Skip to content

Chapter 29

Chapter 29

Mikiya Book One Complete Hausa Novel 1,211 words 0 views Progress saved
Download Book

Wani mugun kallo MOH JIDDO tabi wambai dashi wanda suke ƙira da *RIGA DAKI* a yarensu na cennnnn. Cikin tsana da jin haushi MOH JIDDO ta furta ”Ni na rasa mecece matsalan ABDOUL-MALEEK da ya gwammace ya tafi yawon duniya har wata uwa Nigeria akan abbinda ba tabbacecce bane. Shi burin daya ɗauka alƙawarin cika tashin” Ijiyan zuciya Mommah ta sauƙe tana jin wani abu na yawo a dukkan sassan jikinta. “Yanzu ai idan ya riski saƙon mutuwarsa a yanar gizo ya dawo!, nasan duk inda yake aduniyar nan zaiga news na rasuwan mahaifinshi dan haka zamu ganshi idan ya riski saƙon macewar ubansa” Yana faɗin hakan ya tashi yayi gaba abinsa yawuce yafita yanajan ɗan ƙaramin tsaki aranshi bayan yakai waje. Cikeda ɓacin rai MANDOOD ya furta ”MOH ve said this time without number to Mai Martaba he should call ABDOUL-MALEEK to order, duk cikin yaran me martaba babu gantalalle kaman ABDOUL-MALEEK, yaƙi zama ya koyi komi na al’addun masarautar mu, sabo da yana jin kansa shi tantiri ne” _TUN DAGA HAIHUWA MA KUWA_ Domin Abdoul-maleek hadarine malafar duniya,funkasau babban girki, biri da gatarine shi ajalin me gonna, Jan kasa na bayan daki kowa ya ganshi ya tuna Allah. Shi kadangaren bakin tulune a barshi ya fada ruwa a taba shi kuma ya FASA TULU, Ak ginshikin dutse me kowa yayi karo dashi shika fadi, soja mazan fama namijin mazaje an buga dashi an barshi saidai su buga su barshi kuma domain shi din dashen Allah ne, murucin kan dutse be fito ba saida ya shirya_ ZAID ya furta a cikin zuciyarsa ya miƙe yana ficewa a ɗakin shima domin da biyu yaki sanar musu yayi magana da AK din. haka suka ringa fita ɗaya bayan ɗaya, ɗakin ya rage daga Mommah sai RAZEENERH mata ta farko ga Me martaba sarki *SARKI HASSAN AL-HASSAN EMAAR KUWAIT* Wasu irin kaifaffun hawayene suke saƙƙo mata, cikin ƙunar zuciya da irin raɗaɗin dake ƙona zuciyarta ta kwanto da kanta zuwa jikin Mommah MARYAM. Ta fashe da wani gurgegen kukan ɓakin ciki. ”Shin Sai yaushe zamu dena zubarwa da ƙaddara hawayenmu? Sai yaushe abubuwan dake ɓoye zasu bayyana kansu? Na gaji-na gaji NA GAJI MARYAM, inajin haƙuri na na gab da ƙarewa akan abubuwan dake faruwa dani a cikin wannan azzalumar masarautar HABA!” Ta faɗa cikin sake fashewa da wani gursheshen kukun, "Haƙuri shine matakin ko wacce nasara RAZEENERH, Ko wacce Nasarar rayuwa da ɗaukaka kuma suna zuwarma baya ne da tarin ƙalubalen rayuwa salo daban daban, me yasa zamu gaza cinye ɗan takin daya saura a cikin rayuwarmu?. Xuwa yanxu AYSHATUL HUMAIRA a bayyane take garemu loƙaci kawai muke zuwa ya bayyana kansa,Ayi walƙiya Allah ya bayyana mana magautanmu na ɓoye dana fili mu gansu su fito suna hawaye anyi walƙiya!!!” Sosae suka sha kuka me sunan kuka kafin su runguɗa zuwa ga special room donper ɗin da me martaba yake cikin haɗaɗɗen hospital ɗin masarautar. Dammmmm ɗakin yake tarin ƴan uwa na kusa dana nesa irinsu garin Makka Madina Saudi Arabia dadai sauransu aurarru da ma'aikatan da suke aiki a wojen ƙasar. Wani gauran numfashin da sarki HASSAN AL-HASSAN EMAAR KUWAIT ya kawo ne ya sanya baki ɗaya katafanin jama'ar parloun, juyowa zuwa gareshi. ALHAMDULILLAH wasu suka shiga furtawa wasu kuma zuciyarsu na ƙonewa ne tare da yin baƙikirin tun durun da tsabar masifar baƙin cikin da ke soya zuciyarsu ƙurmus. Ahankali ya shiga bin kowa dake parloun da ido, cike da tsananin ƙarfin hali da kuma dauriya irin ta zaratan sarakai ya saki kyakkyawan murmushinsa me kyau. Wanda exactly tsananin kamfaninsa da ABDOUL-MALEEK KUWAIT AK suka gama bayyana. ”Alhamdulillah Ban mutu ba Allahu Ya tsare lafiyata a kwanana akwai ƙari don haka kowa ya kwantar da hankalinsa” sarki AL-HASSAN EMAAR ya furta Wanda wannan maganar nashi ya daki wasu ɓoyayyan rufaffun zuciyoyi daga cikin al'ummar denpor ɗin.... Haka kaifafan idonsa yaci baba da yawo har sauke kallonsa akan Ayeshan shi. Kyakykyawara mace karshe a fannin hakuri mace me kamar maza CE ita wajen danne ko wanne irin ciwon cake damun zuciyarta. Da wani sassayan kallo ya bita yanajin lallai rayuwar idan babu ita to shima babu amfanin tashi rayuwar, a jinin jikinta taji irin kallon da take binta dashi. ★★★ Abuja Nigeria Zaune yake yayi crossing kafafunsa sanye yake cikin shigar kananan kaya na shan iska, loptop ne a gabansa kan dan table tonight din dake gabansa, yana faman sarrafata cikin kwarewa yake latsa keyboards din system din. A nutse zayd suraj shureim ya karaso har inda AK din yake zaune. Zaman shima yayi ba tare daya furta komai ba, haka suka shiga zaman kurame har na tsawon 30 minutes, A nutse Zayd dubi AK da yama nuna tamkar besan anyi ruwan zayd din bane yadan daki shoulder na AK din. Sai kuma ya dan saki wani shegen murmushi domin shima karshe ne fagen tashi izzar Wanda shima sarautar kano ta gama ratsa ilahirin Jinin dake gudana a cikin jikinsa. ”Yaryadi baka yadon banza yau kuma dame kake tafe?, ka kirani ka sanya na baro garina zuwa wani garin Right?' Ka kuma shareni abunka to Dan ubanka Wllh zan komawa na domin inada abubuwan yi dana baro ba kamar kai ba” Wata katuwar harara ak ya sakarma zayd yana fadin. ”Jeka mana dan uwarka ka gani idan Abbu ko ummieyn Momma basu koromin kaiba” Ya fada a daidai lokacin kuma ya kammala aikinsa na cikin laptop, tashi yayi tare da yin gaba yana fadin. ”Idan kaga dama same ni a room na baka 2 mint domin INA shirye shirye bar muku kasarku ne” ”Look AK karka ma soma hakan, Don munyi woya da mommah tun a daren jiya ta shaidamin cewar jikin Me mar taba da sauki sosae $0 inaga babu bukatar zuwanka!” Ko ta kanshi ak bai biba saima wucewarsa da yayi room Bayansa zayd yabi cike da shekiyanci yake tsokanarsa ai dole ya bashi girma tunda shine autan su momman ak din. Ganin nan din ma ya share shi ne ya sanya shi komawa seriously tare da furta. ”Muyi abinda ya kawo mu kasan akwai Case's da yawa dana tsalallake na baro dude” Charkkk kuwa ak din ya tsaya tare da juyowa ya fuskanci zayd din. Zama sukayi a tsakiyan kayataccen palon hotel din, computer'nshi ya janyo tare dayin wosu yan danne danne said kuma ya juyo da fuskar computer system din xuwa gaban AK. Da wani black beauty guys ya fara cin karo wanda me sanye cikin kaki na yan sanda. Tsaye yake chark a gaban Cf of the police babu alamun tsoro a tattare dashi. Gani yayi wannan ceef din ya mike a fusace yana duban wannan tsayayyen matashin, kafin kuma cikin fusata ya furta. _Akan me zaka harbe shi?, Tambayarka nake me yasa ka harbeshi? Me yasa kai baka Iya sarrafa kankane?_ Gani yayi wannan matashin police din ya furta. _Bana Iya sarrafa kainane akan irin wadan nan tantiran yallabai!_ _Kenan saika harbe shi kuma?_ Ceef ya sake furta a tsawace. _Me yasa bazan hukunta wadan da suke barazana wa al'ummarta ba?, nayi rantsuwa da girman Allah zan kare kasata da al'ummata. Akan mene yasa bazan harbeshi bayan shidin gurbatacce a cikin al'ummar?_ Ya fada tare da sarawa a gaban Ceef din. _To hakan ba

Table of Contents

Chapters

54 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54