Chapter 18
Chapter 18
cewar a masarauta ce. *_EMAAR's EMARANCE MENTION_* Shine sunan dake walƙiya ta saman ginin DPY WELPAPER ɗin dake haskaka ginin da difference color's. A ƙa'idar wannan masarautar ba'a hong ko kaɗan. Wani ɗan ficik ɗin yellow'n card ɗaya daga cikin security'n dake cikin motar ya zira. Abin mamaki sai kawai Ross gold get suka raba tsaƙiya nan motocin suka sake danna hancinan motocin su da mugun gudun tsiya. Ya Ilahi wani irin Mahaukacin katon mention ne ya bayyana masu passage daban da daban. A bakin Ross gold get ɗin farkon wasu irin mahaukatan TIGHT SECURITY ne jibga jibga. Hannuwansu rike da manyan bindugu na tashin hankali. harabar gidan kanta tamkar gari guda ne domin girmanta abin azo a kallane. gashi qasan shimfide yake da kwalta ga flowers of different types shufke a gefe gefen titin. Haka suke wuce get na farko cikin uban sharara gudun nan tafiya mai nisa koko ince gudu mai nisa suka kafin su isa maid entrance ɗin gidan. Nan ma saidai Saida suka sanya wani card ɗin different da wance domin samm ma basu haɗa koda kama bane kana get na biyu ya buɗe. Ya Ilahi kai jama'a shi kanshi wannan gida ko ince masarauta yafi qarfin a ƙirata da SOLDIER'S HOUSE sai dai a ƙirata da HOUSE DIE. Eeeeeeehhhhhh mana tabbas kuwa house die tunda abinda idanuwana suka gano min kenan. A haka har Saida suka kai get na ƙarshe wanda a nan babban tashin hankalin yake. #tight security #Movel : mobile #Police interpol Kai jami'an tsaron da babu wandan da babu a cikin wannan shahararriyar masarauta, banda tarin kuyangain da suma sukama masarautar ƙawanya suka mata GARKUWA. A hankali wannan 2024 Toyota Highlander grand tai parking a dab da wani irin azababben flat Wanda yake zagaye da tarin barori na tashin hankali, fararen sawayensa ya fara zirowa wacce take sanye cikin lallausan takalmin fata irin na sarakai,kafin gangar jikinsa ta biyo baya. Ga hasken street lights ɗin da haske harabar wurin tamkar rana, hakan shine ya sake bayyanar da tsantsar kyawun da subhanahu wata'ala yamay kana ganin mutumin kasan ƙarshe ne wajan tsari da kuma iya ado. Tuni wannan tarin kuyangain suka shiga masa kirari cikin harshen larabci. Wani irin mugun kallo Zaid ya watsa musu Azafafe cikin tafiyarsa ta sanyi² zafi² ya juya kai tsaye ya nufi plat na mai martaba *ONOYIN* (sarki)..... _"OUMMIEYHHH?..... Ya faɗa da ƙarfi cikin ɗaga murya yana shiga makeken falon daya qawatu da kayan alatu ga tattausan carpet da duk takawa ɗaya zakaji kamar zaka nutse aciki don taushi da laushi ne. "OUMMIEY! ONOYIN أين هو بابا ن ياكي؟ " Ya faɗa da sautu me amsa amo. Sama ya nufa ya fara hawa stairs ɗin da shima kanshi abin kallo ne Kasancewar stairs ɗin irin mai lanqwasar maciji nan ne. Saida ya ɗauki loƙaci kafin ya isa. Wani qaton falon ya sake kutsa kansa ciki shima mai mugun kyau ya sake wuceshi sannan ya shiga passage din dazai sada shi da ɗakin oummiey. Koda ya qarasa ƙofar ɗakin oummie banda haki babu abinda yake yi don yasha ha gudu sosai gani yake tamkar elevator bazai kai shiba. Wata kyakkyawar dattijuwa na hanga zaune bisa tattausan carpet gefe kuma irin pillow dinnan ne masu kyau zagayayyu irin wanda akafi gani mostly dama na gidajen sarauta ne ta kishingiɗa akai, plate ne a gabanta cike da yankakkun fruits wanda take ɗauka da ɗaɗɗaya tana ci. Ɗayan gefen kuma shako mako ne, sai tea party, tare da mia piatte ga kuma milagro Saurin dagowa matar tayi ta kalli saitin data jiyo muryan hubby Inta hasken dake haskaka duniyar ta wato ZAID. (_Tsarki ya tabbata ga ubangiji mai talikai daya halicci wannan halitta mafi kyawu mai cike da haiba_) Na faɗa daga cikin zuciyata "Where is my papa? Oummiety!" Ya sake tambayar mahaifiyar nashi cikin cukurkuɗaɗɗen English nashi. Idanunta ta ɗan lumshe kafin ta miƙa mashi kyakkyawan farin hannunta, noƙe nashi hannun yayi a bayansa tare da furta. "Ohh ohh Papa na" ya faɗa cikin sakalci tare da noƙe kafaɗa. Da hannun tamai nuni da wani tsararren room wanda yafi kama da ɗakin tan garan Domin an kawata room ɗin ne da wasu shiles row glasses tamkar irin gidan lantarkin nan. A zafafe ZAID ke taka ƙafafunsa yana tafe yana fesar da numfashi ta cikin bakinsa kansa ƙasa yana tafe cikin sassarfa. koda wasa bai yadda ya ɗaga kansa ba bare ya kalli irin yadda uban kuyangain ke zubewa ƙasa bisu gwuiwowinsu. Shifa sammm koda wasa bai ƙyaunar duk wani abu daya dangaci sarauta ya tsani gaba ɗaya calture nasu komai a takure yake yinsa. So shi yasa sammm Allah bai haɗa jininsa da wannan sarautar ba shi mutum ne da yake son yayi rayuwarsa yadda yake so. Da wani irin sauri yakai gwuiwowinsa ƙasa tare da kafe mahaifinsa da lulu eye's nashi da suka sosae ganin yadda jikin PAPA'N ya koma loƙaci guda. "PAPA?" Ya ambaci sunan mahaifin nashi cikin wata iriyar raunatacciyar murya. Tare da ƙoƙarin kai hannunsa jikin PAPA'N shi. Da wani irin Mahaukacin mari yaji ya ɗauke kyakkyawar Innocent face nash, amma tsabar jinin sarautar dake yawo a gaba ɗaya ko wacce magudanar jini ta jikinsa ya sanya ko gezau be yi ba. "Kada ka kuskura ƙazamin hannunka ya taɓamin tsarkakken jikin ɗan UWA na" muryar 2wins ɗin mahaifinsa ya katse shi a kausashe a karo na biyu da yake kokarin sake kai hannunsa jikin PAPA'N shi bayan uban marin da MOH Ta bashi. Da wani irin mugun gudu *JESRA* ta kulle idanunta cikin kunar zuciya. A nutse Zaid ya ɗago da kansa zuwa ga baki ɗaya jama'ar parloun. EL-HUSSAIN wanda ya kasance biyunini PAPA'N shi, sai MOH JIDDO wadda ta kasance mahaifiyar su PAPA'N shi. MAHBOOB,DAWOOD, MUZAFFAR, MUSADDIQ, AL-MUSTAPHA, MANDOOD, EYESHA, MANSOOR ,REYNA. Sune a room ɗin baki ɗaya wanda mafi yawancin cikin su ke binsa da wani irin mugun kallo, kallo ne irin na tsantsar tsana suke binsa dashi. A...MALEEK..... Idan baiyi ƙarya ba kamar haka Papa ya ambata saman laɓɓansa ko takan jama'ar da suka ma room ɗin ƙawanya bai biba ya haɗe fuskarsa dana mahaifinsa sa. Ta ƙarfin bala'i ZAID ya furta "ABDOUL-MALEEK?" Wani irin razanannen kallo mafi yawancin ɗakin suka shiga bin ZAID dashi. _ABDOUL-MALEEK_ kowa ya shiga maimaita wa cikin zuciyarsa har jikkunan wasun na ɗaukar mazari, sunan da Ambatarsa kawai tashin hankali yake haifar wa, sunan da jinsa yake tada hankula bama hankali, sunan da suke ɗaukar sa wani shuɗaɗɗan al'amari a cikin tarihin rayuwar su. _Tasssss_ Wannan karon EL-HUSSAIN ne ya ɗauke fuskar ZAID da wani irin bahagon marin da dole ya sanya shi dafe kuncinsa. Kiiiiiiiiiiiiiii MANDOOD da yafi kowa na wurin zuciya haka yaja hannun Zaid ya kaishi har bakin door yana cilla shi woje. Cikin tafasar zuciya MANDOOD ya dubi Zaid rinannun eye's nashi ya furta. "Wannan wani shuɗaɗɗan al'amari ne, wata kirkirarriyar tatsuniya ce, sunan ABDOUL-MALEEK shafaffene a cikin tarihin wannan masarauta ka kula" Fuuuuuuuu ya kaɗa da niyar juyawa chark ya dakata jin wata mahaukaciyar dariyar da Zaid ya sheƙe da ita. Hakan ya sanya A tsananin fusace mandood ya ɗaga hannu zai wanke fuskar Zaid ɗin da wani wawan mari. Cak Zaid ɗin ya rike hannun nasa tare da cewa "Kada kayi wannan ganganci"
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54