Skip to content

Chapter 25

Chapter 25

Mikiya Book One Complete Hausa Novel 1,204 words 0 views Progress saved
Download Book

wanne irin laifi ta musu da suka zaɓi su jefar da ita? Tana son ta tambayi wanne irin mutane ne su masu son zuciya?_ _Ita kaɗai tasan abubuwan da suke cunshe a cikin Rai da ruhinta, wanda suka kusa tarwatsa zuciyarta ta buga ta dena aiki, domin tasan tana dab da bugawar. Badon Allah yayi ta mace me tsananin haƙuri da danne abu komi girman sa a cikin zuciyarta da tuni numfashinta ya jima da barin gangar jikinta..... A bayyane ta sauƙe wata nannauyar ijiyar zuciya cikin muryan da yayi low sosae ya furta. "Me yake damun DIDINA haka?" Kanta ta ɗago tare da kallon mahaifiyar nata cikin raunatacciyar murya ta shiga faɗin. ”Nima bansan abinda ke damuna ba Anne! Kawai dai inajin yanayin cinkushewar zuciya ne, da rashin jin dadin yanayin rayuwar ma baki ɗaya” ”Ce ALHAMDULILLAH domin Allah shine abin godiya a koda yaushe!” ALHAMDULILLAH ɗin kuwa ta furta tare da duk sauran adda'oin da suka zo mata. Ƙiran sallar asuba da aka ƙirane ya fitar da Anne a ɗakin bayan taci kukanta harta gode Allah. Ko Washegarin ranar Meerah kasa fita ko ina tayi, kayan karin tama har ɗaki Raiha ta kawo mata..........ita kuma ta wuce makaranta. Tana zaune a ɗaki Sai wajajen sha biyun rana kana ta fito verander inda ƴan uwanta aurarru suke zaune. Gaisar dasu tayi wasu sama sama suka amsa wasu kuwa arziƙin kallo bata samu daga gare su ba. Kwanciya tayi ba tare data nuna damuwarta akan rashin amsanta ba basu yi ba. Babbar yayarsu da suke ƙira aunty Zaheedah ce tace. ”guys na manta ban baku wani latest story ba" Shewa suka sanya a tare kusan su biyar kana aunty Sumayya ta furta. ”Bamu musha ƴer uwa” Saida tayi ƴar dariya kaɗan irin ta rashin mutuncin nan kan furta. “Kai Wllh na daɗe banga mara zuciyar mace irin zulaiha ba, Ata zaluntar mutum amma saiya nuna baimasan ana yimay ba. Kunsan a wayewar garinda Affan ya rasu sai dana sake banka musu ɗaki ita da Belle" ”Kai Wllh na daɗe ko'a littafin Hausa Novels banji me hali irin na matar nan, ayi yarinya sai kace me zuciyar takarda ko ma wacce bata da zuciyar a tsakiyar ƙirjinta” Aunty labiba ta faɗi tana gyara zama "Nake baku labari shegen kamar kullum ranar ma kasa tanka min yay saima rawar jikin daya fara min...... Ita kuwa shegiyar Wllh ko kallo na kasa yi tayi kamar dai ko yaushe” Aunty Maryam da tunda suka fara maganganunsu ce dama kuma bata ce musu komi ta furta. ”Innalillahi! Yanxu dama har yanzu Zaheedah baki dena wannan banzan halin naki ba?, Na cutar yarinyar mutane ta shigar mata ɗaki kina gane mata sirrin aurenta......Wllh kiji tsoron Allah domin ɗaurin talala ya miki duk randa Ubangiji ya tashi nuna miki ikonsa a kanta Wllh daga ranar zaki gane Allah ɗaya yake” "Huyummmmmmm me zuciya irinta marasa kan gado, ke dai kici gaba da zama a cikin duhun kai da bar abada bazaki waye ba" Cewar aunty labiba, shewa suka sanya mata nan fa suka koma kanta suna mata cin mutuncin da suka ga dama. Ni kuwa dake kwance a wurin tsammmm na miƙe domin kunnuwa ba rasuji gaba da jin zunufi ba. A cikin zuciyata kuma ina musu fatan shiriya duniya da lahira. ★★★ *ABUJA* Zaune take akan caution ɗin da yama ƙatataccen parloun ƙawanya, tayi zurfi sosae a duniyar tunanin halin da rayuwarta take ciki. Tana zaune cikin ƙunci na rayuwa da azabtar War kishiya. ”Zulaiha! Zulaiha!!" Shiru alamun tayi nisan kiwo a cikin kogin tunanin data faɗa. ”Zulaiha kodai kin sanya wata damuwar ne a cikin ranki?” Matashin mutumin dake kanta tsaye ya tambaya wanda a shekaru zai iya kaiwa irin Talatin da bakwai ɗin nan ko da shida. zamanta ta gyara tare da fuskantar sa sai kuma idonta suka ciko da kwalla. ”Yanxu Bello tambayana ma kake ko damuwar woni abu nasa a raina? Duk irin ƙalubalen da nake fuskanta a cikin gidan nan? Haƙuri na yana dab da ƙarewa Wllh na gaji- na gaji *NA GAJI BELLO!* Duk irin abubuwan da ake min woni a gaban idonka woni a bayan idonka amma kanzil ba zaka iya furtawa akan anyi min ba daidai ba” Ta furta cikin muryan kuka sosai da sosae. Kafaɗunta ya dafa cikin kwantar da murya ya shiga furta. ”Har abada ba zan gaji da cewa kiyi haƙuri ba zulaiha, ita rayuwar duniya ƴar haƙuri ce kuma duk wanda yayi haƙuri baya taɓa faɗuwa ƙasa....Ƙarshen ko wanne haƙuri nasarace, ƙarshen tsanani darajace, ƙarshen wahala ɗaukakace, ƙarshen jarabawa kuma Alkhari ne ciki gaba da zaman haƙuri dakai kukanki wurin Allah domin shi maji ƙan bayinsa ne" Daga haka ya saki kafaɗunta yay taku ɗaya ana biyu ta riƙo hannuwansa, Sai kuma kawai ta faɗa jikinsa tare da cusa kanta cikin ƙirjinsa rana fashewa da wani irin kuka me cin Rai. Tsammmm ya rungumata ya fara lallashinta,Saman sa ya nufa da ita tana cikin jikinsa. ★★★ Ayau wayar garin litinin zazzafan martani ya fito daga bangaren *AK* Wanda indai mutum masoyin media me to da wannan zazzafan latest news din ya karya. Ga abinda martanin ya kunsha na farko a cikin tiktok. Yana zaune a wani kayataccen palo ne wanda Wanda ya wadatu da komi na mo re rayuwa, sanye yake cikin shigar bakaken Riga da wando yayi covering duka jikinsa ko kwayar idonsa babu me Iya gani. Shi kanshi video'n don ka tabbatar dana musamman ne idan ka shiga kafin ka fara ganin komai said kamar 5 minute haka xuwa 7. Kafafun nan a harde kamar kullum cikin nutsatstsen sautin da yake fita cikin wani irin low voice nd sweet ya shi fara mayar da martaninsa kai tsaye. _Fusata ya kamata ace kunyi bawai nuna fushinku a kaina ba!. Kasancewar kun gane wannan shugaban da kuka zaba ha'intarku yake yi, akanshi ya kamata ace kun nuna fushinku sakamakon zabarshi da kayi_ _A yayinda fitilun titi suka dauke hanya ta cika shara da kuma tarkace, A yayinda ake wulakanta talakawa tamkar dabbobi a asibitin gwammanati!, cin hanci ya wanzu a kowanne ofishin ma'aikacin gwammanati anan zaku nuna fushinku. Me yasa ba baku nuna fushinku fusatarku a ire-iren wadan nan abubuwan?, amma a yayin da gurbataccen shugaba ya shigo hannu shine kuka harda fitowa wata zanga zanga? Kukayi kone-kone kuka har gitsa komai da komai a cikin ko wanne lunguna na wannan gari dama wajen garin?. Idan har wani iftilati ya faru daku ya kasance kuma kuna bukatar taimakonsu to amfani Duke wannan hatta shi wannan taimakon Right?. A wannan kasar shima talakan ba wani salihin bawa bane, shine ma hanya mafi gurbata a wannan fannin. Rashawar dake tattare da kuri'a itace ke bama shugabanni wannan ikon. A yayinda da suka zo suka raba muku wasu yan tsirarun abubuwan amfanin yauda kullum da bazasu wuce wuni daya ba. Shine kawai kuke zabarsu ba tare da tunanin menene abinda gobenku zata haifar muku ba. Sabo da rashin sanin yanci zarmammun cikinku suke dauraku akan ra'ayin da ba naku ba, domin kasa ta sanja dole sai talakan gari ya fara sanjawa domain kawar da rashawa da kuma son zuciya. *DON HAKA MU FARA SANJAWA.....*_ Kafin kace mene tuni media ta dauki hayakin bala'i domin wannan zazzafan martani

Table of Contents

Chapters

54 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54