawa sannan aka ɗora camara a kanmu. A nutse na sanya fararen hannuwana ina janye niƙab nawa zuwa saman fuskana, cikin aro jarumta da bada attention Kamar bani ba, sai da na kalla cemara naima masu kallo sallama tare da gaisuwar barka da wannan loƙaci tare da fatarn sake kasancewa damu a shirin mu na kai tsaye, dangane da wannan bawan Allah dake son bamu ƙarin haske game da AK. (Wama ya sani ko AK ɗin ne) Na faɗa aceñnn ƙasar zuciyar, sai kuma nayi saurin faɗin (kai hakan ba bazai taɓa iyuwa ba, bayan ance shi kamar aljani yake kuma tunda yake babu wata cemara data taɓa haska shi aduk tsawon rayuwarsa, saidai kawai sunan daya karaɗe ko ina sabo da mumman aikinsa) Saurin dawowa cikin hayyacina nayi dan gyaran muryan da aka min a take na dawo da ainihin nutsuwa na zuga ga dubban jama'ar da ke son kallon mu. Cikin tsare sa da Idanuwana duk da cewar bana iya ganin ƙwayar idon sane, na furta. “Assalamu alaika ranka ya daɗe”. A hankali ya motsa lips ɗinsa ya amsa min da “Wa'alaikissalam” cikin muryar dake tamkar wanda akama dole. Kai tsaye zaka taɓa fahimtar kallona yake ko akasin haka ba saboda akwai eyeglasses mai duhu a idonsa. Bayan irin hular nan ta sojojin da suke sanya wa. Yinai kamar ban damu da abinda yay ɗin ba nima, na cigaba da faɗin, “Wannan shiri na maka barka da zuwa, tare da nuna farin

Table of Contents

Chapters

54 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54