Chapter 53
Chapter 53
alwular muka gabatar da sallar la'asr. Bayan mun idar aunty baby ta shiga tsara min kwalliya a fuskana duk da banso hakan ba. Gashin kaina da shi kansa nasa gyaran na daban ne aunty baby tama wani irin style. Ta raba shi biyu ta kai har karshen ƙeyata wanda ya sauka har gadon bayana wasu shegun style ta shiga yi da gashin. Saida ta kammala kana ta sake nado shi da ribom's. Wata fitinanniyar riga da sket half bubu na wani shegen luxury catton less, irin me haɗe da jakar nan ta tamarmi sai mayafinsa. Wasu shegun barima me kama da diamond ta sanya min tare da zobenta da agogon hannu. Ya subhanallah a take wani irin kyalkyali ya shiga tashi a jikina. Ga wasu Mayun turarukan da ban taɓa jin koda irin ƙamshin su ta shige ɓarinsu a jikina. A take dakin ya ɗauki sowar kawayena jan hannuna aunty labiba tayi tana faɗin ALHAMDULILLAH sai gaban Anne da baffa har dama wanda basu so ganin wannan babban rana ba, namu ba irin nasu bane. Ina sanyo kafata tun bai kai ga fitowa ba duk wata jama'a dake tsakar gidan suka zubo idanuwansu a kan bakin kunshin daya wani irin sake fidda kyawun kaɗana. Kwallace take kokarin zubo min ganin tabbas waɗan nan mutanen sun taru ne a yau domin ni, hannuna aunty labiba ta janyo tana karasa fiddo ni zuwa tsakar gidan. Wani irin tsitt duk hayaniyar data kacame gidan a ɗazun sukayi. Ko wanne idonsa na kaina, harda masu sake mitsirtsike idanuwansu. Wata babbar guda Hajiya umma ta saki tana cira hannuwana sama tare da sake ranbada gudarta tana faɗin. "ALHAMDULILLAHI! ALHAMDULILLAH!! ALHAMDULILLAH!!! Yarinya tayi goshi Ubangiji ya baki zaman lafiya tabbatacciya a gidan aurenki MEERAH, Allah ya kare ki daga dukkan sharrin masu sharri. Allah ya tsoka ne idon makiya akan wannan auren da Allah ne ya hada shi, bawai mutum ba saidai Allah Wllh kuwa mutum din zaija da ikon Allah to bismilla!" Duk wannan abin ciki daga murya Hajj umma tayi nan fa wasu suka sha jinin jikinsu domin kaff ya'yan baffa mata babu wanda yaba Anne ko gudun mawar nera biyar. A cewarsu a gudun mawa karin ƙarfin biki. Nan marasa kunyar cikin su suka shiga amshe Hajj umma suna shiga tare da jeruwa da meerah ɗin aka fara buga photuna na garari. Babu kunya Anne ta rungume DIDI'ƊINTA aka musu photos da yawa. Nan manyan yayye maza ma suka shigo akaci gaba da hotunan Raiha ce nanuke da meerah duk inda ta yi cikin tata shigar na cotton less. Nan fa gida ya sake ɗaukar hayaniyar data fi ta ko yaushe kawayena kuwa sunyi cannn ta bayan kewayen gidan sun kafa party tare da shan disko harda mardiyya da bama shiri, dake dama rashin shirin akan hayatuddeen ne saita sauke ta shigo ake shan shagalin da ita. Wajajen sallar magariba kawaye suka fara mitar basu ga ango yazo ba bare ayi zancen photo dake baby na tare dasu sai tace musu ai suma suna da party'n da suke yine da an daura auren shi yasa bai zoba. OHO nidai bansan abinda ake ba domin ina cennn ɓangaren baffa wani zazzafan zazzabi ya rufe ni tun ina dauriya har Saida ya kaini ga kwanciya. Nan baffa kuwa ya sameni da nasiharsa na komai naga ni a lamarin aurena tabbacecce ne tun daga rabbi izzati, karna yadda nayi jayayya da hukuncin da Allah yay min. Kana karna taɓa butulcema zabinsa na zama mace mai tsananin haƙuri da biyayya a gidan aure na Insha Allah zanga sakamakon auren nan ko bayan babu ransa. Abinda ya sake sanyaya jikina kenan sai kaina ma ya soma sara min. Ana idar da sallar magariba ƴan daukar amarya suka zo, tun kamin suzo nake wani irin kukan daya sanyaya jikin kowa dake gidan, kira nake Ni Wllh nama fasa wannan Auren dama ai banaso don karnama baffa musu ne ya sanya ni amincewa toni Wllh na fasa. Nan na tayar da hankalin Anne'na da baffa dama duk wani masoyina, wata irin nasihar dahar nabar duniya bazan taɓa mancewa ba Anne na tamin haka ma baga Hajiya umma ba, domin nasihace irin me ragargaza zuciya harma da ratsa gangar jiki. Nidai kuka na nake a haka har dangin ango suka zo tafiya dani. Nan fa na ce bansan zance ba na rike hannun Anne na kakam ina risgar kuka. "Ki sani wannan tafiyar itace mabuɗin bude abubuwa da yawa meerah! Bawai kuka nace kimin ba jarum taka yaka mata ki nuna, yanxu an dena kuka dan anyi aure. Bare ma ki sani naki auren yasha banban da saura, Ki nuna musu ke kibiyar ajali ce wacce sulke baya iya ratsata! Ki nuna musu kedin jinin da........... Wata farar dattijuwoce tayi saurin damkar hannuna da nata lallausan hannun, wanda ya hanani karasa jin me Anne na take nufi a gaban da ɗin nan?, Motocin da baka ganin iyakarsu wanda tsadarsu kaɗai kan iya juyarma dame ƙaramar ƙwaƙwalwa kai. Cikin kuka nake don haka ban tantace ya kamanni da kalansu yake ba nadai san ban iya hangar iyakarsu. Kar kuce wai bana lura a ah ina lura da komai domin idan naji ana magana har wani sake leƙo da kaina nake. Da bismilla wannan matar ta sanya na shiga cikin wata narkakkiyar Toyota Highlander 2024/2025 bugun American. Ido a rufe yake amma sanda kamshi da sanyin daya ratsa ko ina na jikina ne ya tilas tamin buɗe jajayen idona da sukaci kuka.kallo ɗaya nama motar na furta. "Allah ya isanmu" na faɗa kasa kasa ɗan nasan da kukaden mu talakawan kasa aka siya wadan nan shegun motocin. ★SALMAN POV★ Sabo da tsabar farin cikin da yake a ciki jinsa yake tamkar an yimay bishara da gidan aljanna, wai yau shine ya mallaki meerah a matsayin matar sa shi kuwa me yafi wannan daɗi a duka cikin tarihin rayuwar sa. "BABU!" Ya fadi a fili lokacin da jerin abokan sa suka yo masa rajiyar angwaye. Haka ya kemashe idanunsa yace babu me shigar masa gida wai shi a matse yake don haka kowa ya kama gabansa. Nan fa suka shiga masa tsiya suna cewa zasu rama ne. Shi dai bai damu ba kansa ya mayar da get ɗin gidan ya rufe dan yasan zuwa yanzun kowa ya kama gabansa. Har wani sassarfa yake haɗawa da ita wajen isa ga muradinsa meerah wacce kullum sai yayi mafarkinta suna sheka soyayyar su... Jiki har mazari yake sanda ya ƙarasa shigowa palon gidan da yaji wasu shegen kujeru na alfarma. Da dai yaga saurin kamar bazai masa ba sai kawai ya kwasa da gudu sama kai bedroom ɗin daya tabbar da anan aka ajje masa amaryarsa ya tura. Tana zaune cikin lullubinta har yanzun kuwa ga wani kamshi dake tashi daga jikinta, wata kakkaurar ijiyar zuciya ya saki yana jingina da jikin kofa domin gani yake kamar bazai zo yagan taba. Amma yanzu ALHAMDULILLAH hankalin sa ya kwanta. Ajje ledar da abokanan sa suka bashi yayi saman stool. Zama yayi kusa da ita ba tare dako sallama ya mata ba, kai tsaye ya sanya hannunsa yana janye lullufin fuskarta zuwa kan shoulder nata. Wani irin zabura yayi yanaja baya idanunsa na firfitowa wanda suka bayyanar da tsoronsu
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54