Skip to content

Chapter 46

Chapter 46

Mikiya Book One Complete Hausa Novel 1,202 words 0 views Progress saved
Download Book

zaki majinginarsu. Ka sani shi marar jin magana sai ammasa hukuncin jaki yake ganewa. domin kawo gyara acikin al'umma kuwa dole sai wasu sunsha duka dole wasu sai sunsha jijjiga, maza ka dawo GARGA!!! Kai kadai ne mafaraucin da zaiyi wannan farautar” Wani irin fesar zazzafan numfashi yayi tabbas duk Wanda yake da hannu a poisoning na paah dinsa sai yayi dana sanin saninsa arayuwa. Babu ruwansa da wani yar uwa, dan uwa, dangi domin babu tsoro ba fifitawa ba kara ba alfarma ,zai hukunta duk wanda yake da hannu akan paisoning na paah dinsa. cikin suyar zuciya data ruhi ya Wani irin kaima glass di car din da yake shirin shiga naushi. nan take glass ya tarwatse. bai damu da ciwon dayajiba. Cikin dakakken sautinsa ya furta, “tabbas kafin suga bayan paah ni zanga nasu bayan oummu!!! rayuwar mahaifina bazata salwanta abanzaba! Saina wulakanta dukkan masu hannu aciki kosu waye su wlhy oummey numfashina fansa ne akan mahaifina!!”. Dole saida oum tacire wayar daga kunnenta saboda yanda Ak ke magana cikin matsananciyar tsawa. Buga wayar yayi da kasa batareda ya katse kiranba. Nan take ta tarwatse wata uwar tsawa ya dakama security'n akan suje. Gaba dayansu cikin rawar jiki suka nufi motocin da ke fake a wajen, ko jira abude masa baiyi ba yabude yashiga. Hankalinsu a tashe yake daganin yanayin boss in nasu, sunsan ba karami abune kesa ran boss ya baci haka ba. Saida suka fita daga gidan suka hau kwalta kana suke tambayar ina suka nufa?. Tamkar bazai tankaba sai kuma furta "airport" dake arms yana cikin dayar motarne ya sanya baima san abinda ake ba. Sai dayaga sun dauka hanyar airport din ne ya gane tafiyan nasu ashe na yanzu ne. Domin dama tunda yayi waya da zaid ya shirya tafiya amma sai washe gari. Cike airpot din yake da tarin security na tashin hankali tamkar irin wanda suke gadin gidan mutuwar nan. Sanya yake cikin normal cashmere me tsananin taushi da laushi wanda tsadarsa yake a baiyane, kafafunsa sanye cikin wasu tsadaddun shoe cambot bleim. Kasancewar yau babu komi a face nashi hakan ya bayyana hasalin kyakykywar fuskansa ga jama'a kai tsaye. Nan securityn suka shiga bashi wani irin tsaro na musamman. ★★★★ A hankali Maleek ya ɗago manyan idanunsa tare da kallon taswirar kasar sa da suka iso tsakiyarta. Haka nan yake jin wani irin abu a cikin jinin jikinsa. Ji yake tamkar ya tafi yabar wani abu mai muhimmanci nashi ne a kasar ta 9j. Numfashin mai sanyi ya fesar tare da ƙkara ware manyan idanunsa yana jin yadda zuciyarsa ke hautsinawa bugunta na sake bugu. Misalin karfe sha biyun dare Jirginsu yayi saukar angulu a cikin babban Airport din kasar kuwait. Din na Hammad international airport. Da sauri arms ya kalleshi sai kuma yayi sauri ya mayar kallonshi gefen damanshi ganin har an buɗe ƙkofar jirgin. A hankali ya fesar da sassayan numfashi dai-dai lokacin daya fara taka step na forko wanda ya fito da kanshi sararin garin kuwait yana shakar yancin iskar kasarsa. “Yah Salam” Ya furta Sabida wani irin ni'imtaccen iskar kasar sa mai dadi mai cike da salama da ke ratsashi yana shiga duk ta inda hudar gashin jikinsa yake. Wani rin amintaccen numfashin mai cike da yanayin sauke ajiyar zuciya ya shaka like irin Wanda baya tare da natshwar nan yau kuma ya samj cikakkiyar nutsuwar. A hankali yaci gaba da taka steps din yana sakkowa kasa. Wani saurin runtse idanunsa yayi lokacin da ya dire tafin ƙkafarsa akan kasarsa. A take yaji naman jikinsa na wani irin tsuma tun daga can cikin jikinsa da zuciyarsa yakejiyo wani irin abu na kokarin fusgar numfashinsa. "Subhanallah!" Ya furta a saman lips inshi yana karasawa ware eyes nashi sosae akan kasar sa. Bawai baya zuwa bane yana yawan zuwa kasar saidai zuwan yana kasancewa na sirru ne. Dan baya cikakken 5Months bai leko kuwait din ba. Wasu shegun hadaddun dunkulallun luzury car's ne suka kutso kansu cikin airprt din. Wanda ko wacce bayan mota me makaon lamba dauke suke da sunan *GARGALION*. Ba'a taba ganin mitocin idan harba mamallakansu ne yaso a gane hakan ba. Duk wata shekarar da zata shude tana shudewane da duk samfurin sabuwar motar data fito na GARGALION din. Wanda kai tsaye kowa yasan mamallakin sunan. Zaid ne da kansa yazo daukar biyuninsa airport din ba tare da sanin kowa ba a cikin masarautar. Da yar sassarfa zaid ya karaso tare da hugging dan uwansa hana sumbatar shi a goshi. Tare da fadin "Ur well come 2 u in my country twin" Dan bubbugawa bayansa Ak yayi tare da furta "Well come back againt daya na" Sake hugging nashi zaid yayi kana ya isa ga arms daya kasance amini a gareshi shima yayi hugging nashi. Sake hugging Ak yayi kafin su nufi wurin dunkulallun motocin dake jiransum Da sauri daya daga cikin tight security's din wanda ke gefen damar motar ya kai hannu jikin handle din ƙkofar ya bude Ak. A nutse ya fada cikin motar kana sauran suka shishshiga, saida fadawan suka tabbatar da cewar ya rigada ya shiga kafin su shiga wani irin busa sarewar dake ma duk wani mahaluki cewar GAGALION ne a wurin. Domin busar da ake may ta daban ne irin me sanyin nance dake ratsa zuciya ya tsuma namomin jikin dan adam. Wani irin lumshe ido yayi tare da budesu a firgice wata sabuwar izza da kasaita na zuwar masa.nan fa hankalin duk wani dake cikin airpot din yayo kansu duk da kasancewar tsakar dare na, amma sukam babu ruwansu wasun suma su yanzun shine rana a garesu. Mandood dake daya daga cikin jama'ar airpot dim shima hankalinsa ba karamin tashi yayi ba. Su kuwa jama'ar sauran airpot din kowa kokarin gani yakai wurin tarin car's din, saidai security's sun hana hakan ta hanyar bashi garkuwa. Mirza kan lafiyayyun motocin suka yi kyakykywan kwaltan airport din har zuwa EMAAR's MENTION. Cikin tafiyar da bai wuce 50 minutes ba suka iso gaban katon get din masarautar, katon screen welpaper odysss na mention din na welcome nashi. Dauke da full name nashi shudaye da jajayen da blue din abubuwan ke zana sunan ak din. A get na farko, nu'urar dake tantance mutane ce ta tantance motar kana suka danna get na gana duk inda suka gilma sai kaga kowa a yanayi na kamewa da zuke numfashinsu na dan wani lokaci. Da wannan kaifaffan eyes din nashi yake bin ilahirin masarautar din da kallo. Haka suka dunga shige get get ko wanne da kalan nashi tarban da sukema Ak din. Shi kuwa yana hakimce cikin tsumammiyar lafiyayyar kujerar motar ya nutse, sanyi da mayen kamshim sa na dada sanyi shi yin relax acikn kujerar mortar. Gefe guda kuma daddadar kira'ar Afif muhd taj na tashi. Nan din ma daya daga cikin bafadawan ne ya fito yana bude mai motar tamkar mai gudun tashin yaro a barci.A kalla saida aka kwashe sama da awanni goma ciff be fito ba, kana aka sake dibar wata gomar kafin almurin bakin takalmin shoe combat dinsa mai adon golden ya sauka saman maroon carpet din da aka shimfede masa ahankali. Sai da aka sake jan wasu sakannin kamar uku kana dayar kafar ma ta sauka sky blue

Table of Contents

Chapters

54 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54