Skip to content

Chapter 26

Chapter 26

Mikiya Book One Complete Hausa Novel 1,207 words 0 views Progress saved
Download Book

na ABDOUL-MALEEK AK tuni ya baza ko INA. Har wasu na mai dashi rubutu ta hanyar copy suna dorawa irinsu Facebook, Twitter, Instagram, telegram dadai saurinsu haka gidajen radio suma suka ringa maimaichin abun kamar ba gobe. Sai yanxu hankalin mutane ya fara dawowa jikinsu. Tuni hankalin jami'ai kuma ya tashi da wannan ballo ruwa da AK yayi Wanda suka rasa ta inda zasu toshe hakan. Hankalin duk wani Dan siyasar dake Nigeria a tashe yake da ganin wannan video, tuni jamaar dake kiran AK da criminal suka dawo girmama koda jin sunan shine. Saidai amsa daya da ko wanne mutum ke dokon jira a jirace shine bayyanar ak a zahirance. Da kuma asalin kasar shi da inda yake zaune domin kuwa kallo daya mutum zai yi masa yasan cewar shiba mutumin NJ bane, ko daga yanayin zancenshi da baya idasa fita duka. Wannan Abu shine yayi sanadiyar takawar shugaban kasa har xuwa Lagos. Inda suka tattauna da manyan Jami'ai da kuma wasu kuso shin gwommanatin dake mulkarmu ta karkashin kasa...... Meeting din gaggawa suka shirya tsakanin masu ruwa da tsaki a cikin tafiyar. After like 50 minutes haka suka shirya meeting ɗin gaggawa cikin wani haɗaɗɗan building mai haɗe da wani ƙaton hall acikinsa, coutions ne acikin sa na alfarma wanda hall ɗin yaji kayan mo re rayuwa, ko ina stainding A/C ne manner a wurin sai sanyayyar ƙamshi da kuma fitar numfarfashin jama'ar da wurin ya tara ne ke tashi. meeting sukayi me sunan meeting Dan sai dab da magrib suka tashi suna ta faman kulli da warwara, ahaka har suka sami mafita kana kowa ya kama gabansa bayan zaida mafitar da suke ga itane kadai mafitarsu. Kwanan Armstrong hudu AK yayi dirar miki a boyayyen wurin da suka boye shi ta hanyar footage din dake cikin karkashin harshensa. Tsaro sosae akama wurin duk don kaicema samin kuskure,amma hakan bai hana ak bayyana a gabansu ba. A lokacin su Mr President, Ajmaal, Isa manu, dadai sauran manyan kawunan suna a cikin setrest din ne don sun fitar dashi a station din ma baki daya. Suna kan azabtar da Armstrong Woyar dco ne yayi kara hakan ya sanya shi dakatawa da bugun Arms din. ”What AK kuma?” Ya fada a zabure har yana kokarin hantsilawa saida Ajmaal yayi saurin taro shi tu kuna ya daidaita tsaiwarsa. Wani matsiyacin kallo Ajmaal ya jefawa arms. ”Ta Yaya yasan kana a wannan boyayyen wajen?” Ya fada yana shakar arms din. Wata shegiyar dariya arms ya saki tare da furta. ”Ku a dakikin tunaninku da kunyi haka ne don boye ni daga BOSS?” Ya fada cikin wannan dangerous voice din nashi. ”ANSWER MEE ARMS!” Ajmaal ya sake maimaitama arms tambayarsa. Dariya ya shiga yi kafin ya furta ”footage” ”Karya kake arms babu camera a jikinka nida kaina nayi check out naka!, don haka ka bani amsana a karo na karshe” ”Shi yasa na CE duk cikin Ku babu Wanda Zan kira da *JAN WUYA, duk kaninku ”KOLAYE NE” Ya fada yana daga harshen Sa tare da sanya shi tsakanin seen da tongue nashi ya turo musu Yar karamar camerar. Duk cikin su babu Wanda be razana da wannan basirar tasu ak ba. Ehhhh dole suce basira mana amma sai suka waske abinsu.... Few minutes Zaune yake zama irin na harde kafar nan. Akan kujerar da Isa manu ke kanta a da a yanxu kuma ta dawo da ak din. Fuskarnan tamkar tayi aman Wuta tsabar tsananin fusata,A fusace Ajmaal yayo kan ak duk kuwa da yadda Mr President ke kokarin hana shi amma be hanu ba. ”Kaida kazo da sunan kwatar yaronka to kasani kazo nan da sunan mutuwarka ne!,, A wannan rana a kuma nan wurin idan har ban dagarzaga kasusuwanka to na rantse ni ba namijine” Wani Dan iskan kallo da ak ya watsawa Ajmaal ne ya sanya jikin Isa manu ya soma karkarwa,shi da ba shi aka ma kallonba. Wani irin gyara zamansa yayi ya sakko da kafarsa daya dayar kuma ta na kan kujerar da yake kai. Ya dora hannunsa saman kafar like irin kasaitaccen basaraken nan. ”Ko wane mafarauci gwarzone har sai sanda ya fuskanci ingarman zaki. Ba kamar kai da rundunar jami'anku ba!, bana da runduna bana da tsoro a jikina bare naji tsoron mutuwa. *TUN A HAIHUWATA NACI GALABA AKAN MUTUWATA_*” Ak ya furta kalaman tare da wani iriin doka hannunsa akan kujerar da yake zaune a kai. Kalaman da suka kusan zauta yar karamar kwanyar duka jama'ar dake setrest din..... A zuciye wani da suke kira da tonfal babban yaron su Isa manu yayo kan ak, da wani irin salon daukar hankali ak dake zaune ya sanya kafarsa tun kafin mutumin ya karasa ya sarke kafarsa. Ji kake rigifff mutumin ya zube kasa ba tare da ya ko motsa ba. Cikin kankanin lokaci ak ya sissince arms dake daddaure ya tafi dashi a gaban idonsu ba tare da sun Iya dakatar dashi ba haka suna ji suna gani ya sabi arms a kan shoulder nashi yabar wurin dashi.cikin wannan takun NASA me cike da bajinta,hadi da mazan taka Wanda kallo daya idan kai masa sai hantar cikin ka ta kada..... ”Kai wannan yaro anyi dan tsinanne, kasa sai kace ta uwarka kazo ka zame mana fitina tare da hana mu rawar gaban hantsi” Isa manu ya fada bayan daya tabbatar ak dade da barin wurin. Ajmaal da gefen kunnansa ke digar jini ne Wanda ak ya bashi rabon shi. Cikin tsanin bacin ran ya furta. ”Stoppp” Da karfin masifa ”Na gaji dajin koda me irin sunan sane” Sai kuma ya dago ya kalli Mr President ya furta. ”Sorry sir. Duk ba laifinka bane da alokacin da na d'ana kunamar bindigata baka tsayar dani ba ai da tuni saida wani bashi ba!, amma ka dakatar dani” ”Babu dai kai ba shiba!” Tonfal ya fada Wanda babu jimawa ya farfado daga mutuwar wucin gadin da yayi. ”More bit never get one choice but if we take a maximum change we get a big choice” Mr President ya fada yana gama fadar hakan ya fice a wurin... A lokacin da akai wannan darbarwar salman yana kasar India yawan shakatawa tare da wayayyun yan matansa. ★★★ ”Mommy Wllh duk inda yake a fadin duniyar nan saina dau fansar Jinin mahaifina da yayi, sai nayi sanadiyar barin numfashinsa da gangar jikinsa kamar yadda yaso raba nawa mahaifin da nashi!” *FAROUQ AUDU BASHASHA* kenan da ga audu bashasha shi kadai ya haifa a duniya.Shi yasa yaron ya taso cikin wani irin sangarta da tabara, Duk inda ake neman wani teteros to in akace maka Farouq fakat kenan. A yanxu haka Audu bashasha yana kasar India wurin kwararrun likitoci don kula dashi. Ashe be mutu ba da sauran ranshi lokacin da ak ya fasha kansa, Sun boye hakan ne domain gudun bacin sunan Sa, shi da kansa shine ya dauke RIYYA, ya mata wani irin mugun boye mahaifiyarsa kuma irin muta nan ne da sammmm babu ruwansu da duniya. Itace ma dalilin daya sanya ta hana. Cikin muryar da yake cike da tsantsan sarauta Hajiya Khadija suraj sunusu shureim ta dubi Dan nata Tare da furta. „Idan har Jinin dake gudana a cikin naka Jinin nawa to ban amince maka ba” Ta

Table of Contents

Chapters

54 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54