Skip to content

Chapter 7

Chapter 7

Mikiya Book One Complete Hausa Novel 1,205 words 0 views Progress saved
Download Book

cikin manyan samudawan sane ya fito tare da buɗe masa ƙofar motar, cikin zallar izza ya fito yana ƙara gyara zaman p-carp ɗin dake saman kansa, wanda lallausar sumar kansa ta fito ta ƙasar ƙeyarsa. Ya Ilahi wannan gida kacokam ɗinsa saidai mu ƙirashi da aljannar duniya, ga wasu haɗaɗɗun beneye wajen hawa ashirin da wani abu. Su dukka daga nan suka dakata shi kuma ya soma tafiya cikin tsananin zallar iya sarrafa tafiya, wata rantsatstsiyar ƙofa ya dosa tare da seta ƙofar da ƙwayar tsaƙiyar idanunsa, wanda suke nan exctly irin na mage a take kofar ta buɗe sai gashi cikin wani irin azababben narkakkun parlour, wanda ya linka na gidansa dake Victoria island sau goma a haɗuwa da tsaruwa. Baki ɗaya parlourn ɗauke yake da wasu uban lumtsuma lumtsuman kujeru wajen set huɗu, ga ta ko ina na parlourn kewaye da na'u'rorin sarrafa abubuwa, gaban wata kerarriyar ƙofar glass ya nufa, bayan ya shiga cikin lifter ɗin ya danna Black B Parlour 3 zuuuuuuu lifter ɗin tayi ƙasa dashi idanunsa Lumshe a haka har ta kawo shi parlourn, still wasu kofofin da suka kusa kwance min kai na kuma cin karo dasu, nan ya ringa ratsa parlouna yana wucewa har ya isa gaban wani ɗaki da yafi kama dana masu bada horo. Nan ma Saida yayi amfani da ƙwayar idonsa kafin kofar ta buɗe ya sanya ƙansa cikin ɗakin, tare da ɗan yin baya da blue jacket ɗin dake saman shigar sa, mutane biyun dake a galabaice ne suka yi saurin dago kansu domin tun da aka kawo su wurin ko sau ɗaya babu wani mahalukin da suka kuma gani. Gashi yau wajen kwanaki shidda ake magana, komai na amfan da aka tana jar musu ga ɗan madaidaicin stoor nan a cikin dakin wanda abubuwan da suka shafi rayuwa aka tanajar a cikin sa irin su kayan girki ne, maƙulashe ne kayan tea ne, chocolate cake recipe with milk duka dai abubuwa ne da akayi tanajinsu dama, farar kujera yaja irin da ƴan ɗaurin auren nan yana zama akai tare da fuskantar su. A take suka sha jinin jikinsu sai suka ji duk wani hope na ƙwarin gwiwar dake garesu ya gudu nashi wuri, Cikin haɗiye miyan wahalta governor Aminu Bello ya dubi AK tare da faɗin. "Mine hurumin ka na sacemu?, Wani irin ɗan jujjuya kyawawan ƙwayar idonsa yayi tare da furta. "Kar kayi magana a loƙacin da babu abin faɗa, koda da abin fadanma kasani shuru bai taba zama illaba, rayuwar duniya kamar series film take, episode episode take zuwa amma duk yawan film ɗin dole ne ya ƙare wata rana" Ministan gida ne ya ɗan zunguri Aminu Bello, tare da fara kifkifta masa ido ga jikinsa dake tsuma Shi kuwa cikin aro wata jarumtar ya kuma furta. "Yaro A wasu loƙutan kana ganin kayi nasara shine faɗuwa, haka ma wasu loƙutan ka yadda ka faɗi shine nasara" "Ka sani sawa a rai ne yasa falke baya jin wahalar tafiya,wanda idonsa basa gani sunanshi makaho, Ammah cikakken makaho shine wanda zuciyarsa bata gani kamar dai ku ɗin nan" "Ita fa Duniya kamar jirgin ruwa take, Zata iya kaika inda kake so, kuma zata iya kaika inda take so. don haka be careful respect your mouse ba lallai a wannan karon ta kaika inda kake so ɗin ba" "Bani da loƙacin ɓatawa loƙaci loƙacinsa,don ba zamane ya kawo niba, a cikin mutanen ku duk mutumin da ya kuskure ya kuma yarda ya haɗa hanyar sa da nawa, saidai uwarsa ta haifi wani badai shiba rayuwata rayuwa tace, haka za rayuwarku rayuwar kuce, kowa ya rufe idanuwansa akan mahaukacin zakin daya fito domin yin farauta, ya kuma toshe kunnuwansa daga hargaginsa" Sosae suka sake rikicewa ba kuma su sake rikicewar ba Saida ya danna wani ɗan abu mai kama da elevator kyawawan kwalaben wine suka bayyana tare da dasu cocaine cigarettes. Wannan cocaine ɗin ya ɗauka tare da walwale ledar yana matso da ita dab da hancinsa, wani irin kyawawan shaƙa ya mata tare da Ciro kwalin cigarette yana zarar guɗa daya lighter ya ɗauka a cikin abun kana ya karsta ya mata zuƙa ɗaya tare da faso musu hayaƙi Sigarin, zuƙa biyu ya mata ya gama da ita kai da ganin yadda yake zuƙar cigarettes kasan ehhhhhhhhh lalle wannan ubanta ne. A take yanayin idanunsa suka jirkice zuwa wasu colourn daban, wannan blue In tuni ya kau yana dawo wa jaaaa sosae ga kuma ƙwayar idon ta tayi wani irin fari tasssss tamkar wanda aka ɗura madara a cikin su. Haka ya tashi yana tafiya irin ta wanda ya bugu har yaje bakin kofar sai kuma ya waiwayosu cikin muryarn maye ya furta. "Duk lalacewan kura a dawa to tabbas tafi ƙarfin kare, haka duk lalacewan mafaraucin zaki yafi karfin alade" Zuuuuuuu kofar ta koma bayan ya gama fita , directly ya hau lifter ta komar dashi har zuwa asalin wannan narkakken parlourn. Cikin mayen daya fara ɗibarsa ya nufi kofar yana fita bayan ya loda mata security. Suna ganin yanayin her boss ln nasu suka tabbatar ba'a cikin hayyacin sa yake ba, axton ne yayi saurin buɗe masa murfin motar, shiga yayi suka ja motocin nasu a guje tare barin anguwar baki ɗaya. Wayar sane ya hau vibrating ring a fusge ya shi ƙoƙarin zaro wayar, *first love* sunan daya bayyana kenan saman screen In wayar, manna wayar yayi a kunnensa bayan yayi picking call ɗin, "My Boy!" Shine sautin daya fita cikin wata irin kamalalliyar murya me sanyi, a take yaji jikinsa yaji ya yi wani irin sanyi rauninsa na ƙoƙarin bayyana. Shirun da taji yamata ne yasanyata ta furta *"William"* gaban sa ne yaji yayi mummunr faɗuwa jin sunan data ƙira shi dashi. yanzun ma shirun yamata dama tasan abunda zai faru kenan ɗin, dama tasan hakan ce zata kasance duk loƙacin da zata ƙira shi da wannan sunan na William bakin sa yana masa nauyin ne wajen amsata. Da dai taga alamun bazai amsa tan ba ya sanya ta furta "ABDOUL-MALEEK KUWAIT! har yanzu kana nan kan bakarnka na ƙim amincewa na dawowarka gida?, rayuwar da ka zaɓarma kankayanxun William. takai ƙarshen maganar cikin yanayin Sanyin murya da kuma raunin da muryar ta samu, domin maganar harya fara fita da sautin rawa rawa na rarrabe wa. A hankali yaji jikin sa na ƙara yin sanyi sanyi, ita kuma cikin muryarn dake dab da fara zubar hawaye taci gaba da faɗin. "Kasan irin mikin dake cikin zuciyarmu kuwa William?, kasan irin tsananin ciwon dake galabaitar damu aduk loƙacin da duniya zata haskaka a matsayin criminal kuwa?, do on hey ta yes'ka'rev'nvu ka dawo ƙasarka me ƴanci, Onoyin na nan na maraba da dawowarka tare da sauran ƴan uwanka, harda ma jesra, twin yafi kowa missing naka. MOH tana buƙatar ganin ka William....... Sammmm bazai juri waɗannan maganganun ba hakan yasa hannunsa har rawa yake wajen datse qiran, wayar ya tsura ma lumsasaun Idanunsa tamkar mahaifiyar tasa ce agaban sa,Ajiyar zuciya ya sauƙe mai nauyi,yana ƙara lumshe birkitattun idanunsa. yana jin yadda namomin jikinsa suka ɗauka rawa, daga cenñnn ƙasar zuciyarsa kuwa wani irin mugun zugun masifa yake ji. Kife kansa yayi da tafin hannunsa yana cusa kansa tsaƙiyar cibiyoyin sa. Daga nan bai kuma

Table of Contents

Chapters

54 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54