Skip to content

Chapter 50

Chapter 50

Mikiya Book One Complete Hausa Novel 1,200 words 0 views Progress saved
Download Book

kanta tana komawa inda ta fito, shunenta maman affan ta mata ai kuwa ta tafi zata fusgo Anne. Wani irin juyowa Anne tayi tare da watsa mata wani mugun kallon daya sanya maman sury jan burki daga shirin fusgar da taso yima Annen. Tsananin kwarjinin da idanuwan annen suka mata ne ya sanya ta hadiye sauran maganganunta, tana kama kanta cikin muryan da baya daukar wargi ko wanne ta furta. "Idan har kun isa da danku kuje gida ki hana a daure aurensa da DIDI!, jinina yafi karfin a wulakanta shi haka jinin Ayshatul humaira ba daskararren jini bane jinin dake gudana a jikinta tafarfasa yake ya tafashensa yake. Tafi karfin ta hada zuriya da gurbat..... Maganar ce ta yanke mata sakamakon rufe bakinta da hajiya umna tayi. Ita kuwa sury tuni ta makale jikin mummynta haka nan ta tsinci kanta da shakkun matar ba karamin kwarji ta mata ba. Daya bayan daya matan gidan suka fara zamewa domin su kansu ba karamin gwarjini Annen ke musu ba barin ma idan halinta najin kai ya tashi. Su kansu yayanta wani bin sai su wuni ba tare da kalma daya ta shiga tsakaninsu ba, wannan halin nata kuma ba karamin tayarma da malam abdullahi hankali yake ba. Jan hannunta umma tayi suna komawa parlournta. Nan ta shiga bata baki amma samm taki tanka mata ita kanta tasan wannan gwamutsen hadin auren ba son shi take ba, to amma ya ta iya. Ta kasance matar da bata jayayya da hukincin ubanhiji in banda haka ko ita da tuni ta farke wannan auren da take ganinsa kamar ba tabbatacce ba har waye war garin yau din. Har yamma hajiya umma na gidan.... Bangaren meerah kuwa haka tayi wunin sukuku gashi ba damar fita bare ta dan fita ko ta samu full energy nata ya dawo. Ta hanyar shakar iskar wage, abincin da tun dazu Anne ta tura mata take ta faman jagwalgwalawa, ita bata ci ita bata dena jujjuya shiba. Har saida hajiya umma ta fasu ta furta. "ya abincin gabanki tun dazun kinki ci sai famar jagwalgwalashi kike?. Meye haka kike yi da abincin nan meerah?" dago kanta tayi ta kalleta Itama Anne sai ta maida attention dinta kan meerah din. Wani dan murmushi ta saki irin me ciwon nan kafin a hankali tace. "Umma kinsan dazu da yamma na ci Wannan abin sam bana wani jin cin abincinne kawai na ji yanzu bana jin yunwar ma" "Toh idan baza ki ci ba ki rufe anjima kyaci" tashi tayi sai kuma jiri ya dibeta ba tare da kowa ya lura da hakan ba Kawai sai faduwarta suka ji. Da sauri Anne ta nufeta tana jijjigata, dakatawa tayi sai kuma ta juyoo da kallonta zuwa ga hajiya umma tare da furta "Bata numfashi" "Subhallah dama ba jiri bane ya dibeta?". Hajiya umma ta fadi tana yin kan meerah din " Maza kira malam ki sanar dashi Ayshatu" hajiya umma ta fadi cikin kidima domin ba karamin tashi hankalita yayi ba. Cikin kankanin lokaci saiga malam tare da Ibrahim babban dansa. Fito da ita sukai suka sanya a mota suna nufar hospital drektly.... A hankali take bude idanunta da sukaimara masifar nauyi, dan motsa idanunta tai tare da dan cije leɓe kadan. kafin ta samu nasarar bude ido da ƙkyau. "Asibiti kuma?" Ta ambata a hankali tana dan waige-waige da kallon dakin data bude ido ta ganta cikin bazata. Nan komai ya shiga dawo mata sai kawai ta koma tana jingina da jikin gadon, lokacin wajen goman dare. "Meerah ashe kin tashi ma?" Hajiya umma ta fadi tana komawa don yin magana da dactor. Tunda Anne tana gida babu jimawa hajiya umman tace taje. Ba don taso ba ta tafi tana tunanin damuwar da ake taima didinya yawa da kuma yawan tunani. Sai gasu ita da nurse ta dawo sake aunata nurse din tayi nan tace ma da umman babu wata damuwa insha allah zuwa safe ma zasu basu sallama. "Zanyi sallah ummah" Meerah ta fadi cikin muryan da yayi low sosae. Da taimakon Umma ta sakko a gadon sai yanzune ta kuma fahimtar a daki na musamman take, kuma ita kadaice a ciki hakan ya sanyata kallon umman da alamun tambaha. "Bamusan wanda ya sanar masa ba muma kawai ganinsa mukayi yazo ya sanya an sanja miki daki" dan lumshe ido tayi tana jin ma sam.. Bata son ci gaba da zaman hospital din. Sallan magrib da isha'i ta kawo tana koma ta jin gina kanta da karfen gadon. Sallamar salman din itane ta katse mata rufe idon da take niyar yi. Hannuwansa rike da manyan ledojin shopping ya shigo. Gaida umma yayi ts amsa tana tsokanarsa da angon kwana biyu. Dan murmushi yayi yana shafar sumar kansa yana jin wani irin madararn dadi na lullebeshi. Don ji yake tamkar ya jawo wannan kwanan biyun su dawo yau, kamar ya janwo nesa kusa haka yake ji da yana da damar hakan da tuni ya dawo da nesansa kusan sa. Kodan muradin wannan lafiyayyan jikin da yake ya kwadaitu sosae da sosae da tsarin halitta da kuma surar jikinta. Kallo daya ta masa ta dauke kanta shine ya gaida ta tare da mata ya jiki ciki² ta amsa. Nan ya shiga yar firarsa da umma domin gwanar tamu taki ko saurarensa. Kiran wayar sa friend's nashi suka yine akan sun sauka lafiya suna airport yazo ya dauke su, shine ya san yashi masu sallama yana cema umman abokanan sane suka zo domin tun gobe juma'a zasu fara shagwalgulan bikin. Yama so ace tun laraba suka fara amma malam da kanshi ya dakatar da hakan. Domin ya kawoma meerah katunan shagulgulan ne d nufin ta rabama friendies nata, wannan shine dalilin dakile maganar da malam abdullahi yay, ba tare daya sani ba kuwa haka salman da manyan abokanansa suka kama manya manyan hotels dake garin lagos dim suke abinda suka ga dama. Ta hilton hotel yabi ya taho da wasu domin debo manyan friends dinsa. Ajeborters na waje sa sauran garuruwa, a lokacin dayay ido biyu da dolly ba karamin baci ransa yayi ba domin idan ya tsani abu ya tsane shi kenan. Haka idan yaso tofa ya so shi kenan da dukkan zuciya da ruhinsa. Cikin kaushin murya ya kalli moussa yana fadin. "Kaine kazo da wannan abin ko?" Ya fadi yana masa nuni da dolly wani kafurin murmushi dolly ta saki tana " hey beb baka happy da zowa na ba kenan?" Tana shirin rungume shi ya ture ta a jikinsa yana fadawa motarsa yana fadin. "Le's go guys ku muje ko?" Sauran motocin suka shishshiga suna barin airport din tare da kama hanyar hilton hotel dasu.. Tun da suka shigo harabar hotel din suka soma jiyo tashin sautin Wakar da aka sanya din. Irinta shegen nan wanda suka rike a harkar tantiranci. Tab katon harabar inda suke yake da wayayyun matasa da yan mata 'yan bana bakwai,wadanda rayuwa da kuma duniya ke musu dadi suke cashewarsu cikin kwarewa, wasu babu kayan arziki a jikinsu mafi yawan mazan kuma gajerun wanduna ne a jikinsu. Hannuwansu dauke da manyan kwalaben giya wasu cigarette's ce a hannunsu suna busa hayaki. Wasu kuwa pep na shisha ne a ganansu suna zuka su fesar da hayakin cikin

Table of Contents

Chapters

54 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54