Skip to content

Chapter 10

Chapter 10

Mikiya Book One Complete Hausa Novel 1,193 words 0 views Progress saved
Download Book

ciki matuƙa wajen zaɓarsu da kayi duk da bamu san dalilin ka nayin hakan ba, duk da bamu san waye shi ba" “Barkanmu tare fatan Alkhairi ma duka jama'ar dake sauraraen wannan shirin!" "To masu kallo zan iya cewa duk sai ku sake matsowa gaban akwatinan talabijin naku, masu rediyo su ƙara sauti domin ji daga bakin babban baƙon namu da musan waye shi ba!” Sai kuma na sake juyowa garesa tare da faɗin, “Ko zamu iya sanin cikakken sunan ɓoyayyen baƙon namu?” Wani irin kafirin murmushi ya saki irin na gefen bakin nan, Cike da wani salo ya sake harɗe ƙafafunsa da yay crossing cikin motsa lips ɗinsa kaɗan ya furta. “ABDOUL-MALEEK KUWAIT" “to Saidai kanmu ya daure da sunan baƙon namu, gashi kuma bama iya kallonka kai tsaye, duba da cewar kazo mana da batu ne akan wannan babban CRIMINAL ɗin Wato EAGLE, wanda ya kasance cikin aikata tarin ɓarnuka marasa ƙyau, wannan shi yaja hankulan masu bibiyar wannan tasha ta zamani tv jin batu ne akan CRIMINAL ɗin da ake nema ruwa a jallo!" Wata zazzafar iska ya fesar daga cikin bakinsa na wasu sakanni sannan yay wani ɗan murmushin gefen baki, a taƙaice ya furta, "Kai tsaye ki ɗauka kina tare ne dashi wannan babban CRIMINAL ɗin da kowa ke nema ruwa a jallo" Manyan Idanunta da suke kama da na mashayiya, uwa uba tsarin halitarsu da girman da suke ta ware baki ɗaya, tare da wani irin zaro su Wanda har saman fattar idon Saida ta ɗan kara faɗi kadan. Tana tsare shi dasu tamkar irin me tuhumar nan nasa, A nutse ya zare baƙin sun glasses in daya manne fuskar sa dashi, tare da kafe ta da nashi manyan Idon wanda kana kallon su zaka so fara kawar da dubanka, dan ba irin idannuwan da ake tsatsarewa da kallo bane, ga wani ruwa ruwa mai nuni da cewar Saida aka shawu kafin a fito,wanda ba dan ta kasance mai tsaurin ido ko mai taurin kai bane da taurin zuciya babu abinda zai hana ta kutsawa a gujeeeeeeee. hasalima ana ƙiran da farar kurane amma Halittarta mai bayar da tsoron ce ita ma Farar fuskarta dake ɗauke da kwantaccen gashi a gaban goshinta, wanda lafcecen hijabinta bai hanna su bayyanuwa, A hankali ta sanya hannunta mai ɗauke da awarwaraye na roba irin masu kyallin nan kwaya biyu pitch color ta shiga mirza saman goshinta irin tana cike dashi ɗinnan. A hankali ya sake zuba mata ido tun daga yanayin yadda ta zazzaro ido har zuwa sanda ta shiga mirza saman goshinta yadda Idannuwanta suka rinqa sama da ƙasa. Haƙorinsa ya ɗan datse yana ci gaba da mata kallon ƙasar Ido. "Duk da ance shi ɗin ba kamar sauran mutane bane, amma a yadda nake ji ɗinnan idan har nayi gaba da gaba dashi zan iya kashe shi a matsayina na me kishin ƙasa" Haka ya riski muryan ta me kama da waƙa take rerawa ba masifa take sirfawa ba, harda irin mutsitstsike hannuwan su bada sautin ɓasss. Dade beyi niyar jimawa a zaman tattaunawar ba domin akwai manufar shi na yin hakan, akwai saƙon da yake son masu shi su ɗauka. Don haka cikin wani irin jannn hankali da salo me kyau ya ɗaga hannunsa sama tare da mirza shi irin gintsewar nan yace. "Mutuwa dai kika ce idan kuma ya kasance shi ɗin baya tsoron mutuwar ba fa?" Zuciyarta ce ta ji ta buga da mugun ƙarfi amma cikin ƙarfafama kanta gwiwa ta mayar masa da amsar daya bata daidai dashi. "Idan harya kasance baya tsoron mutuwar, ya bayyana kansa mana ga jami'an tsaron da suke fafutukar nemansa ruwa a jallo, nasani dai baifi ƙarfin hukuma ba saidai idan ya kasance shi ɗin matsoraci ne, domin jarumi ba'a san shi da yakin suƙuru ba ya fito ayi na sarari gaba da gaba shida matakan tsaro a gabza yaƙi" Wani irin ɗan waro mata Idanu yayi, tare da mata alamar jinjina da hannuwansa, kafin cikin hosky voice nashi ya furta. "Idan kuma ya kasance su jami'an ne da kansu suke tsoron tun karar safa? Mutumin daya Kasan ce baka gane gabansa balle bayansa balle ka gane inda ya dosa, yanzu duk rikicin da tarzomar da ya haɗa a garin nan amma ace yasha, kinga kenan ƙarfinsu yafi ya musu zarrar da basu taɓa iya ja dashi ba, idan kuma sun shirya to Bismillah, hakan bai hana shi ya shiryawa kansa zuwa mataki na gaba ba kamar yanda ya tsara ma kansa , yana da karfin hali sosai, komai zai aikata yana aikatawa ne cike da kwarin gwiwa ɗari bisa ɗari, tare da yaƙini da kuma sanyawa a ransa tabbas zai yi nasara, Ki sani sawa a rai ne yasa falke baya jin wahalar tafiya,wanda idonsa basa gani sunanshi makaho, Ammah cikakken makaho shine wanda zuciyarsa bata gani kamar dai jami'an tsaron ku. Haka za Kafin ya sanya kansa cikin harkar sai da ya shiryawa kansa komai da komai, tare da tsara ko wanne mataki!, don haka idan ma da wata manufar suka tsoma zancen zuwa gidan jarida, wannan shine yaƙin sunƙurun da suƙe ikirarin AK EAGLE yana yi, wannan yaƙin iya na filin daga ne bawai na media ba, don haka sojoji, ƴan sanda, wannan yaƙin ba na nan bane, yaƙi ne na iyaka jami'an tsaron da suke ikirarin suna son kare ƙasar su, kana Idan suna jin sunkai sun kuma isa su nuna jajirwarsu, wajen dawo mana da governor da kuma minister ta hanyar nuna jajircewar su a aiki". Zuciyar tace taji ta matse da tunanin irin fassarar da yayi ma Maganganun sa Atake taji tana jin wani abu na narkewa a cikin jikinta kamar ƙarfen da ake ƙonawa a cikin wuta, tabbas yayi maganar gaskiya, wannan yaƙi ne na jami'ai, bawai su kawo media ba, kafin ta ɗago wayammmm taga babu shi babu alamunsa, a wurin da yake zaune, jikinta ne ya shiga wani irin mazari da tsoron masifa, tuni ta gaza sarrafa kanta wajen dawo da nutsuwar ta, tana shirin tashi ne kuma tayi gamo da Katar ɗin ganin ƴar ƙaramar fara tasssss ɗin takarda, wanda take ƙaya ce cikin kyakkyawarn ado, tare da tsarin rubutun daya fi kama da a inji aka zana, cikin manyan harrufa aka yi rubutun kamar haka. *" FLOWER BERRY PIE, THANKS DA KASANCEWA DA AK EAGLE 🦅 "* A razane ta tayi cilli da takar dar tana juwo gasu MD, bata tashi aune ba sai ganin Md tayi ƙarƙashin dujuwar office ɗin. To ai shikenan kooooo saimu gimtse🫰 *By AMMEY LAYLERH ✍️* 🦅 MIKIYA 🦅* {Mai hangen nesa 👀} *~We want an end to oppression💪~* https://chat.whatsapp.com/DGIo9iiSjlgJPPqFHNtddH #HOT LOVE #ROMANCE #AK FOV #DEEP ASSUMING FOV ____________________ #*NA MARYAM NASEER* #~AMMEY LAYLERH ✍️~ ✯ *~🌠 OFFICIAL MIRRAH 💫~* Page 9&10 🤍🔥✅ __________________ ★★★★ Ba md kaɗai ba duk wani ma dake ƙarƙashin zamani hankalin sa idan yayi billions dollars to a tashe yake. Cikin tsananin tashin hankali itama ta shiga zara idonta, bawai don tsoron abinda ka iya zuwa yaje ba. Sai don kawai hangen irin tashin hankalin da Annenta da zata shiga harma da baffan ta. Hankalin ta bai sake tashi ba saida jiniyar ƴan sanda ta karaɗe gidan jaridar baki ɗaya cikin fitar hankamotar ƴan sanda,wasu

Table of Contents

Chapters

54 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54