Skip to content

Chapter 1

Chapter 1

Mikiya Book One Complete Hausa Novel 1,180 words 0 views Progress saved
Download Book

*🦅 MIKIYA 🦅* {Mai hangen nesa 👀} *~We want an end to oppression💪~* https://chat.whatsapp.com/GiLzmY90dz17bRbw5yMYBg ____________________ *HAJIYA idan har kinsan ba karatun littafin MIKIYA ne ya kawo kiba pls kada kiyi joining ma, kinga basai kinba kanki wahala Nima kin bani ba, so be careful, domin bazan lamunci zama da shara ba❌🫰* Ɗan ɗano🫰🤫 daga alƙalamin AMMEY LAYLERH 💐 Page 1&2 BY* *AMMEY LAYLERH ✍🏻♥️* ✯ *~🌠 OFFICIAL MIRRAH 💫~* *THE WRITER'S OF* * KAREN BANA* *JALAAL AREEF* *ƘAUNA BIYU* *And Now MIKIYA* # KIDNAPPER'S # Informants # DEEP # BEST LOVE # BlackMoney # By terrorism # Treason # Strong love # Right # Women's travel # The Secret Society # Oppression # Corruption # SADAUKARWA 💪 Rayuwa da ƙaddara a tare suke tafiya tamkar ƴan uwan juna sukee, rayuwa take tafe take da tarin ƙalubale a cikin ta,ko wanne mai numfashi yana tsoron MUTUWA. Wannan ba labarin ƙarfafa gwiwa bane,kuma ba labarine na al' ajabi ba, wannan kawai labarine na wata iriyar ƙaddara. Na Tsara wannan labarin ne da tunanin zan kawo gyara wa al' umm. Saboda zan bada labari na # KARFAFA GWIWA, JARUMTA, HAƊARI da kuma AL' AJABI EHHH tabbas Al'AJABI. Kunsan akan waye? *AK, EAGLE*. Wanda akema laƙabi da *THE MAN WHO CANNOT DIE🙄😱 {Mutumin da baya mutuwa} Shin UBAN DABANE SHI? Ko kuma ƊAN DABA,? Ko kuma BABAN MASHEƘA⁉️🚯. Tabbas duk wanda ka gani yau to yabiyo ta jiya. Haka zalika duk wanda ka gani a matakin nasara, to kuwa tabbas acikin nasarar nashi akwai tarin ƙalubalen daya fuskanta kafin haka, SADAUKARWA 💪 Labarine daya shafi ko wanne ɓangare na zalumci cin amana hassada baƙin ciki munafurci ƙunci duk wani nau'in saɓon Allah da abubuwan da suke faruwa da rayuwar mu a zahiri suna tattare acikin Wannan littafin na mikiya, wanda yake ƙunshe da manyan sakwannin da nake son isar wa ga al'umma harma da kasarmu nigeria 🔥🔥🔥 _________ *LAGOS* Victoria island A tsare a kuma jere ƙerarrun motocin suka gama daidaita parking na car's nasu Cikin wani haɗaɗɗen mention me girman gaske, wanda kallo ɗaya zaka ɗauka a ƙasar turai kake,, domin baƙi ɗaya komi dake cikin gidan na glass da glass ne. Cikin zafin nama jibga jibgan guards ɗin suka shiga dirowa daga cikin manyan motocin hannuwansu riƙe da manyan bindigu da bakaken kaya zaka dauka basamudaye ne. Cikin tafiyar sassarfa suka soma kutsa kansu cikin ainihin haɗaɗɗen mention ɗin. A natse suka ƙarasa shiga cikin rantsatstsen parlourn daya amsa sunan parlour, wanda yake kewaye da wasu fitunannun ƙayatattun Cautions masu azabar ƙyau da tsari farare tass dasu, ga shi an ƙawata parlourn da wasu irin roll designer's masu azabar haɗuwa, Sai wasu manyan zanen emojis da aka manna a bangon gabas da kuma yamma, komi na parlourn dai so need. Wani irin ƙamewa naga wannan samudawan sunyi tare da rusunar da kansu kasa, hakan yasa nayi saurin duban inda suke tsayen. Da wani Wani bazaraten matashin saurayi naci karo wanda kai tsaye na gaza fuskantar ainihin waye, iyaka kwantaccen gashin dake kwance saman qeyarsa kawai nake iya hanga, wanda yayi parking na lallausan sumar ƙasan ƙeyarsa, in banda walwali da ɗaukar idanu babu abinda sumar take aikin yi, ga wani irin fitinannen qamshin da take fitarwa. Yana sanye cikin wasu haɗaɗɗaun buttoned shoulder strip wool sweater na Paco Rabanne, Coffee and white color sai sweater daya ɗaura saman kayan, kansa sanye cikin p-carp blue black sai facemask dake saman kyakkyawarn fuskarshin, da ya mai wani irin kyau banabwasaba, a takaice dai babu ta inda na iya Gano wannan bawan Allahn wani irin azababben ƙamshi yakeyi tamkar Companyn tularen duka ne a jikinsa. Ƙafafuwansa sanye cikin designer sneakers ruwan toka ƙirar Dior, daga yanayin yadda yake zaune zama irin na sarauta na fashimci Dogo ne da tsayinsa zai kai kamu ɗaya da ɗigo tara ma'unin meter (1.9m) kusan a ido za ka ƙiyasta tsayinsa da wannan shahararren ɗan film ɗin ƙasar Indian wato PRABHAS. Tamkar ma bai san anyi ruwansu a wurin ba wanda ni anawa tunanin nama ɗauka bai gansu bane, domin kuwa typing nashi yake a system ɗin dake gabansa mai ƙirar apple da sauri da sauri yatsunshi kaman wani machine, Idanunshi nakan system ɗin har loƙacin kuma bai ɗago yakalli waɗan nan masu kama da samudawan ba. "Sit" Ya furta a dakile iyaka saman laɓɓansa. A nutse suka zazzauna fuskar nan haɗe tamkar tayi aman wuta tsabar haɗen da dake, daga haka bai ƙara ko kallar inda suke ba yaci gaba da sarrafa system nashi. saidai aka kusan kwashe sama da ten minutes kafin ɗaya daga cikin guards ɗin ya furta ”BOSS wannan ba abun ɗaga hankali ba ne. Har yanzu akwai sauran loƙaci dan haka zamu cigaba da saka musu ido kafin loƙacin ya cika!” Cikin rashin son ya magantu saida yaja wasu sakonni kafin cikin deep sound nashi ya furta " They are all going to taste my wrath Arielle!” cike kuma da fusata ya karasa faɗar maganar, wani kalan gajeren tsaki yaja har loƙacin bai buɗe idanunshi dake lumshe ba, kaman wanda magana kema wahala Kafin ya zuba baki ɗaya guards ɗin blue eyes nashi tare da folding hannunsa saman ƙirji kamar mai nazarin wani abu. Luuuuuu yaja kyawawan idanunsa ta cikin sun glasses in daya toshe nake iya hango su, fuskarn system ɗin dake gabansa ya juya musu, sosae razani ya bayyana saman fuskokinsu, amma kuma dake cikakkun maza ne yasa sammm basu girgiza ba, cikin wata kalan murya dake nan ada ƙile irin muryan nan na no nonsense person ba wasa kokuma fara’a yace. ”I want to see him in front of me in 24 hours” Fuskansa har wani bala'i kake iya hangowa domin ƙirjinsa har wani dagawa yake. ”Yes Sir.” Suka haɗe baki tare da sara masa suna barin parlourn baki ɗaya sai mutum ɗaya daya saura, "Sir there is something you need" *NO!" Ya furta a ɗakile tare da janyo plask na Black tea nashi zuwa gabansa a ɗan madaidaicin bowl ɗin dake gabansa ya tsiyanya wanda yake ta fidda turirin zafi ga kuma wani daddaɗan ƙamshin dake tashi na kayan haɗin shayi, duk uban turirin da yake amma shi ko a jikinsa haka ya shiga sipping abunsa hankali ƙawance. 1:40am ya tashi yana nufar upstairs nashi tsararre haɗaɗɗen benen ya shiga takawa bibbiyu, zuwa loƙacin gidan ya ɗauka wani irin shiru, babu motsin komai sai ƙamshin flower's ɗin dake ratsa ko ina na gidan, kasancewar mention ɗin kewaye yake da tarin shukoki na flower's color daban daban, kuma ginin gidan na saman ruwa ne sai wata iriyar sassanyarn iskar dake ratsa ko ina irin ta farkon damunar Nan. Siiiiiiii siiiiiiii siiiiiiii haka sautin iska ke fita. Few minutes sai gashi ya fito cikin wasu blue black suit inda ya toshe ko ina jikinsa babu abinda kake iya kallo dade da hannuwansa suna rufe cikin sos na hannu, sawayensa na cikin covershoe dake kyalli na tomford hannunshi daure da wani rantsatstsen wristwatch, Cikin takun isa se kace wani sarki yake taku, ko wanne lungo da sako na gidan na sanƙame da manyan escort wanda suka fi kama da samudawa, duk inda ya gitta sai sun Sara masa, amma ko kezau ba yayi kai tsaye ya nufi ƙaton parking space na gidan, wanda suke

Table of Contents

Chapters

54 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54